Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun kamala, wannan shi ne abin da zamu gano a wadannan ayoyi:
Amma shiriya ta kebanta ne ga masu hankali wadanda suke tunani, kuma ta rataya da abubuwa na shari'a kamar akida mai kyau da dokokin Allah abin da ya dace ayi da wanda bai dace ba, wannan shiriyar tazo ne ta hanyar Annabawa da Imamai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi irin wannan shiriyar ta game mutane gada daya kuma kyauta ce daga Allah yayi musu.
Dan haka duk mutane suna amfana da shiriya ta asali da ta shari'a
"إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا"
Hakika mun shiryar da mutum dan ya gane hanyar tauhidi, ko ya gode wa Allah (yin tauhidi, ko ya butulce masa (kin yin tauhidi).
Wannan hakika (dama) zabin shima irin shiriyarwa ce ta asali daga Allah, wannan saboda baya yiwuwa ya kasance mafarin zabin mutum da kansa saboda hakan zai jawo dawu (abu ya je ya dawo yaje ya dawo) ko kuma ta saysuli (abu ya zarce yayita tafiya ba tare da yazo karshe ba).
Kafin mu shiga bayani ya zama dole muyi nuni zuwa ga wasu alamomi masu muhiommanci:
((و لو شئنا لا تينا كل نفس هداها و لكن حق اقول منى لأملأن جهنم من الجنة والناس أجمعين))
Da munso da kowacce rai mun shiryar da ita, sai dai maganata ta tabbata kan cewa zamu cike Jahannama da Aljanu da mutane.[1]
((ربنا أعطى كل شيء خلقه ثم هدى) [2]قال تعالى : ألذ من خلق فسوى" والذمن قدر فهدمن))[3]
Ubangijimu shi ne wanda ya bawa komai kyautar halittarsa, bayan nan kuma ya shiryar da su.
Allah shi ne wanda ya yi halitta kuma ya dai daita ta, shi ne wanda ya iya kance komai sannan ya nuna masa hanya
Amma shiriya ta shari'a (Hidaya tashriyaya) shiriya ce kebantacciya wacce aka bawa masu hankali da tunani, kuma ta rataya da abubuwa na shari'a kamar akidoji na gaskiya da dokokin rila abin da ya kamata ayi da kuma abin da bai daceba, wannan shari'ar tazo ne daga wajen Annabawa da Imamai ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, Allah yana cewa: 4
((فريقا هدمن وفريقا حق عليهم الصلالة)).
Wasu bangaren Allah ya shiryar da su wa kuma bata ya fada musu.[4]
A wata ayar Allah ya ce: "والله يهدى من يشاء إلى صراط مستقم"
Allah ke ya shiryar da wanda yaso zuwa hanya madai-daiciya.[5]
Zamu gane cewa abin nufi da wannan shiriyar shiriya ce ta shari'a, kamar yadda shiriyar nan duk da yake ta kebanta da nufi ne ba ta da alaka da sauran ababan halitta, amma fa ta game dai-dai kun mutane (ko wanne mutum shari'a tana aiki a kan sa)
((وقل الحق من ربك فمن شاء فليؤمن ومن شاء فليكفر))[6]
"Ka fadi gaskiya duk wanda ya so ya yi imani, wanda ya so ya yi kafirci".
Allah ya kuma cewa:
((إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا))[7]
Tabbas mun nunawa mutum haya ko dai ya zama ya mika wuya ga Allah (godiyar ita ce muka wuya) ko kuma ya kafirce (ya ki gode masa), sabdoa haka, mutum idan ya so sai ya yi wani aiki idan bai so ba ba zai yi ba, wani mawaki ba'iraniye ya bayyana wasu baitoci yana cewa: "Hakika idan nace yi wannan ko wancan wannan yana nuna zabin mutum.[8]
Hakika wannan 'yancin wani bangare ne daga halittar mutum da kasancewarsa, kuma baya rabuwa da mutum a cikin kowanne yanayi cikin halaye, saboda haka mutum an dora shi a kan zabi da 'yanci, kuma da ya kasance wanda ake bawa zabi a cikin zabibn da aka bashi to fa a irin wannan yanayin zai iya zabar ya zamanto mara zabi ba a samun mutumn wanda zai zamanto mara zabi. To a nana zamu gane cewa asalin zabin mutum ba zai yiwu a ce shi ne mutum din ba idan ba haka ba to za a gamu da mushkilar daur (tafiyar abu gaba sa'annan ya dawo baya tare da maimaituwar hakan) ko kuma matsalar tasalsuli (abu ya zarce ba tare da yankewa ba). Shi mutum yana da zabin ayyukan sa, yana da 'yanci gwargwadon fidirar sa (asalin tsarin halittarsa) ko ya aikata ko ya bari wannan ce hidaya takwiniyya.
