Kallon wannan fim din laifi ne kuma ya haramta, kuma lalle ne ki nisanci sake kallon sa, amma dangane da kallon farko wanda ba ki san me ya ke cikinsa ba shi ma kin yi laifi tun da tun a farko ya kamata ki gasgata babarki da ta gaya miki cewa ba komai a cikin sidin ya kamata ki dogara da abin da ta fada kuma kar tseguminki ya kai ki ga ganinsa. Na biyu, da zarar da kika ga farkon fitowa ya zam wajibi ki tsaya daga nan kuma kar ki ci gaba da gani. Amma a yanzo kar ki ci gaba da damun kan ki a kan wannan al’amarin ki je ki tuba tsakanin ki da ubangijinki, hakika ubangiji mai ramama ne mai jin kai kuma zai yi miki afwa ya yafe miki.
Jigogi masu alaka da wannan:
Karuwar karkata zuwa ga son yin jima’a ta hanyar kallon fina-finai masu tsaraici, 3086 (sait 3339)
Kallon fina-finai na ilimi wadanda ba tarbiyya a cikinsu 6817 (sait: 6904)
.