advanced Search
Dubawa
10017
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Da a ce manufar addini ita ce gina rayuwar duniya da lahira ga mutum, to saboda me muke ganin mutunen da ba su da addini suka fi ci gaba da more rayuwa.
SWALI
kuna cewa, addini ya zo domin gina duniya da lahira ga mutum, amma kuma muna ganin wasu mutanen da ba su da addini sun fi ci gaba da more rayuwar duniya. Ta yaya zamu iya warware wadannan tambayoyi?
Amsa a Dunkule

Musulunci ya zo ne domin ya kafa dokoki da alakar dan adamtaka. Madinar Manzon Allah (s.a.a.w) ta kasance samfuri na al’umma mai bin dokoki, ta yanda ta tsara dukkanin alakar dan Adam karkashin inuwar dokoki.

A mahangar Shahid Sadar (r.a) yana cewa, musulunci ya ajiye ma’aunai guda biyu, domin tabbatar da wannan manufofin. Na farkonsu shi ne na zahiri, wanda ke tsari ga jama’a wacce take kiyaye wannan dokoki. Na biyu shi ne ma’aunin da ba na zahiri ba (badini), wanda su ne manufofi da matafiya wanda musulunci ya samar ga kowane mutum domin ya damfaru da su ga bin dokoki. Sai dai jama’ar musulmi saboda wasu dalilai (abin takaici) kuma babu damar da zamu ambace su yanzu, sun kauce wa hakikanin addinin, da hakikar manufar addinin. A yau ba zamu lissafa wanna jama’ar cikin jama’a mai bin dokoki ba. Sai dai sadanin haka.

Wasu al’amurori sun gudana a yammaci da yadda hakan shi ya haifar musu da wannan ci gaba. Kuma da zamu yi nazarin hakikanin tarihi da mun ga musulumai yadda suka kawowa duniya ci-gaba sanda suke riko da addinin musulunci madaukaki, ci-gaban birnin Andulus da abin da kasar Iran da Iraki da wasu kasashe sanda suka yi riko da addinin musulunci sun samu hadaka da ci gaban ilimi mai girma, har da ilmin nukiliya, da kimiyan sararin samaniya, da wasu ilimomim ma da da ba sai mu ambata ba, a karni uku kawai. Kar mu manta da rawar da yammaci suka taka wajen mayar da musulmi fakirai don samun damar salladuwa a kan su.

Amsa Dalla-dalla

Da akwai abin tsokaci a kan wanan maudu’i, cewa shi fa musulunci ya dora alakar dan Adam a kan dokoki da tsari – birnin madinar da ma’aiki ya kafa ta zamanto samfuri abin koyi, in ana maganar al’ummar da ke kan dokoki. Ya kasance duk alakokin dan Adam a karkashin inuwar dokoki suke gudana.

A mahangar Shahid Sadar (r.a) yana cewa, musulunci ya ajiye ma’aunai guda biyu, domin tabbatar da wannan manufofin. Na farkonsu shi ne na zahiri, wanda ke tsari ga jama’a wacce take kiyaye wannan dokoki. Na biyu shi ne ma’aunin da ba na zahiri ba (badini), wanda su ne manufofi da matafiya wanda musulunci ya samar ga kowane mutum domin ya damfaru da su ga bin dokoki. Sai dai jama’ar musulmi saboda wasu dalilai (abin takaici) kuma babu damar da zamu ambacesu yanzu, sun kauce da hakikanin addinin da hakikar manufar addinin. A yau ba zamu lissafa wanna jama’ar cikin jama’a mai bin dokoki ba, Sai dai sadanin haka.

Wata kadiya ta faru a turai, ita ce: - a cikin wannan zamani na motsawa (wanda kafin shi yakoki suka faru na tsawon lokaci tsakanin musulmi da kiristoci) ta yanda yammaci suka leko wayewar musulunci, suka hango ci-gaban musulunci mai habaka da sauri. Sai suka fara tambaya da bincike a kan dalilan wannan ci-gaban. Sai yammaci suka amfanu da tsarin wayewar zamanin da bincike wanda yake da alaka da ci gaban. Daga nan ne yammaci suka amfanu da damarmakin da karfi na kai tsaye. daga lokacin ci-gaba zuwa yanzu, sun yi kokarin ilmantar da mutanensu kimiya. kuma sun daukaka kimiyarsu da fasaharsu. amma basa riko da ma’aunai na zahiri a wani bigire kuma basa riko da rukunan addini ko koyarwarsa, ya kasance a gare su nasara babba ita ce ta fuskar kimiyya da fasaha da kere-kere da gine-gine.

sau da yawa muna duba ne zuwa ga zahirin al’amura, wanda shi ne danfaruwar jama’ar yammaci (turai) wacce ba ta da addini da bin dokoki sai da ci gaban kimiya kawai, da zamu binciko dalilin wannan damfaruwar da zamu ga cewa ba komai ba ne illa tsanantawar masu sa ido a kan dokoki. ta yanda da za a dauke wannan tsanantawar aguri daya (a yammacin turai) ko da na lokaci kadan ne, da kun ga rushewar dokoki lokaci daya.

