Please Wait
Dubawa
7106
Ranar Isar da Sako: 2019/05/18
Lambar Shafin fa1899 Lambar Bayani 99479
Jimilla Ilimin Sira,تاريخ کلام,تاريخ بزرگان,برخی صحابیان
Likawa masallaci|Musulami|Baitocin Waka
Takaitacciyar Tambaya
Wadannan Baitocin Waka Ammar Dan Yasir Ya Rera A Lokacin Da Ake Aiki Ginin Masallacin Manzo (S.A.W)?
SWALI
Wadannan Baitocin Waka Ammar Dan Yasir Ya Rera A Lokacin Da Ake Aiki Ginin Masallacin Manzo (S.A.W)?
Amsa a Dunkule
Allama majlisi a cikin biharu ya rubuta cewa: a lokacin da Manzo (s.a.w) tare da sahabbansa suka kasance suna gina masallaci sai wana sahabi ya zo wucewa ya tsaba ado yana sanye da tufafi mai kyau a lokacin Ammar Dan Yasir ya daga muryar ya yana mai rero wake yana mai cewa: ba za su taba zama daidai ba wadanda suka bada jikinsu da lokacinsu wajen gina masallaci kuma suke yin ruku’u da sujjada a cikinsa da wadannan da suke kangare wa kuma suke nuna kiyayyarsu ga masu yin hakan, sannan suke kin kura ta taba kwalliyarsu da kayansu na alfarma.[1]
Kuma inbi HisHama ma a cikin sirarsa ya rawaito wannan waken da Ammar dan Yasir ya rera. [2]      
 
[1] Ba zasu taba zama daya ba* wanda ya wanzu cikin raya masallatai kuma yana ruku’u da sujjada
Da wanda zaka gan shi mai jayyaya mai tsaurin kai* yana ta kokarin kauce wa kura.
A koma littafin Biharul Anwar na Allama majlisi mujalladi na 30 shafi na 238.
[2] Al- siran Al- nabawiyya j 1 shafi 142.