advanced Search
Dubawa
22247
Ranar Isar da Sako: 2012/04/15
Takaitacciyar Tambaya
Me nene hakikanin zunubi? Menene hakika tasirin sa ga ruhin mutum da ransa? Kuma yaya zamu kubuta daga wadannan guraban?
SWALI
Me nene hakikanin zunubi? Menene hakika tasirin sa ga ruhin mutum da ransa? Kuma yaya zamu kubuta daga wadannan guraban?
Amsa a Dunkule

Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4):

  1. Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi shi ne wanda ke bin sha'awa da fushi, maimakon ya bi hankalinsa saboda haka sai ya zamana cewa zai iya yin laifi wannan yanayin (sha'a da fushi), idan mutum ya yi sabo to fa ya ha'inci kansa. Zunubi tarkon shaidan ne wanda badinin sa wuta ce zahirin sa kuma jin dadi da sha'awa wacce take jefa rafkananne a cikin azabar Allah saboda kwadayi.
  2. Gurbin laifuffuka: laifuffuka suna da gurbi (kanta) mai nuni a kan mutum shi kansa da kuma al'umma, gurbin laifuffuka a kan mutum shi kadai sun hada da bushewar zuciya da kuncin rai kai har ma da rashin ma'arifa (ilmin sanin Allah) da wasu sirrikan da Allah ke sanar da bayi, kuma a karshe zuciyar mutum sai ta zama mazaunin shaidan kuma zunubai suna hana mutum ya gane illar da ke tattare da ashi  a cikin zuciyarsa ko ruhinsa, har ma ya kasa gane mahaliccinsa, ya kuma rasa riskar jin dadin ganawa da Ubangijinsa, har da karbar ayyuka, zai iya musun zuwan ranar sakamako. Ta bangaren da guraban da suke shafar al'umma kuwa, zunubai na sabbaba abubuan da suka hada da kaskanci da ci bayan al'umma, ko da kuwa al'ummar mai ci gaba ce a fili idan dai ta afka cikin kura-kurai da badala tabbas ma'aunin darajar mutumtaka da dabi'u masu kyau zausu gushe kuma su watse gaba daya.
  3. Asalin zunubi: malaman addini sun karfafa abubuwa guda biyu cewa su ne asalin laifuffuka, jahilci da shagala, hakika mafi girman makamin makiyi (shaidan) ko damar sa ta farkon wajen sa mutum yin laifuffuka ita ec gafala da jahilci, kuma wannan shi ne tushen barna, kamar jahiltar matsayin dan Adam da abubuwan da suke bawa mutum ci gaba da kuma jahiltar gurabba masu girma kamar kamewa da tsarki har da jahiltar makomar mai yin laifuffuka da sauran su.
  4. Hanyar tsira: akwai hanyoyi da yawa,
  • Tuba da yin istigfari: ma'ana tuba shi ne komawa ga Allah tare da niyyar barin sabawa Allah, hakan yana da matakai.
  • Tuna laifin
  • Tuna Allah tare da ambatonsa.
  • Manufar mutum
Amsa Dalla-dalla

Zunubi ma'anarsa laifi da sabawa, hakan na nufin kin bin umarni da kuskure tare da karkacewa gaskiya (dai-dai) da kuma sabawa umarnin Ubangiji da haninsa: abin nufi shi ne aikata aikin da Allah baya so, har ma yake zargin bawa akai saboda ba shi da kyau, ko kuma mutum ya bar wajibin da Allah ya dora masa, idan mun yi la'akari da wannan, zunubi shi ne sabawa hakkin bauta.