Idan muka kalli wadannan nukudodi da aka ambata da idon lura kuma kamar yadda aya ta bayyana za mu ga hidaya takwiniyya (shirya ta asali) ta game komai. Tabbas mutum ya sami sharafin hidaya tashri'iyya bayan ya sami hidaya takwiniyya. Sai dai idan an duba za a ga mutum an halicce shi yana dauke da siffar zabi da 'yanci a dabi'ar sa da asalinsa, don haka ne yana da zabi dangane da neman taimakon shiriyar Allah (hidaya tasari'iyya) don ya share fagen samun shiriya babba, kamar yadda yake da ikon ya zabi yon tawaye ga shari'ar har ma kuma ya kau da kai daga gare ta har ya shiga wata hanyar da ba waccan ba, wanda karshen al'amari sai ya fada cikin kafirci da zalunci.
Ayar da muka kawo a farkon bayanin mu tana bada hasken cewa zamu iya gano cewa manufar Allah idan ta so zata iya sanya mutum halinsa ya zama tamkar na ragowar halittu wadanda basu da zabi (dabbobi da sauran su), sai dai manufar Allah ta bawa kowanne mutum shiriya ta asali da ta shari'a, kuma a dai-dai wannan lokacin ta ba shi 'yanci da hakkin zabi wanda wannan shi ne ya sa mutum aka dora masa nauyi (taklifi) dan ya banbance gaskiya daga karya.
Ya bayyana a fili da'awar cewa Allah Allah madaukakin sarki bai yi nufin shiryar da baki dayan mutane ba wannan idan mun dogara da aya 13 a suratus Sajda, wannan da'awar da'awa ce mara kyau, sabanin wannan maganar shi ne dai-dai domin Allah ya yi nufin shiryar da duk halitta, sai dai yadda sunnar Allah take gudana mutumin da ya zabi bin hanya mai duhu da zalunci har ma da kafirci to shiriya ta ALlah ba zata same shi ba, domin ba zai yiwu shiriyar Allah ta rataya da shi ba[9] amam mutumin da ya zabi tafiya a cikin hanyar gaskiya zai dace da samun shiriyar babba[10] Allah ya ce:
((والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا وإن الله لمع المحسنين))
"Duk waanda suka yi kokari saboda mu to tabbas za mu nuna musu tare da shiryar da su hanyar mu, hakika Allah yana tare da masu kyautatawa". [11]da[12]
[1] Sajda, 13.
[2] Daha, 50.
[3] A'ala, 2-3.
[4] A'araf, 30.
[5] Bakara, 213.
[6] Kahfi, 29.
[7] Insan, 3
[8] Maulawiy, Masnawiy ma'anawiy.
[9] Duba Albakara 264, Ma'ida 67, Tauba 37, Tauba 80.
[10] Duba Albakara 264, Ma'ida 67, Tauba 37, Tauba 80.
[11] Ankabut, 69.
[12] Mun dogara da littattafan da zamu kawo a wajen bada amsa: Allama tabataba'iy Tafsirul Mizan, I 14 sh 214 sh 214 sh 66 j17, sh 167, j32, sh 80. Makarimushshiyraziy, Tafsirul Amsal fi Tafsiri Kitabullahil Munazzal): I 1, sh 67 da 430 da j2 sh 259 da abinda ya zo baya j17, sh 166 da abinda ya zo baya da j25, sh 366 da j11 365, 233 har ya zuwa sh 226 da 420 da abinda ke bayansa.