Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka: Sharudda da siffofin jagora: 1- siffantuwa ...
Idan muka koma wa tarihi da littattafansa zamu ga cewa Abubakar dan Ali dan Laila ‘yar Mas’ud assakafi, da Umar dan Ali dan Ummu habib, da Usman dan Ali dan ummul Banin (s), dukkansu ‘ya’yan Imam Ali (a.s) ne, kuma bayan mun duba sanadin ambatonsu da wadannan ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Hadisin Kisa’ ya zo a littafin Sahih Muslim, amma da dan wani bambanci da yadda ya zo a littattafan Shi”a, a littafin Muslim ya zo ne kamar haka: حَدَّثَنَا أَبُو بَکرِ بْنُ أَبِی شَیبَةَ، وَ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللهِ بْنِ نُمَیرٍ – وَ اللَّفْظُ لِأَبِی بَکرٍ - ...
Allah baya amfana da ibadar wani daga cikin bayinsa da komai, ba tare da banbancin cewa bawan ya yi ta ne bisa son ransa ko kuwa.Sai dai yin ibada bisa zabi na da amfani wajen kara samun kamala da daukaka da shiryuwa a sannu ...
Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya ...
"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun ...
An samu sabanin ra’ayoyi tsakanin malamai maraji’ai game da limancin mace ga mata a sallar jam’I da zamu kawo bayanin kamar haka: 1. Mafi yawan marja’ai sun tafi a kan cewa bisa ihtiyadi wajibi ne limancin mace ga ‘yan’uwanta mata ba ya inganta
Ka iya samun wani mutum yana kokarin cin mutuncin wani da yake adawa da shi ko ta hanyar bata masa rai da tsawa da tada hankali. To shi Musulunci yana ba da damar ramuwa, watau “ramuwar gayya”. Sai dai a garin ramuwar bai dace a ci mutunci ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...