Ruwayar da take da alaka da haduwa Salmanul farisi da Sayyida Zahara (a.s) wacce aka kawo ta kan wancan tambaya- a wasu litattafan shi’a an nakalto ta daga cikinsu akwai littafin muhujul da’awat da minhajul ibadat na wallafar Sayyid ibini Dawus wanda ya yi wafati a shekara 664 hijri, wanda isnadin wannan ruwaya ya kasance kamar haka: daga Shekh Ali bin Abdus-samad ya ce shekk kakana ya ba mu labari ya ce masanin fikihu Abu Hassan Allah ya jikan rai ya ba mu labari ya ce: Sayyid Shaik Alimi Abu barakat Ali bin Husaini Hasani aljauzi ya zantar da mu ya ce shekh Abu Jafar Muhammad bin Ali bin Husaini bin Musa bin babawaihil kummi masanin fikihu (r.a) ya zantar da mu ya ce: Hassan bin muhammad bin Sa’id kufi ya zantar da mu ya ce: Furatu bin Ibrahim ya zantar da mu ya ce: Jafar bin muhammad bin Bishrawaihi kaddanu ya zantar da mu ya ce: muhammad bin Idris bin Sa’id Ansari ya zantar da mu ya ce: Dauda bin Rashid da walid bin shuja’u bin marwanu daga Asimu daga Abdullah bin Salmanu farisi daga babansa ya zantar damu ya ce:
[1]
Wannan ruwaya ce mai tsayi wacce a wannan mahalli da muke ciki ka dai za a tarjama iya inda a ka yi tambaya kansa: ya zo cikin ruwayar cewa: Salmanu farisi yana cewa: kwanaki goma bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) na fito daga gida na nufi gidan Sayyida fatima (a.s) sai Ali ya ce mini” ya kai salmanu bayan wafatin manzon Allah ka yi mana jafa’i ya masoyina ya Abu Hassan ni ban yi muku jafa’i ba, sai dai cewa bakin ciki da jimamin rashin manzon Allah (s.a.w) ya hana ni zuwa ziyarar ku, sai Imam Ali ya ce mini: ya kai salmanu taho mu tafi gidan fatima yar manzon Allah; saboda ita tana son yi maka wata kyauta kuma tana begen ganinka tana son baka tsarabar da aka kawo mata daga aljanna, Salmanu yana cewa: sai na nufi gidan Fatima (a.s) bayan na shiga cikin gidan sai na ga Fatima (a.s) zaune sannan tana lullufe da wata yankin abaya sai dai cewa abayar duk sanda ta yunkura jawota kan kwaurin kafarta kanta zai yaye haka ma duk sanda ta jawota kanta sai kwaurinta ya yaye, lokacin da ta ga Salmanu sai ta lullufe kanta da wannan abaya, sannan Sayyida Fatima ta ce: ya kai Salmanu hakika kai tun bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) ka yi mana jafa’i ko? Sai na ce: ya ke yar manzon Allah, shin zai iya yiwuwa a ce ni na yi miki jafa’i? Fatima (a.s) ta ce to zauna ka saurari abin da zan gaya maka ka hankalce shi sosa.
[2]
Idan ana son samun ingantacciyar fahimta daga wannan ruwaya dole a nutsu a lura da wadannan nukdodi:
-
Wasu daga cikin marawaitan wannan ruwaya mutane da ba a ma san sunayensu ba ne a litattafan ilimin mazajen hadisi saboda haka ruwayar isnadinta ba ingantacce ba ne.[3]
-
Wannan ruwaya ibin Dawus ya kawo ta ne a babin cewa Sayyida Zahara (a.s) ta bai wa salmanu wata addu’a ne don kariya daga zazzabi[4] ana kiransa da sunan (hirzun Sayyida fatima)[5]
-
Batun cewa Fatima ta yi shaukin ganin salmanul farisi, ba ta da wata matsala da ma’asumancinta da kamewarta; saboda idan da ka lura da farkon hadisin da karshensa zaka fuskanci cewa lallai wannan haduwa ta faru bayan kwanaki goma da wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan Imam Ali da Sayyida Zahara (a.s) sakamakon wannan babban rashi da bakin ciki zuciyarsu ta shiga kadaici sai ya zama suna begen ganin Salmanu, wanda ya kasance abin girmama da kauna a wajen manzon Allah (s.a.w) da yadda ya samu kusanci dasu wanda ya kai ga cewa suna kirga shi daya daga cikin danginsu har ta kai ga manzon Allah yana ce masa (Salmanu daya daga cikinmu yake Ahlilbaiti).
Sai ya yi sauri ya tafi ganinsu domin ya yi tarayya da su cikin bakin cikinsu da kadaicinsu, ta wannan fuska a lokacin da Imam Ali (a.s) ya ga Salmanu sai ya soki lamirinsa ya ce masa ya Salmanu bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) ka yi mana jafa’i ne? Sai Salmanu daga wannan lokaci ya fadaka cewa Fatima (a.s) ma tana begen ganinsa ta na kuma son ba shi wata tsaraba da aka kawo mata daga aljanna, saboda haka shi wannan shauki da begen ta fuskar shari’a ba shi da wata matsala.
Na hudu: Idan ka yi duba tare da lura zaka ga an nakalto a cikin tarihi da sira kan tsari da shakalin hijabi da tufafin Sayyida Fatima (a.s) zaka iya kai wa ga wanna sakamakon cewa ita a kowanne lokaci tare da wanda ba muharraminta ba tana cikakken kiyaye hijabi da tufafinta, sai dai cewa tana kiyaye matsakaicin haddi wanda hakan wani abin koyi ne ga sauran matan musulmai. Bisa la’akari da wannan nukuda ko matashiya daga bangaren da ya zo a ruwayar da cewa (sai kwatsaham na same ta zaune kanta akwai wani kyalle daga abaya wacce idan ta lullube kanta kwaurinta zai yaye idan kuma ta rufe kwaurunta kanta zai yaye) ya kamata a ce Salmanu kadai dai yana bayanin kaya ne wanda hakan yake nuna saukin kan Sayyida Fatima (a.s), ba wai hakika kwaurin kafarta ya kasance tsirara ba ne, Allah ya tsare mu daga wannan tunani. Kari kan wannan bayani ya zo a ruwayoyi da dama cewa mataye gama gari a wancan zamani suna sanya dogon wando a kasan abayarsu manzon Allah (s.a.w) yana cewa: (Allah ya yi rahama ga macen da take rufe kafafuwanta take sanya wandon kirki)
[6] da wannan siffantawa ta kaka za ace Sayyida Zahara (a.s) wacce take da mukamin isma da kamewa da jin kunya a ce ba zata sanya wannan dogon wando kasan abayarta da take gajeriya ba? Saboda haka tabbas a kasan wannan abayar tana sanye da wani tufafin.
Bisa la’akari da wadannan nukdodi cikin sauki zamu iya banbancewa tsakanin shauki da koyar da addu’a cikin abin da ya zo a cikin tambayar, sannan ya kamata mu san cewa wasu sun yi wa wannan hadisin mummunar fahimta da ganin cewa ba sa kiyaye hukunce- hukuncen shari’a ba a tsakaninsu, dangane da muharrami da wanda ba muharraminsu ba, tabbas wannan kiyasin da suke yi gurbatacce ne.
Dubawa da gyara kermani [1] Muhujud da’awat . minhajul; ibadat: sh 5-6 wallafar ibn dawus Aliyu bn musa
[2] Muhujud da’awat. Minhajul ibadat wallafar ibn dawus Ali bn musa sh 5-6. Biharul anwar juz 43 sh 66 manakib sh 297-298
[4] Tambaya mai lamba 28424
[5] Muhujud da’awat: 5 hirzu maulatina fatima alaihas salam
[6] Manla yahaduruhl fakihu juz na 3 sh 467