Alkur'ani mai girma ya ambata a fili sosai, game da mas'alar gina masallaci a kan kaburburan As- habul Kahafi, a inda ya ambaci labarinsu, kuma ya halatta shi ne, bai hana ba, a'a sai dai ma, ya ambace shi ne, yana mai karfafa shi, a matsayin wani al-amari ne mai kyau.
Akwai kuma ruwayoyi masu yawa, wadanda ba wai kawai suna nuna halaccin yin ibada a kusa da kabari ne kawai ba, a'a, suna ma nuna cewa yin ibadar tana da lada ninkin ba ninkin, a wani bangare na uku kuma akwai ruwayoyin da a dubi na farko za a ga kamar sun saba daga ita wannan ayar mai girma da gungun ruwayoyi na farko, sai dai kuma dole ne a fahimci cewa abubuwan da suke faruwa, da wasu al'amura na zaman takewa, kamar yin ridda zuwa ga shirka, da fankamar yawa, da alfahari, da rashin hakuri da juriya, da wasu tunanunnuka na bata wadanda ba su dace da addinin musulunci ba, da wadanda suke barazana ga al'ummar musulmi suna daga cikin jimillar dalilan da suke sa wa a hana mutane, su nuna tsananin karkata ta wajen muhimmantar da kaburbura daga imamai ma’asumai, (a.s)
kari a kan haka kuma shi ne cewa idan muka duba gamammiyar al’adar musulmi, da kuma na Ahlul baiti (a.s) a kebance zamu gan su suna gani da idanuwansu yanda aka yi gini a kan kabarin Manzo mafi girma (Sallal lahu alaihi wa alihi) da imamai na farko kamar Imam Husaini (a.s) amma ba su hana ba, kuma matafiya da malaman tarihi sun labarta mana labarin kubbobi da yin gini a kan kaburbura, a kan idon malaman musulunci gaba dayansu, a nan ga kabarin da ake darajantawa na Abu Hanifah, a can kuma akwai kabarin Abdul Kadir, na uku kuma ga na Malam Wane, ….
kuma dadin da dawa a kan hakan, wannan dabi’ar ta watsu a cikin dukkan kasashen duniyar musulunci, tun daga arewacin Afurka har zuwa kasar Indiya, da kasashen da suka yi makwabtaka da su.
Ba a taba hanawa ba, sai a shekaru dari biyu da suka wuce, daga wasu da suke daukar kansu a matsayin masu kare tauhidi, kai kace dukkan Malaman Musulunci, a tsawon shekaru darurruka, ba su fahimci abin da wahabiyawa suka fahimta ba!!.
Kuma wannan yana nuna kasancewar dukkan Malaman mazhabobi, suna fahimtar ruwayoyin hanin nan da wata fassara ce ta daban, wacce ba ta kore halaccin gina kubbobi a kai ba.