Dubawa
3555
Ranar Isar da Sako: 2011/04/11
Takaitacciyar Tambaya
shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka Daular Safawiyawa, kana mai yaba wa mahukuntanta?
SWALI
Shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka daular safawiyawa kana mai yaba wa mahukuntanta?
Amsa a Dunkule

Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da al’umma, kana akwai manufar yada ilimi da fahimtar Addini bisa dogara da cewa ikon fada aji da hukuma take da shi.

Daga cikin zarge-zargen da ake dangane da alkar Allama Majlisi ta siyasa har da zuwansa fada tare da tawagar mahuntan Safawiyawa da kuma taimakawa sarakuna na zamaninsa. Babu Shakka malami kan bada kai ga yanayi da suka samu kansu a ciki. Irin alakar Allama Majlisi ba ita ce farau a gun malamai ba. Tabbas irin wadannan malamai na Shi’a suna tafi da harkokinsu ne bisa tafarki na Imamai Ma’asumai  (a.s) wadda –wani lokaci- takan ginu bisa turbar amfani da sarakuna ‘yan-kama-karya da halifofi azzalumai ta hanyar duba na sanaki ga yanayin da ake ciki musamman a bagaren mahimman lamura da matsaloli da suka Shafi duniyar musulmi da zamantakewa da ilmatarwa, ta hanyar amfani da wannan alakar da nufin aiki tukuru don samar da fa’ida da nufin amfanar da al’umma da shiryar da mutane da samar da gyara a al’umma, musamman a gefen yada Addini da yada Mazhaba ta gaskiya da kokarin samar da adalci na rayuwa. To a nan zamu iya ganin dalilai da suka sa Allama Majlisi ya yi wannan hubbasar bisa wannan manufar, watau bai yi hakan don wata manufa tasa ta kashin kai ba. Wannan hubbasar tasa ta samu ne bisa yanayi da ya samu kai a ciki da nufin cimma wancan manufar da hadafi na siyasa. Ko da yake akwai malamai da suke da ra’ayi da ya saba nasa na katse duk wata alaka da mahukuntan Safawiyawa da ma wasunsu.

Amsa Dalla-dalla

Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya dama wasu mahukunta na wasu dauloli ba da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da alfanu da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da taimkon al’umma, kana akwai manufar yada ilimi da fahimtar Addini bisa dogara da cewa  ikon fada-aji da hukuma ke da shi. Kare malamai daga shiga hadari, samun damar  bayyana musa mutanen kirki don ba da kariya ga gurare masu albarka yayata hukunce-hukuncen Shari’a a tsakanin al’umma duk wannan kan samu ne ta hanyar kyautata alaka tsakanin malamai da sarakunan Safawiyawa. Bisa gaskiya manufarsu ba bishe Shari’a ba ne, manufa ce ta yada karantarwa da ilimi. Abin lura a nan shi ne wannan alakar da kyatata fahimtar juna wata dama ce a wani zamani ta sanin Ubangiji. Abin lura a nan shi ne wancan alakar da fahimtar juna wata mahimmiyar dama ce a tarihance kana gaba ce ta samun kyakkyawar dama ga Shi’a a wannan lokacin.

MaSharhanta game da daular Safawiyawa a wannan zamani sun yi amannar cewa “Tushen daular Safawiyawa ya faro ne a matsayin kungiya ta wannan hanyar ce daular ta samu shimfida ikonta da kafuwa da tabbatar dokokinta. Tsarinta na masarauta ya kunshi sassan bangaren soja, wadda kowane sashi na da nasa aikin, kana akwai bagaren tafiyar da mulki mai kare dokoki da tsara bukukuwa na Addini da ke karkashin malaman musulmi da yadawa da bunkasa harkokin Mazhabobi, karfafawa a kan batun wilaya da bara’a, da tsattsara bukukuwa na farin ciki da na takaici da idudduka na Addini da…, duk wadannan ababe sun yi matukar taka rawa wajen habaka siyasar Iraniyawa a daular Safawiyawa.”[1]

