advanced Search
Dubawa
14250
Ranar Isar da Sako: 2007/06/09
Takaitacciyar Tambaya
shin ahalissunna sun canzama ayoyin gadir da zuka zo a cikin kur'ani wuri?
SWALI
wasu suna da mahangar cewa ahalissunna sun canzama ayoyin gadir da suka zo cikin kur'ani wuri, domin boye asalin hakikanin ayar wato khilafanci imam Ali (a.s)? Mine ne mahangar ka a kan canza wannan ayar wato ayar gadir muna bukatar bayani.
Amsa a Dunkule

Mafiya yawa na masu fassarar kur'ani daga bangaren sunna da shi'a, sun tafi akan cewa; اليوم يئس الذين  jimlace wadda tazo tsakanin aya ta ukku ta suratul ma'ida dan haka acin ilimin nahawu bata da muhalli na li'irabi. Kuma mafiwa yawancin su suna ganin wannan ta'aruz din ya faru ne tun farko da kuma ummurnin manzo Allah; saboda Allah madaukaki ya dora nauyi shirya kur'ani a hannun manzon sa. Amma abunda ya shafi dora nauyin shirya ayoyin a hunnun al'umma kuma shiryawar a matsayin kur'ani cikake wanda yake a matsayin mu'ujiza ta Allah wanda shi ne aiki da kuma Magana daya ta Allah ta'ala, tayi karo da abunda muka fada a baya wato dora aikin hunnun manzon Allah: saboda daya daga cikin asashe na mu'ujizar kur'ani shi ne tsari da yadda aka shirya shi. musan cewa in aka canza wani bangare ko tsarin shi {kur'ani} akan tsarin san a farko to zai rushe kuma ya rasa matsayin sa na abu daya.

Amma cewa ahalissunna sun canza ma wasu ayoyi wuri domin boye gaskiyar khilafanci imam Ali (a.s), wannan tunanin abun korewana ne: saboda taka tsan-tsan na manzon Allah akan kiyaye kur'ani mai girma, kuma rubuta kur'ani ya faru ne ta hannun manyan sahabban shi mai tsira da aminci da yayan gidan sa, kamar irin su imam Ali {a.s} da dan abbas da sauran makamantan su. Wannan shi zai hani ga kawo canji ko kari ko kuma canza ma wasu ayoyin wuri.

Kuma abun korewa ne cewa a zamanin khalifofi ukku an canza ko kuma anyi kari a cikin ayoyin kur'ani, saboda kur'anan da ke hannun yanzu an hada sune bisa ummurnin usman sannan bayan gama hadawa sai yasa aka aika su zuwa sauran garuruwa, kuma imam Ali {a.s} ya yarda da wannan kur'anan domin kuwa imam bai kawo wani abu ba wanda yake nuni da kari ko canji na ayoyi da khalifofin da suka zo kafin shi su ka yi ba.

A zaman sauran a imamai (a.s) ya zo cewa suna ummurni akan lada ta karatun kur'ani da kuma haddace shi wannan yana nuni da cewa kur'ani ba canji ko kari da ragi a cikin sa kuma shi ne hannun musulmi.

Kuma bayan zamanin na imamai wannan mahangar haka take, domin babu wani ma abaucin tunani ko kuma manyan masu fassara da suke shakka akan gaskiyar kur'ani ko kuma suka yarda da kari ko ragi ko canji a cikin kur'ani.

Duk da cewa nuskan kur'ani bugun kufi tun zamanin a imam masu tsarki yake kuma masana da ma abauta bincike sun tabbatar da dadewarsa, abun burkewa shi ne wasu bangare na wadannan kur'ane sun fito ne daga hannu a immai masu tsarki.

Daga karshe koda munyadda da cewa akwai rashin daidaituwa abangare na aya ta uku ta cikin suratul ma'ida, tabbas ba hannu marubuta a ciki kuma abun ya wuce hannu ma'aiki maitsira sai dai a danganta abun da Allah madaukaki kai tsaye.

Kuma muna iya cewa ba wani bambamci tsakanin bangare na wannan ayar da kuma wasu bangarorin na suratul ma'ida; saboda ga dukkanin wani maitunani afili yake cewa ayar tana jaddada da kuma tabbatar da rikon alkawali. Domin haka Allah madaukaki sarki baban nauyi ko kuma alkawalin da ya dorama mutane shi ne biyyaya ga imam Ali {a. s ], a wasu wuraran asanya alkawulla sun zamo tamkar hukunce hukunce na shari'a. domin kada tsawon lokaci yasa amanta da shi, saboda hake Allah madaukaki yasa ayar ikmaldin tsakanin ayoyin hukunce hukunce.

Amsa Dalla-dalla

Idan mu ka yi nazari a cikin ayar ikmaludin[1]; abu biyune zamu iya fahimta:

A: bangare na daya shi ne wulaya ta shugaban muminai aliyu bin abi talib, to in haka ne jimlar ayar na da bambamcin ma'ana da farko da kuma karshe na ayar.

B: duk da cewa bangaren da aka ambata da kuma bangaren da ya zo kafinsa da kuma wanda ya zo a bayansa na ayar akwai banbanci afili, amma da ansa lura za a iya hada alaga zakanin ayoyin.

Karin bayani akan bangaren farko:

Saboda mu isa ga amsa cikakka dole ne muyi bayani akan dalilai na banbanci da suke cikin ayar.

A 1: bangare na jimlar sama jimlace marar tasiri a cikin ma'ana wanda hukunci Allah madaukaki tun farkon saukar ayoyin suratul ma'ida yasaka ayar a tsakanin su.

A 2: bangaren da ake Magana akai wato na ayar da umurni na manzon Allah maitsira da aminci wanda yaba sahabban dake rubuta kur'ani umurni su sa wannan ayar a cikin suratul ma'ida.

A 3: ko kuma wadanda suke kiyyaya da jagoranci da kuma wasiyar imam Ali (a.s) ne suka canzama ayoyin wuri.

A tsakanin wadannan mahangar uku mahanga ta karshe ita ce tafi kusa da abunda muke so muyi Magana akai saboda hakene zamu fara da shi.

Idan a ka yadda cewa ahlisunna nada mahangar cewa wasu ne daga cikin sahabai suka canza ma ayar wuri; to wannan canjin ko da ya zamo lokacin manzon Allah ko kuma zamanin a imam (a.s) ko kuma bayan shaikaru 329 na hijira wato bayan mutuwar na'ibin imamuzaman na musamman wato Ali bin Muhammad samiri. Idan aka lura da muhimmanci wanda manzo maitsira ya baiwa kur'ani da kuma taka tsantsan da marubuta wahayi suke da shi da kuma hardacewa da wasu sahaban sukayima kur'ani don haka awannan zamani babu wanda zai iya canza wata aya ko kuma wata sura daga cikin kur'ani domin hakan zai iya kawo sabani a cikin rubutu ko kuma harda kur'ani mai kirma.

Idan kuma mukace canzama ayoyi wuri a cikin kur'ani ya farune zamanin khalifofi da kuma kokarin rufe gaskiya da sarakuna na umayya da banu abbas su ka yi, ita ma wannan mahangar ba dai dai bace.

Saboda na daya anfara rubuta kur'ani tun zamanin manzon Allah[2] kuma awannan lokacine ya bada ummarni da a aika shi kasashe daban daban na musulmin[3] wanda haka yasa musulmi suka samu ilimi na kur'ani. Saboda haka sahabban manzon Allah sunada masaniya akan tsari da kuma rubutun kur'ani, inda aka hada wadannan dalilai to za mu ga zai yi wahala a canja wa ayoyin kur'ani wuri.

Na biyu; tsawon shaikaru na hukumar adalci ta manzon Allah wadda ta kai kusan shaikara 35 ko 40 da ta dauka tana da iko na siyasa da kayan aiki wanda zata iya kyara canje canjen da akayima kur'ani; amma ba mutaba jin wata Magana makamancin haka ba. Ya zo a cikin ruwaya imam Ali (a.s) na cewa kur'anan da usman ya hada sun inganta kuma ya cigaba da cewa da nima ina kan shugabanci al'umma da aikin da usman ya yi shi ne zanyi[4] {wato hada kur'ani}, acikni jawabin da imam Ali (a.s) yake ba dalhatu yayin da ya tabbayeshi cewa kur'anan da a ka hada sune kur'anan da aka saukar na wahayi? Imam ya ce; duk lokacin da kai aiki da shi zaka tsira daga azaba wuta ka shiga aljanna; saboda shi ne hujjarmu, hakokinmu da kuma wajifcin yimana biyyaya[5].

Bayan khalifanci imam Ali (a.s) da kuma zamani a imam ba wanda ya taba jin sun yi hani akan riko da kur'ani da usma ya hada. Sai mai kwadaitar da mutane a kan karanta shi da kuma hardashi domin samun sakamako mai kyau, da kuma tabbatarma da mutane cewa babu kuskuri na tsari ko na mahanga a cikin kur'ani mai girma.

Amma wai ace canza ayoyin wulaya ya faru ne bayan gaiba ta farko da hannun wasu khalifofi shima baa bun yarda bane; saboda da farko akwai kwafi kwafi masu yawa wanda tun bayan gaiba baba suke wanda wasunsu ma ana ganin da hannun a imma masu tsarki aka rubuta su. Na biyu ba wani malamin ilimin kur'ani koda a cikin wadanda suka yarda da cewa akwai ragi a cikin kur'ani[6] amma suma kansu ba su yadda da canza tsari na ayoyi da kuma surori ba a kuma wannan zamani da muke ciki duk an hadu akan dalili na cikar kur'ani maigirma.

Yanzu kuma zamu shiga mahanga ta biyu; wato manzon Allah da kansa ya canzama ayoyin wuri, koda yake wannan mahangar ta fita daga cikin rukunin tambayarmu amma yana da kyau mu amsata.

Wasu manyan masu tafsiri na daga shi'a[7] na ganin cewa tsara kur'ani da shiryasa ya kasance a hannun manzon Allah maitsira da aminci suna cewa: duk da cewa shirya alkur'ani abarsa a hannu al'umma amma akwai dalilai masu garfi da suka sabama hakan. Na farko kur'ani mu'ujizace ta Allah madaukaki kuma mu'ujizoji dukkansu abu gudane wanda in bangare daya ya kauce to kamar dukan sune suka kauce.

Ya zo a cikin litattafai na kur'ani dake nuni da cewa daya daga cikin mu'ujizojin kur'ani maigirma[8] shi ne tsarin rubutunsa. Don haka barinsa a hannun al'umma ko hannun manzon Allah to hakan zai zama cewa ba aiki ko kuma maganar ta Allah madaukaki ba, don haka wannan mahangar ba dai dai bace, don haka barin shiryawa da tsara kur'ani a hannun manzon Allah shima ba dai dai bane. akwai dalilai da suke tabbatar da wannan mahangar ga mai bugata sai ya nema[9].

Yanzu zamu koma mahanga ta farko wadda ke nuni da cewa rashin daidaituwa dake tsakanin ayoyi na farko da na bayan ayar wani ikone da nufi na ubangiji madaukaki wanda ya shirya haka tun lokacin saukowar ayoyin saboda haka ba hannun wani dan adam ko kuma hannun manzo mai tsira a cikin lamarin.

Amma shin menene hikimar haka? Wani lamari ne wanda bai bayyanar mana ba a fili. Koda yake akwai wasu dalilai da zamu iya kawowa:

Allah madaukakin sarki kamar yadda bai bayyana al'kunya da kinaya ta imam Ali {a.s} abayyane ba a cikin kur'ani domin kada mutane suyi nisa da shi {kur'an} da wannan dalilin ne yasa wannan bangaren na ayar a tsakanin ayoyin hukunce hukunce domin kada masu hassada suyi kiyayya da kur'ani maigirma. Kamar yadda dan adam ke boye abubuwansa masu daraja a cikin wasu abubuwan domin kada a samasu ido.

Abunda aka fadi a sama da sharadin cewa mun yadda da cewa akwai rashin dai daito tsakanin ayar wulaya da wasu bangare na farkon suratul ma'ida.

B: sai dai tayiwu a samu haduwar ma'ana ta boye a tsakanin ayoyin da ake Magana a kai. Ta yadda in mutun ya yi nitso cikin fassarar ayoyin zai bayyanar masa cewa a sun a nuna muhimmanci rigo da alkawali wannan alkawalin ko tsakanin Allah da bayinsa ko kuma tsakanin mutun da mutun.

Daya daga cikin alkawali Allah akan mutane wanda riko da shi tamkar cikar addini ne da kuma cikar ni'ima; shi ne yadda da wulaya {shugabanci} na imam Ali {a.s} a matsayin wanda zai gaji manzon Allah kuma khalifan Allah a doran kasa. wannan alkawalin na da wani bangare abun lakari, domin wulaya ta shafi dukkanin nau'I na rayuwar mutun ko shi daya kansa ko kuma a cikin al'umma baki daya. saboda haka a bayyane yake alkawalin da ya fi ko wane muhimmanci shi ne nauyin da Allah ya dora akan mutane kuma ya rika nuni da shi asashe daban daban na kur'ani maigirma domin kada gushewar zamani tasa a manta da shi. Don haka a iya cewa: shi ne dalilin da yasa wannan bangare na ayar a tsakanin ayoyin hukunce hukunce.

Domin Karin bayani akan waki'ar gadir ana iya duba wadannan litattafan:

1-mustanad na ahmad bin hanbal, jildi na 1, shafi na 84, zuwa 370; jildi na 6, shafi na 401.

2-sunnan ibin maja jildi na 1, shafi na 55 zuwa 60.

3-almustadarak ala alsahihan, hakim nishaburi, jildi na 3, shafi na 118 zuwa 613.

4- algadir, allame amini, jildi 1.

Manazarta:

  1. Jarji zaidan, tarik tamadun islam, tarjama ta Ali jauharkalam.
  2. Javad Ali, almufassal fi tarik al'arab gabla isalam.
  3. Sheikh abu Abdullah zanjani, tarik alkur'an.
  4. Ahmad bin abi yakub, tarik yakubi.
  5. Ali bin asir, kamil bin asir fi tarik.
  6. Salim bin kis hallali, kitab salim bin kis.
  7. Abdurrahaman siyudi, al'itikan fi ulumulkur'an.
  8. Tarjamar Muhammad bakir musawi hamdani, almizan fi tafssiri alkur'an.
  9. Sayid abufazl mir Muhammadi, tarik wa ulumul alkur'an.

 


[1] Ma'ida 3

[2] Daya daga cikin nau'in rubutu da larabawa jahiliya ke amfani das hi kafin zuwa musulunci shine rubutun nibiti daya daga cikin kabilun arewacin hijaz da gushewar zamani aka fara rubuta kur'ani da shi, jawad ali, almufasil fi tarikhl arab gabla isalam, shafi na 153; sheikh abu abdullahi zanjani, tarihin kur'ani, shafi na 48.

[3] Tarihin yakubi, jildi na 2 shafi na 112.

[4] Ali bin alsir, kamil ibin asir fi tarikh, jildi na 3, shafi na 112.

[5] Salim bin kais halali, littafin salim bin kais, shafi na 312

[6] Abdurahaman suyuti, al'itikan fi ulumulkur'an, jildi na 1 shafi na 72.

[7] Almizan fi tafsir alkur'an tarjamar Muhammad bakir musawi hamadani.

[8] Sayid abulfadil mir muhammadi, tarihin ulumulkur'an, shafi na 197.

[9] Munahil al'irfan, jildi na 2, shafi na 309.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa