Hanyoyin Amfani (2)

Hanyoyin yin Tambaya

Tun da tambayoyin mutum ba su da iyaka, kuma ikon mutane da cibiyoyi na bayar da amsa yana da iyaka, to masu tambaya zasu iya taimaka mana ta hanyar wannan shawarwari da zamu bayar domin ku taimaka mana mu samu amfana da damar da tafi dacewa. Kuma tambayoyin da ba su yi daidai da wannan bayanin ba, to zai iya yiwuwa su fita daga cikin jerin tambayoyi, ko da yake za a sanar da mai tambaya game da dalilin hakan.

1. Kada tambaya ta kasance sama da abin da ake bukata, wato kada amsarta ta bukaci shafuka masu yawa; misali “Mece ce mahangar musulunci game da mutum?”, wannan wata tambaya ce mai fadi wacce amsata yake bukatar rubuta littafi guda. Ko kuma mai tambaya ya nemi nakadin wani littafi cikakke wacce zata iya bukatar amsa da zata yi littafi mai girma fiye da littafin da ake yi wa nakadin ma.

 2. Tambayarku kada ta kasance ta mutum daya kawai ta yadda sauran mutane ba zasu iya amfana da ita ba; misali mutum ya yi tambaya game da fassarar wani mafarki da ya yi, ko wata matsala ta danginsa tsakanin mutane biyu wacce zata nuna kebanta da wadannan mutanen kawai.

3. Tambaya ta kasance cikin mas’alolin addini. Don haka tambaya kamar “yaya tsohon sunan garin Karman” ko kuma “hakikanin haske current ne ko atom”, ba sa cikin tambayoyin da wannan sayet zai iya amsawa.  

4. Idan a tambaya an ciro wata magana daga wani littafi ko makala, ko wani shafin intanet ko huduba, da sauran su, to ya zama dole a kawo su, don mika wannan madogarar maganar a hannun masu aiki shafin intanet ya zama yana da saukin samu gun su.

5. Sannan yana da kyau kada a kawo sama da mas’ala daya a cikin tambaya daya.

6. Idan amsa tambaya yana bukatar lokaci mai yawa, to da farko za a aiko muku da amsa a dunkule ne, sannan bayan an gama binciken amsa, daga baya sai a aiko da amsa dalla-dalla.

7. Yakamata matanin tambaya ya kasance babu wani abu a dunkule, kuma ya kasance da rubutu mai kyau tsararre domin a samu damar ba ku amsar abin da kuke nufi a tambayarku.

8. Bisa la’akari da tambayoyin da aka bayar da amsarsu a wannan shafin da suke a bangaren tambaya, ku yi kokari da farko ku duba tambayoyinku a wadannan bangarorin tukun, idan ba ku samu cikakkiyar amsarku ba, to sai ku yi tambayarku.

9. Yana da kyau a yi amfani da magana mai ladabi a matanin tambayarku.

10. Wannan shafin ba ya daukar nauyin bayar da amsar da ta zama tana kan mai tambaya ne. Don haka ba ya bayar da amsar rubutun da yake kan marubuci kamar makaloli, risalar gama karatu… duk ba sa kan wannan shafin.

11. Duk da cewa muna kokarin ganin ba mu bar duk wata tambayar addini ba tare da mun amsa ta ba, amma saboda yanayin da yake wakana na samun rikice-rikice, idan muka ga akwai cutuwa wurin bayar da amsa ga wata tambaya, to za a ki bayar da amsa, ko kuma a jinkirta bayar da amsa har zuwa wani lokaci.

 12. Duba ga cewa ma’aikatan wannan shafin na intanet suna bisa matakai mabambanta na ilimi ne, kuma sanin su ga mas’alolin addini yana da bambanci, to ana kokari ne na ganin cewa amsar da aka bayar ba ta takaita da amfanin mai tambaya ba, za a yi kokarin ganin an bayar da amsa ne yadda sauran masu tambaya ma zasu iya amfana daga gare ta.

13. Idan akwai amsar tambayar mai tambaya da muka ga ta dace akwai ta a wani shafin na intanet, to zai iya yuwuwa mu bayar da wannan amsar ga mai tambaya ta hanyar gaya masa adres din wannan amsar.

14. Mai tambaya, mu kokarinmu shi ne mu bayar da amsar ilimi gare ka, ingantacciya kuma mai zurfi, amma idan ba ka samu gamsuwa da amsarmu ba, ko kuma ba a samu dacewar tambaya da dokokin bayar da amsarmu ba don haka ba ku samu amsarku ba, to yana da kyau ku yi kokarin ganin kun samu amsar ta wata hanayar.

Muna godiya ga dukkan masu tambaya

Bangaren bincike yana daga cikin mafi muhimmancin sabon abin da aka kara wa wannan shafin. Wannan bangaren yana da abubuwa da yawa wadanda zasu iya taimaka muku bincike a wannan shafin. Kuma zai nuna muku hanyar aiki da bincike dalla-dalla a wannan shafin.

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa

Linkoki