advanced Search
Dubawa
5412
Ranar Isar da Sako: 2013/07/20
Takaitacciyar Tambaya
A ina ne za a iya yin salla da taimama maimakon wankan janaba?
SWALI
Saurayina da aka yi mana baiko yana yin wasa da ni wani lokaci da dare amma ba tare da ya shiga ciki ba... sai dai ba zai iya yin wanka don sallar asuba ba.! Shin zai iya taimama maimakon wankan janaba?.
Amsa a Dunkule
Idan dai mani ya fita daga gare shi ya samu janaba, to wanka ya zama wajibi kansa. Sai dai a wurare guda bakwai ne zai iya yin taimama maimakon wanka da suka hada da[1]:
 1. Idan ya zama ba shi da ruwa.
 2. Idan babu isasshen lokacin yin wanka ta yadda idan ya tsaya yin wanka to salla zata zama ramuwa.
 3. Idan ruwa zai cutar da shi ko kuma zai kara masa tsayin rashin lafiyarsa.
A nan zai iya yin taimama maimakon wanka. Amma idan saboda kunya ne ba zai iya yin wanka ba to ba zai iya yin taimama ba  a farkon lokaci don ya yi salla! Ya zama dole ne ya zuba ruwa a bangaren da ya zama najasa a jikinsa) kuma sai ya yi hakuri har zuwa karshen lokaci ta yadda zai iya yin taimama ya yi salla (da zai iya isar sa har ya yi salla ba tare da ta zama ramuwa ba), sai ya yi taimama ya yi salla yayin nan. Kuma jinkirta salla da kawar da damar yin wanka daga kansa da ya yi yana da zunubi don mu sani, ya yi sabo ke nan, sai dai duk da haka amma sallarsa ta yi[2].
 

[1] Taudhihul masa'il: hashiyar Imam khomain, j 2, sh 365.
[2] Taudhihul masa'il: hashiyar Imam khomain, j 1, sh 377, mas'ala: 679.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • menene hakikanin ma’anar salla?
  22913 Halayen Aiki 2012/07/25
  Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
 • Shin shedan na da zuriya, kuma shin su ma la'anannu ne?
  4604 ابلیس و شیطان 2012/07/24
  Hakika shedan na da zuriya kuma su ma la'anannu ne kamar yadda yake la'ananne, domin su ma bisa hakika sun bi tafarkin sa kuma sun yi riko da hanyarsa da salonsa wajen batarwa da kokarin kautarwa daga tafarkin gaskiya, sun dogara da wannan hanyar a wajen batar ...
 • shin ahalissunna sun canzama ayoyin gadir da zuka zo a cikin kur'ani wuri?
  9302 غدیر خم 2012/11/21
  Mafiya yawa na masu fassarar kur'ani daga bangaren sunna da shi'a, sun tafi akan cewa; اليوم يئس الذين jimlace wadda tazo tsakanin aya ta ukku ta suratul ma'ida dan haka acin ilimin nahawu bata da muhalli na li'irabi. Kuma mafiwa yawancin su suna ganin wannan ta'aruz ...
 • shin ya inganta mutum ya karanta littatafan wasu malamai irinsu Dr. Ali shari’ati (a.j)?
  5726 تاريخ بزرگان 2012/07/25
  Akwai ra’ayoyi mabanbanta masu sabani da juna dangane da karanta littatafan Dr. Ali Shari’ati. Akwai masu wuce gona da iri, akwai masu tauye shi. Sai dai daidaitaccen ra’ayi kan batun shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Wannan shi ne ra’ayi madaidaici kuma mafi adalci a wannan ...
 • mene ne ma’anar Takawa?
  8150 تقوی 2012/07/25
  Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
 • Yaya asalin mutum yake?
  10343 خلقت انسان 2012/07/25
  Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
 • menen hukuncin kallon fim din biki mai tada hankali da sa sha’awa.
  579 2018/11/04
  Kallon wannan fim din laifi ne kuma ya haramta, kuma lalle ne ki nisanci sake kallon sa, amma dangane da kallon farko wanda ba ki san me ya ke cikinsa ba shi ma kin yi laifi tun da tun a farko ya kamata ki gasgata babarki da ...
 • Mene ne mafi muhimmancin abu a tarihin rayuwar annabi Ibrahim (a.s) bisa dogaro da ayoyi da ruwayoyi?
  1424 تاريخ بزرگان 2019/06/12
  Za a iya karkasa rayuwar Annbi Annabi Ibrahim (a.s) zuwa mtakai uku; kamar haka: 1. Matakin kafin annabta 2. Matakin annabta da fafatawa da bautar gumaka da tunkararsu 3. Matakin hijira daga Babila da kai-kawon fafutuka a Masar da Falasdinu da kuma Makka 1. Haifuwar Annabi Ibrahim ...
 • Tarihin Adam (as)
  443 2019/06/16
  Amsa Filla-Filla: bayani kan rayuwar wasu nau”in mutane da aka fara halitta a bayan kasa, da kuma sanin shekara nawa kenan da halittar su zuwa wannan zamani da muke ciki? To hakika babu wata aya da ta yi bayanin hakan cikin kur”ani. Allama daba”ba”i cikin tafsirinsa na ...
 • Me nene hakikanin zunubi? Menene hakika tasirin sa ga ruhin mutum da ransa? Kuma yaya zamu kubuta daga wadannan guraban?
  14976 گناه 2012/09/16
  Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...

Mafi Dubawa