Dangantaka Tsakanin Allama Majlisa Da Mahukuntan Daular Safawiya

Daga cikin zarge-zargen da ake yi dangane da alakar Allama Majlisi ta siyasa har da zuwansa fada tare da tawagar mahukuntan Safawiyawa da kuma taimakawa sarakuna na zamaninsa. Kafin shiga wannan batun muna ganin ya zama tilas mu yi nuni zuwa ga wani muhimmin zance shi ne:   Hakika malaman Shi’a a karkashin daular Safawiyawa a zamanin sarki Sha kafin kafuwar daular Musulunci sun rayu ne a hali na takaici da shiga tasku da nisanta su a fagen siyasa da harkar zamantakewa ta yadda aka nisanta malaman Shi’a da wakilansu daga kowane irin mukami na harka da  jama’a. Wannan ke nan! A daya gefen su kuwa talakawa sun sallama wa wadannan mahukuntan. Tambaya a nan ita ce, wane mataki za’a dauka  idan aka tsinci kai cikin wannan yanayi? Shin ya dace a tunkari wannan hukumar ta hanyar fadanci da bambadanci da amfani da addini? Ko fito-na-fito da fafatawa da yanke hulda da rashin bada kai ga mahukunta?  Shin zai yi kokarin wayar da kan jama’a don kau da matsalar?  Ko ya wajaba ya shelanta jahidi don kau da ita da nufin kafa halattacciyar gwamnati da rusa ta baya? Ko kuma kyakkyawar mafita a irn wannan yanayi shi ne bude kofar tattaunawa da hada kai da mahukunta don samar da fa’ida da maslaha ga Addini da Mazhaba da ma al’umma?.

Babu Shakka malamai kan bada kai ga yanayi da suka samu kansu a ciki. Irin alakar Allama Majlisi ba ita ce farau a gun malamai ba. Tabbas irin wadannan malamai na Shi’a suna tafi da harkokinsu ne bisa tafarki na Imamai Ma’asumai  (a.s) wanda –wani lokaci- takan ginu bisa turbar amfani da sarakuna ‘yan kama-karya da halifofi azzalumai ta hanyar duba na tsanaki ga yanayin da ake ciki musamman a bagaren mahimman lamura da matsaloli da suka shafi duniyar musulmi da zamantakewa da ilmantarwa,  ta hanyar amfani da wannan alakar da nufin aiki tukuru don samar da fa’ida da nufin amfanar al’umma da shiryar da mutane da samar da gyara a al’umma, musamman a fagen yada Addini da yada Mazhabar  gaskiya da kokarin samar da adalci a cikin rayuwa. A irin wannan halin malaman Shi’a kan yi kokarin samar da kyakkyawar yanayi da nufin haifar da fa’ida ga jama’a ta hanyar wannan alakar. Wannan salon zamu gan shi a tsarin rayuwar Amirul muminina (a.s) haka kuma a rayuwa ta Imamai (a.s) na bayansa. Ga misalai:

- Taimakon da Amirul muminina (a.s) ya yi ga daulolin halifofin nan uku, da karbar mukamin gwamnan Ahawa’az da almajirin Imamu Sadik (a.s) watau Abdullahi Annajashi ya yi, Aliyyu bin Yakdin ya rike ministan kudi a gwamnatin Harunarrashid bisa umurnin Imamu  Kazim  (a.s), Imamu  Rida  (a.s) ya karbi makamin wilayatul ahad (yarima) a gwamnatin Ma’amun  Abbasi, Alkawaja Nasiruddin Dusi ya yi aiki a gwamnatin Holako da sauran su. Kazalika manyan malamai na Shi’a shigarsu gwamnatin Safawiyawa ya  taimaka a bangaren siyasa, malaman sun hada da gogaggen masani Alkarki, sheikh Baha’i, Allama Majlisi babba da Majlisi karami da sauran su, sun riki wasu mukamai na siyasa a fannin Addini. Abin lura a nan shi ne shigarsu gwamnatin Safawiyawa ba ya nufin sun shiga ne don bukata ta kashin kai ko samun matsayi ko mukami don tara dukiya ko kudi ba. Sun yi kokarin ne da nufin kare daula ta Shi’anci ta wani gefen. Wajabcin kulla wannan kyakkyawar alaka kan iya bayyana karara idan aka dubi wariya da a kan yi wa malaman Shi’a a tsawon tarihi. A bisa dabi’a kulla kyakkyawar alaka tsakanin mahukunta takan tsayu ne da nufin samar da wata dama ga malamai na sauke wani muhimmin nauyi da ke wuyansu da nufin kare Addini da Mazhaba da yada ta don ida sako na ilmantarwa da kare gundarin Mazhabar Shi’a da  kakkafa makarantun Hauza da ilimi da sauran su.

Domin karin bayani za’a iya duba gurare kamar haka:

 1. Marwi Baradanshiya siyasi Allama Majlisi; izalatu mazhab siyasi inda Allama Majlisi.
 2. Mujallat Hukuma Islamiya, daba’i na 20,suldan muhammadi, Abulfadal; <mururu bar’andake siyasia=Allama Muhammad Bakir Majlisi>

 


[1] . Nahram Nazad Muhusin safawiyah darkastara tarikh Iran zamin sh99, (makalar siyasar kan daujjlar Safawiyawa), daba’in IntiShara’at sanwidah,  jami’ar Tehran 1383 HK.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Shin shedan na da zuriya, kuma shin su ma la'anannu ne?
  4429 ابلیس و شیطان 2012/07/24
  Hakika shedan na da zuriya kuma su ma la'anannu ne kamar yadda yake la'ananne, domin su ma bisa hakika sun bi tafarkin sa kuma sun yi riko da hanyarsa da salonsa wajen batarwa da kokarin kautarwa daga tafarkin gaskiya, sun dogara da wannan hanyar a wajen batar ...
 • Me ye mafi dadewar madogarar jagorancin malami da ake da ita?
  3137 پیشینه تاریخی ولایت فقیه 2012/07/24
  Mafi dadewar madogara game da wilaya ko jagoaranicn malami da muke da ita sun hada da littafin Mukni'a na sheikh mufid ne, ya kawo wannan bahasi a babin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka hau kan malami.
 • menene hakikanin ma’anar salla?
  22120 Halayen Aiki 2012/07/25
  Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
 • shin wasannin motsa jiki a lokaci daya tare da kida {muzik} ya halarta? Shin irin wannan motsa jiki hukuncin su daya da rawa?
  5665 حرکات ورزشی همراه با موزیک 2013/08/15
  Kida {muzik} da rawa wasu abubuwa biyu ne da suke da hukunci ma bambamcin juna inda alokaci daya mutun zai hada rawa ta haram da kida na haram, to ya aikata laifi {zunubi} biyu ne daban daban a lokaci daya. Mafiyawanci malaman figihu kida {muzik} wanda ya ...
 • Illolin wasa da azzakari, manyan zunubai, wankan janaba, dalilan haramci
  390 Miscellaneous questions 2019/06/16
  Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
 • Shin ya halatta a yi salla a gefen Kabarin Imamai wanda wani lokacin Kabarin nasu kan zama a bangaren alKibla kuma ya dace da inda mai yin salla ya ke kallo?.
  875 زیارت قبور و بنای مراقد 2017/05/22
  Bisa haKiKa zahirin wannan ayar abin a duba ne. ayar tana magana ne kan halaccin gina masallaci a kusa da Kabari, kama bayanan da suka zo a tafsirai na nuna cewa wannan masallacin an gina shi a gefen Kaburran Ashabul Kahfi. Duk da cewa a kwai ruwayoyin ...
 • Mene ne sharuddan da ke sa wa Rana ta tsarkake kasa da gini?
  3841 بیشتر بدانیم 2012/07/25
  Rana na daya daga masu tsarkakewa kamar yadda ya zo a fikhu, yadda rana ke tsarkake gini da kasa kuwa; ka da a samu tazara tsarkakakkiya tsakanin zahirin (doron) kasa da bayanta (cikinta) ko kuma ginin da hasken ranar zai sauka a kansa kamar iska ko wani ...
 • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
  826 زن 2017/05/21
  Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
 • Me ake nufi da hukunci da fatawa? Me ye bambancinsu?
  5399 بیشتر بدانیم 2012/07/24
  Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin. Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana ...
 • me ake nufi da duniyar zarra
  5252 پیمان پروردگار با مردم 2012/07/26
  Duniyar zarra ko kuma duniyar alkawari, na nufin wani lokaci ko wata marhala ko mahalli ko kuma wata duniya ce wacce Allah ta’ala ya fitar da rayukan dukkanin mutane daga cikin tsatson Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a bisa kankanuwar sura sosai, kuma ...

Mafi Dubawa