Dubawa
6752
Ranar Isar da Sako: 2012/07/24
Takaitacciyar Tambaya
Yaya hukuncin Kudin ribar (kudin ruwa) da ake karba daga Bankunan a Daulolin musulunci da wadanda ba na musulunci ba?
SWALI
Na ji cewa Cin riba (kudin ruwa) yana daga manyan zunubai, yanzu ina tambaya ne cewa shin ya halatta karbar kudin riba (kudin ruwa) daga bankuna tare da sanin cewa ina rayuwa ne a kasar da ba daular musulunci ba ce? Haka nan kuma me ye hukuncin Katin Canji da ake bayar da kudi mai yawa na kudin riba (kudin ruwa) kan kanta?
Amsa a Dunkule

Fatawar Jagoran Juyin musulunci mai girma sayyid Kham’na’I game da mu’amalar banki a daulolin da ba na musulunci ba ita ce:

a- Bayar da Riba garesi haramun ne; Wato karbar dukiya daga bankin a kan cewa rance ne da sharadin dawo da kudin da ya haura hakan yawa, haramun ne. Sai dai idan ya matsu sosai kwarai matsuwa da ta halatta ya karbi haram din, sai dai gudun kada ya fada cikin aikata haramun mutum yana iya niyyar ba zai dawo da karin da aka dora masa ba, ko da kuwa ya san cewa zasu nemi ya kawo wannan kudin karin[1].

b- Ya halatta a karbi kudin riba (kudin ruwa) da na ribar ciniki daga bankunan Daulolin da ba na musulunci ba[2].

Kuma Sayyid Kham’n’I ya bayar da fatawa game da Takardar Canji kamar haka: Ba matsala game da kudin da ake ajiyewa a akawunt da mutum yake dibar su yayin da yake bukatar su, amma dukiyar da ake ajiye ta a akawunt - ba tare da an samu wani kudi da mai akawunt ya zuba ba – idan ta kasance da sunan rance ne, kuma ya zama akwai ribar kasuwa, to asalin bashin da aka bayar ya yi, sai dai karbar dadi kan hakan cin riba (kudin ruwa) ne kuma haramun ne[3].

 


[1] Taudhihul Masa’I na marja’o’I, j 2, shafi: 935, s 1911.

[2] Abin da ya gabata: shafi: 936, s 1917.

[3] Amsar Ofishin Jagora ga Tambaya 369, Maudu’i: Takardun Canji da Kudin ruwan Banki.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Mene ne ra’ayinku dangane da wilayar imamai ma’asumai (a.s) a kan mumini?
  3572 دانش، مقام و توانایی های معصومان 2012/07/25
  DAGA AYATULLAHI MUKARIMUSH SHiRAZY (MZ) ‘E’ imamai ma’asumai (a.s) suna da wilayar da Allah (s.w.t) ya sanya musu da wacce shari’a ta sanya musu duk gaba daya a kan muminai; sai dai cewa ita wilayar ta doru ne a kan wasu mas’lahohi wato wasu sharudda ...
 • Me ye alaka tsakanin Zuhudu da ci gaban zamani?
  5482 Halayen Nazari 2012/07/24
  Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin ...
 • A ina ne za a iya yin salla da taimama maimakon wankan janaba?
  4895 شرایط انتقال به تیمم 2014/02/12
  Idan dai mani ya fita daga gare shi ya samu janaba, to wanka ya zama wajibi kansa. Sai dai a wurare guda bakwai ne zai iya yin taimama maimakon wanka da suka hada da[1]: Idan ya zama ba shi da ...
 • Su waye “Tabi’ai” kuma meye matsayin tafsirin sahabbai da abin da ya fifita da shi
  237 Ilimin Kur'ani 2019/06/16
  Khadibul bagdadi yana cewa: Tabi’i shi ne wanda ya abokanci sahabi. Amma a cikin maganar da Hakim ya fadi akwai nuni kan saki ba kaidi kan tabi’i da cewa shi ne wanda ya hadu da sahabi kuma ya rawaito daga gare shi ko da kuwa bai abokance ...
 • Shin Ammar Dan Yasir ya temaka wa Imam Ali (a.s) kan lamarin da ya faru a SaKifa ko kuwa?
  320 سقیفه بنی ساعده 2018/11/04
  Mutane da dama sun tafi kan cewa Imam Ali shi ne shugabansu, amma yanayin yanda suke yi masa biyayya kuma suka sallam masa ya banbanta, babu tantama tun a farko Ammar ya kasance matemaki kuma mabiyu wanda ya sallamawa imama Ali (a.s) duk da cewa ta yiyu ...
 • Shin wace hanya ko salo zan bi wurin yin wa’azin addini?
  7127 تبلیغ و گفتگو 2012/08/15
  Wa’azi yana nufin isar da sakon Allah (s.w.t) zuwa ga jama’a. Kasantuwar sakonin Annabawa a dunkule abu guda ne, sannan sakon Fiyayyan Annabi (s.a.w) na masamman ne, da ya zo da nufin shiryar da bil Adama don fitar da shi daga duffai zuwa ga haske. A bisa haka ...
 • wanene mu”azu dan jabal?
  1442 برخی صحابیان 2016/07/12
  Mu”azu dan jabal dan amru dan ausu dan a”izu, ane masa alukunya da baban Abdurrahman, sannan ya na daga cikin mataimakan manzon Allah {s.a.w}.[1] mu”azu dan jabal tare da mutane 70 na daga cikin wadanda sukai mubaya”mar akaba sannan suka yi tarayya cikin yakoki ...
 • Shin mutum na da zabi? Yaya iyakar zabin sa yake?
  5667 Tsohon Kalam 2012/09/16
  Sau da yawa mukan sami kawunan mu baki a rayiwa kuma makadaita, sai ka ga mun samu kan mu a hanyar da ba makawa dole sai mun tafi a kanta, wannan ita ce tabbatacciyar hanyar rayuwar mu ta tuntuni, kuma hakan ya hada da wasu al'amura kamar ...
 • Zai yiwu ga fakihi ya damga ani ga Kur'ani alhalin ba shi da mukaddima ta ilmi?
  6496 بیشتر بدانیم 2012/09/16
  Abin da zamu kawo a dunkule shi ne msar tambayar. Hakika Kur'ani tushe ne daga tushen shari'a, kuma shi ake komawa don gane ra'ayin addini. Ba hakan nan ake istinbadi da Al-Kur'ani ba sai abubuwa biyu sun tabbata: kafa dalilin tabbatar da Al-Kur'anin, sannan ...
 • Wane addini ne Cikamakon Addinai?
  3460 Sabon Kalam 2012/07/23
  Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo. Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda ...

Mafi Dubawa