A bisa misali mu dauki dokokin ketare hanya, abin da ya zo mana shi ne su turawan yamma suna riko da bin dokokin ketare hanya, mu kuwa ba haka muke ba. Eh wannan magana gaskiya ce, Sai dai mene ne dalili?

Ba komai ba ne dalili, illa matukar ko-in-kula da aiki da dokokin ketare hanya. Ta yanda ta jirkita kiyayewar a gurin kowa da kowa.

A wasu kasashen ba a samun kyamarar daukan hoton masu laifi ko ‘yan sanda da suke tsayawa gefen hanya. Da haka zaka samu mutane suna bin dokokin ketare hanya sosai. Idan ka tambaya a kan dalilin, amsar da zata zo, da wani zai ketare alamar fitilar hanyar ba tare da kula da shi ba, sai ya zamo yana tsammanin mutum ashirin ko fiye da haka sun sa masa ido daga wadanda suke kallon shi na daga masu shaguna da sauransu, da zarar ya tsallaka za su ba hukuma lambar motarsa da ta saba dokar. Kuma da ya fuskanci horo mai girma sosai.

Don abin da dokoki suka tabbatar a gurinsu shi ne, gaskiya tana tare da mai kara har sai an tabbatar da sabanin haka.

Da zarar an sanar da ‘yan-sanda cewa wannan motar ba ta bin dokokin alamar hanya, to za a yi masa horo nan take, sai dai idan sun tabbatar da bayanai masu gamsarwa, amma ta yanda zasu iya samun damar haka. Horo yana kasancewa ne ta hanyar biyan kudi, idan mai lafin ya yi jinkirin biya, harajin zai iya nunkawa.

A bisa dabi’ar mutane suna jin a cikin wannan yanayi suna misalta bin dokoki. Sai dai wannan nau’i na riko da dokoki ba ya da wata ma’ana ta badini. Saboda lissafinsu yana karewa ne a kan abin duniya kawai.

Misali da zaku yi tafiya zuwa turai lokacin dusar kankara. Zaku ga dacewar wannan bayani nan gabanku. Shi ne yayin saukar kankara da kasantuwar tafiya a hankali saboda tular kankara a kan titi. Zaka samu cewa mutane suna tsayawa da jar alamar hanya. Kuma suna kiyaye alamomin wucewa. Sai dai bayan lokaci kankane idan jinkirin ya tsawaita zaka ga mutane suna duba agogonsu, suna tunanin makara. Na wani dan tsaiko zaka gansu suna danfare da bin dokoki amma daga baya sai su fara sabawa bayan haka.

To saboda mene ne hakan ke faruwa? Saboda suna aiki da lokutansu. da zasu saba dokokin za a yi musu tarar $ 50, idan suka jinkirta biya za suyi asarar $100, sai ya zama sakamakon sabawar ya zaman masu amfanin duniya.

Tunda haka ne, dukkanin rayuwarsu tana gudana ne ta tushen amfanuwa ko cutarwa a duniyance. Amma abin da musulunci yake nufin tabbatarwa: - abin takaici ko da kuwa bai samu ba a cikin al’ummar musulmi sai ‘yan kadan, shi ne ya sanya bin dokokin musulunci a cikin jama’ar musulmi, ba wai don karfin hukunci yana bin al’amuransu ba. Kawai dai saboda Allah madaukakin sarki yana ganinsu kuma yana shaida a kan ayyukansu da al’amuransu. To da hakan zai kasance da an sake ganin zamanin daukakar musulunci komawa, kamar yanda ya kasance zamanin Ma’aiki (s.a.w). kunga ai shi (ma’aiki) ya ci nasarar a tsawon shekarun da ba su fi goma ba wajen juyar da al-umman kauyawa, jahilai zuwa wayayyu, ci gababbu da ba a yi kamarsu ba kuma ci gaban da ba kamarsa a tarihi.

Da a ce haka ne har wa yau zamu ga zamani na musulunci mai haske kamar yanda ya kasance lokacin manzo Allah (s.a.w) ya samu dama ta hanyar koyarwar addini a cikin shekara goma.

Idan mu ka yi duba ga abin da ya faru a tarihi zamu ga musulmi sun tabbatar da ci-gaba babba, yayin da suka zama suna riko da addinin musulunci da koyarwarsa. Daular Andulus da abin da ya faru a Iran da Iraki da sauran kasashe zasu tabbatar da haka. Sai dai yayin da suka jingine addini, sun zamo suna rayuwa a yanayin koma baya. Abin duba a yanzu ita ce jamhuriyar musulunci ta Iran, a lokacin da suka dogara da tsarin addini a rayuwarsu. Mun ga sun samu ci gaba a ilumummuka masu girma, har suka wayi gari a shekaru talatin dinsu sun zama a cikin kasashe masu mallakar fasahar nukiliya ta zaman lafiya, da binciken sararin samaniya. Bugu-da-kari, da nasarori a bangarorin sauran ilmi wanda ba zai yiwu a kawo su ba.

Kar mu manta rawar da yammacin duniya yan mulkin mallaka suke takawa a wajen sanya musulmi suna rayuwa cikin halin rashin kimiyya da fasaha don samun saukin dannesu.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa