advanced Search
Dubawa
5867
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Shin zan iya samun dama game da yin wani aikin na biyu bayan wanda nake yi
SWALI
Shin zan iya samun dama game da yin wani aikin na biyu bayan wanda nake yi?
Amsa a Dunkule

Shari’a ba ta hana mutum yai koyi ko ya kware kan wata sana ‘ar ba bayan wacce yake yi ko ya iya ko yin aiki sama da yadda ya saba abin kawai da shari’a ta hana kuma take kara tsoratarwa a kansa shi ne son duniya da nace mata, da nisantar ayyukan alherai da ke gina lahira da mantawa da lahira da kuma gafala daga gare ta, a hakikanin lamurra wannan shi ne ma’auni har ma wajan kwarewarsa kan dukkan ayyukan da yake yi (sana’ar) har ma zuwa ribar da ya kamata mutum ya samu,  zaka samu wasu daga mutane sun kware kan sanao’i daban daban suna samun riba mai yawa, duk da haka wannan ba ya hana su tunawa da lahira tare da muhimmantar da nata ayyukan da kan gina ta ba kuma zaka ga sun kwallafa rai ga duniya ba.  A nan abin magana shi ne, ya zama wajibin da ba mustahabbi ba ma a kan duk mutum ya yi aiki na biyu idan har aiki na dayan ba zai ishe su gudanar da rayuwa ba da a ce ya bar su suna rayuwa cikin wahala da kunci.

E (haka ne) aiki sama da ka’ida na nufin saba wa doka, domin haka idan aiki na biyun zai haifar masa saba wa doka tare da rashin yin na farkon yadda ya kamata kuma da rashin cika aikinsa, a nan yin aiki na biyun akwai matsala. Haka nan kuma idan aiki na biyun zai cinye masa gaba dayan lokutansa da zai ba wa iyalinsa tarbiyya tare da rashin kula duk abin da ya same su wanda shi ne abin da ya hau kansa mai girma.. wanda kulawa da iyalin nasa ya fi masa zama muhimmi a kan zuwa aiki na biyun ka ga aiki na biyun ya haifar masa da hadarin gaske, wanda ya kamata mutum ya dinga auna abin da zai amfani lahirarsu da duniyar su a lokaci guda tare da lissafa abu kafin farawa; ruwaya tazo daga IMAM HASSAN DAN ALIYU DAN ABI DALIB (a.s) cewa; na tambayi babana game da tsarin wajan manzo (s.a.w) sai ya ce da ni ba a shiga wajansa sai da izini, sannan kuma yana raba lokacinsa zuwa gida uku, daya na ganawa da Allah (s.w.t), daya na iyalinsa, dayan kuma nasa a kan kansa (s.a.w).

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Me ake nufi da hukunci da fatawa? Me ye bambancinsu?
    9569 بیشتر بدانیم 2012/07/24
    Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin. Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana ...
  • Yaya za a azabtar da mutanen da suka kirkiro wani abu mai amfani ga dan'adam alhalin ga hidimar da suka yi?
    9657 Sabon Kalam 2012/07/24
    Zamu iya kasa mutanen da suka riki musulunci zuwa jama'a gida biyu ne: 1- Jama'ar da ake kira jahili mai takaitawa ko kafiri mai takaitawa, ana nufin su ne wadanda kalmar gaskiya da sakon gasiya na sama na adinin musulunci ya je musu, suka san ...
  • Shin akwai ingancin ruwayoyin nan da suka nuna Imam Husaini (a.s) ya na da wani matsayi da makami da darajoji? Shin wannan darajar suma sauran Imamai ma\'asumai (a.s) suna da ita?
    3521 تاريخ بزرگان 2017/05/21
    Lallai babu shakka Imam Husaini (a.s) yana da wasu baye-baye na masamman. Kamar kasantuwarsa baban Imamai (a.s) wadanda dukkansu sun biyo ta tsatsonsa ne (a.s). Ana samu waraka ta hanyar Turbarsa, da karbuwar Addu'a a Hubbarensa mai daraja. Amma duk da wannan karamomi da kebantattun darajoji, ba ...
  • mi a ke nufi da zayuwar a barzahu kwana daya ko kuma kwana goma?
    10442 برزخ 2012/11/21
    Wannan ayar na nuni da halin da mujurumai suka samu kan su bayan an busa kahon tashin kiyama suna tambayar junan su kwana nawa mu ka yi a duniyar barzahu? Mujurumai sana tunani a duniyar barzahu kwana daya ko kuma kwana goma su ka yi sai wasu ...
  • saboda me ya wajaba a yi takalidi?
    6632 بیشتر بدانیم 2012/07/26
    Halaccin takalidi na daga cikin lamuran da ke wajabta wa mai yin takalidi ya yi iya kokarinsa a cikin lamarin kuma lalle fatawar mujtahidi ba ta isar wa mai yin takalidi, saboda haka wannan mas’alar na daga cikin mas’ala mafi girman mihimmanci. Sananne ne cewa ...
  • Shin wace hanya ko salo zan bi wurin yin wa’azin addini?
    12582 تبلیغ و گفتگو 2012/08/15
    Wa’azi yana nufin isar da sakon Allah (s.w.t) zuwa ga jama’a. Kasantuwar sakonin Annabawa a dunkule abu guda ne, sannan sakon Fiyayyan Annabi (s.a.w) na masamman ne, da ya zo da nufin shiryar da bil Adama don fitar da shi daga duffai zuwa ga haske. A bisa haka ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    12766 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14041 کیفیت زندگی امام غایب 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • me ye sharuddan jagorancin malami?
    6496 شرائط و خصوصیات ولی فقیه 2012/07/24
    Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka: Sharudda da siffofin jagora: 1- siffantuwa ...
  • Mene ne dangantakar da take tsakanin jibintar malami da kuma komawa zuwa gare shi?
    11546 ولایت فقیه و مرجعیت 2012/07/26
    Ma’anar marja’iyya a mahanga ta shi’anci Abu ne biyu da a ka cakuda su suka ba da ma’an bai daya wato sha’anonin (Bada fatawa) da (jibintar malamin ko shugabancinsa), Hakika malaman addini masu girma sun tsaya kyam a fagen yin bayani da shiryarwa ta hanyar bayyana hukunce-hukuncen ...

Mafi Dubawa