Hakika mutum mai zunubi yana gabatar da sha'awarsa da fushinsa har ya sanya su a gurbin hankalin sa da ya gushe, alhalin su (sha'awar da fushi) rassa ne na mutum, abin da ya kamata a nan ya bi hankalinsa ba wai ya bari sha'awa da fushi su maye gurbin hankali ba, a irin wannan lokacin sha'awa da fushi su suke da ragamar mutum saboda haka sai su afkar da mutum cikin laifuffuka, sanadiyyar haka duk aikin da zai yi sai ka ga ya dace da sha'awarsa ko aiki irin na masu fushi, to wannan shi ne aikata laifuffuka. Kuma bugu da kari kamar yadda mutum aka hana shi ha'intar 'yan uwansa haka ma an hana shi ha'intar kansa. Idan mutum ya ajiye sha'awar sa da fushinsa a gurbin hankali mai kyautata aiki, idan mutum ya ajiye tunani mara kyau da zato a mahallin hankali mai taimakawa nazari sai ya zama mai fushi karshenta kuma ya ha'inci kansa, idan mutum ya zama mai ha'inci a wajen sanin Allah to fa zai jarrabtu da ha'inci a lokacin aiki kuma ba zai kiyaye hakkokin sa ba.[1]

 

Zunubi Tarkon Shaidan Ne:

Bayani ya zo a riwayoyin ahlul-baiti amincin Allah ya kara tabbata a gare shi game da abin da ya shafi kayan duniya cewa tarkon shaidan ne, zunubai kuma suma tarkon shaidan ne: ma'ana shaidan yana farautar mutane ta hanyar sa su yin laifuffuka, saboda haka yana yin amfani da tarkon har ma da dabaibayi ya daure masu laifi. Wannan tarkon fa iri daban-daban ne wani karami ne wani babba. Shaidan yana yaudarar kowa ta hanyoyi daban-daban wasu ya yaudare su da samun dukiya wasu da samun shugabanci ko makami wasu kuma da sha'awar jima'i da sauransu.

 Tabbas wutar jahannama tana tare da jiye-jiyen dadi da sha'awa, ma'ana abin da ke cikin tarkon nan wuta ce, a waje kuma kofin sha'awa, mutum yana fadawa cuikin makogwaron wuta saboda kwadayin kofin sha'awa[2] gurbin zunubai.

Gurbin laifuffuka ya kasu kashi biyu, na dai-daiku da na kowa da kowa:

  • Gurbin Dai-daiku

Gurbin dai-daiku shi ne:

  1. Ainihin laifi tsatsace wacce ta ke jawo duhun ruhi, mutum bayan ya yi zunubai baccinsa ba ya kyau saboda ba ya samun ma'arifa ta hanyar mafarki, sannan farkawarsa ma bata da kyau saboda ba ya iya gano wani ilmi mai inganci ballanta ya sanar da wasu. Idan muka dauki wannan maganar to idan ruhi (rai) ya yi duhu to sirruka da yawa suna buya, kuma wannan ran shi ne Allah ya sanya masa ilhama har ma Allah ya rantse da shi, haka nan ma abin da ya wajaba ga mai yunkurin gyaran ruhinsa ya karanta magana kuma ya lura da abin da yake ci (halal ne ko haram) duk wannan fa don saboda ya sami baiwar ilhama daga Allah, saboida idan yana son ya ji magana ta ciki (wato ilhama) sai ya karanta magana.[3]
  2. A lokacin da mutum ya zama karkashin jagorancin shaidan ya kuma karbi waswasin sa ya yi aiki da shi, to a hankali zuciyar sa zata zama gidan shaidan sai ya zama mai yiwa shaidan liyafa. Wannan an anbace shi a ayoyi madaukaka[4], saboda haka, zuciyar mutum makaryaci wajen saukar shaidan ce. Amman mutumin da ya zamanto amintacce a cikin mas'alolin ilmi mai cika alkawari, har ma ya zama amintacce a cikin sha'anin dukiya mai cika alkawari to Allah ba zai bar zuciyar sa ta zama gidan shaidan ba.[5]
  3. Zunibu yana hana nafsu samun ilmi na ma'arifa (wato nafsu ta gane kanta, sannan ta gane Ubangijin ta): Hakika mutum bayan ya yi sabo a hankali fa zai mance Allah, sai wannan mantuwar ta zame masa hijabin da zai hana shi samun ma'arifa, wannan mantuwar ba zata bar shi ya san wani abu ba har nafsu dinsa ma ba zai gane ta ba.[6]

Hakika mutumin da ya jarabtu da laifuffuka ya fadar da kansa har abada kuma ya daure kansa da madaurin da ko wutar jahannama ba zata kwance masa ba, domin wuta tana iya tausasa bakin karfe idan ya zama wuta: abin da ake nufi ainihin wutar ta bayyana da surar bakin kakarfe saboda haka ba abin da zai iya narkar da shi.[7]

  1. Daya gurbin na sabo shi ne idan mai sabo zai rasa jin dadin ganawa da Ubangiji, to fa yana cikin dauwamammiyar asara domin ba zai ji dadin ibada ba sai dai saboda zunubi da busharar zuciya, zai rasa wannan damar. Hakika Shaiku Saduk ya rawaito a littafinsa mai kiyma (tauhid) daga Imam Ridha amincin Allah ya kara tabbata a gare shi wani mutum ya tambaye shi wasu mas'aloli daga ciki ya tambaye shi game da Allah ya ce: saboda me ba a ganin Allah? Abul Hassan sai ya ce: "Hijabin da ke tsa kanin Allah da halittar sa (laifuffukan su) shi ne yake hana ganin fidira (asalin tauhidi) kuma ba zai bar mutum ya ga Ubangijinsa ba da idon fidira".[8]

A musulunci, Hadisai da yawa sun zo suna karfafa cewa zunubai suna zama hijabi kamar inda Annabi (SAW0 yake cewa: "Hakika bawa idan ya yi zunubi sai bakin digo ya fito a zuciyar sa, idan ya tuba ya daina ya yi istigfari sai bakin ya goge idan kuma ya sake yin laifi sai bakin ya karu har ya rufe zuciyar sa".[9]

Annabi (tsira da amincin allah su akaratabba ta agare shi) yana cewa a cikin wani hadisin: "Yawan zunubi yana bata zuciya".

An karbo daga Imam sadik amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: "ba abin da ya fi laifi bata zuciya, hakika laifi yana fadawa zuciya har sai ya rinjaye ta har samanta ya dawo kasa". Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: "Inna yi maka wasiyya da jin tsoron Allah da tsantseni da kokari, ka sani kokari baya amfani idan ba tsantseni". Ya zo a hadisin Annabi wanda yayiwa Abu Zarri magana yake cewa: "ya Aba Zarri, asalin addinio tsantse kansa kuma biyayya... ka sani ko kun yti sallah har kuka zama kamar baka, kuka yi azumi har kuka zama kamar tsirkiya wannan duk ba zai yi muku amfani ba idan ba tsantseni ya Aba Zarri hakika masu tsantseni da gudun duniya su ne waliyyan Allah na hakika".[10]

  1. Musul alkiyama: Hakika zunubi yana hana yarda da lahira, zai yiwu mutum ya san akwai alkiyama sai dai wannan sanin na sa sai ya zama an binne shi (an rufe shi) a karkashin tsatsar sha'awa saboda haka ilimin sa ba zai yi tasiri ba,[11] Kur'ani ya yi ishara a cikn suratul Mudaffifina a kan masu musun alkiyama inda ya ce: "Su ne masu karyata alkiyama (ranar sakamako) ba mai karyata alkiyama sai dan ta'adda mai laifi, idan aka karanta masa ayoyin mu sai ya ce tatsuniyoyin mutanen farko ne"[12] Sannan Kur'ani yake cewa: "ina! aikin da suke aikatawa ya yi kanta a zuciyar su".[13] Zamu gane daga wadannan ayoyin cewa zunubi yana tafiyar da tsarkin zuciya ta yadda abubuwan gaskiyan ba sa sanyawa a cikin mabudin Ubangiji. Idan kuwa ba haka ba ayoyin gaskiya a bayyana suke a fili musamman abin da ya shafi halitta da alkiyama.[14]

 

Gurbin Laifi A Zamantakewa:

Laifuffuka suna mai da al'umma baya da yawaitar laifuffuka da kuma lalacewa wacce take daga tasirin dai-daikun mutane. Idan an kalli gefen gurbin laifuffuka sai su hana ci gaban al'umma kai har ma a zamantakewar turawan yamma masu laifi su ne koma baya na can kasa a al'ummar su, kuma su ne basu da wata kima.

Asalin Zunubi Gafala Da Jahilci:

Tabbas mafi girman makamin makiyi kuma farkon samun damarsa - a kan mutum - ta hanyar gafala ne, saboda haka idan shaidan ya gafalar da mutum ba zai bukaci kawata masa abubuwa ba, ba kuma sai ya sanya masa jahilci mai yawa ba, idan dai wannan sawar ta gushe (tuna Allah) to shaidan ya sami nutsuwa (saboda zai sami biyan bukatarsa). Jahilci shi ne asalin yaduwa da watsuwar barna. Ayoyin Kur'ani wadanda suka kawo kissar Annabi Yusuf sun yi nuni a kan begen da ya cudanya da zunubi da sha'awar jinsi duk wannan sun faru ne saboda jahilci da rashin ilimi, kamar jahiltar darajar mutum, da jahiltar gurabba masu girma na kamun kai da tsarki, da jahiltar karshen abin da zunubi ke jawowa kai har ma da jahiltar umarnin Allah da abubuwan da Allah ya hana[15].

 

Hanyar Kubuta Daga Zunubi:

Zai yiwu mu ambaci hanyoyin kubuta daga zunubi akwai:

  1. Tuba daga zunubi[16] da istigfari: tuba a yare yana nufin dawowa, lokacin da bawa ya dawowa Ubangijin sa sai ace: ya tuba, Allah ya umarci baki dayan muminai da su tuba[17] a cikin Kur'ani.
  2. Tuna zunubin.[18]
  3. Tuna Allah da ambatonsa[19]
  4. Nufin mutum[20] da.[21]

 


[1] Jawadi Amuly, Abdullahi, marahilul aklaki fil Kur'ani sh 332-334.

[2] nahjul balaga, huduba 176: jawadiy Amuly mabadi'ul akhlak sh 318, Maulanarrakiy, jami'ussa'adat, sh 194, jawadiy amuly, Tasniym, j2 sh 400.

[3] Jawadiy Amuly, marahlul akhlak, sh 155-159.

[4]  Ashshu'ara, 221-222.

[5]  Jawadiy Amuly, Mabadi'ul Akhlak, sh 111.

[6] Almujadala, 19.

[7] Jawadiy Amuliy, Mabadi'ul akhlak sh 235-236.

[8] Tauhidussadak, sh 151: jawadiy Amuliy Alfidratu fil Kur'an, sh 103.

[9] Tafsirul Kurdubiy, j10, sh 705: Ruhul ma'ani j30, sh 73.

[10] Kulaini, Usulul kafi, j2, Babuzzunub; j1 da 13: Makari-mushiraziy, risalatul Kur'an.

[11]  Al-Jasiya, 23: Jawadiy Amuly, tafsiruttasniym; j2, sh 203.

[12] Suratul Mudaffifina, 11-14.

[13] Suratul Mudaffifina, 11-14.

[14] Mukarimushshiraziy, Risalatul Kur'an, j1, sh 361: Tafsiru fakhruddeenir-raziy, j31, sh 94.

[15]  Jawadiy Amuly; TafsTasniym, j3, sh 397: makarimush-shiraziy, Risalatul Kur'an, j1, sh 88.

[16] Suratun Nur, 31.

[17]Nahjul Balaga, sh 128, hikima 409: al'maula Ahmadun Narakiy, mi'irajussa'ada, sh 669: shgahidul mudahhari, falsafatul akhlak, sh 164.

[18] jawadiy Amuly mabadi'ul akhlak, sh 55-56.

[19] Suratul Ahzab, 41.

[20] Jawadiy Amuly, mabadi'ul akhlak, 237.

[21] Maudu'ai masu dangantaka: shiriya da zabi: taka rawar mutum wajen samun arziki.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa