samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
Addinin muslunci na ganin tsarin tausayi da jin kai da tausasawa ita ce hanyar da ta fi tasiri fiye da ragowar hanyoyi, duk da cewa a wasu wurare ya zama tilas idan yaro aikata wani nau'in kuskure a ladabtar da shi ta hanyar dukansa a sakamakon aikin ...
Zuwa yanzu malaman addini suna da masaniya mai yawa da aka tattara ta game da ilimin musulunci wanda yake kunshe da dokoki da ka'idoji. Akwai tafarkin ganin abubuwa ta mahanga tsukakkiya da kuma ta hankali, wannan lamari ne ya sanya aka rasa wata makama mai fadi game ...
A bisa ayoyin kuráni mai girma ibilis yana daya daga cikin aljanu, saboda yawan ibadar shi ya zamo daga cikin mala'iku, amma bayan Allah ya halicci Adam sai aka umarce shi da yi wa Adam sujada amma ya ki sai Allah ya nisantar dashi daga gare shi. ...
Ya Dan’uwa mai girma muna masu baka hakuri sakamakon jinkirin da aka samu wajen aiko maka da amsar tambayarka/ki a sakamakon yanayin ayyuka da suka sha kanmu. “Ammar Dan Yasir Dan Aamir” ana yi masa alkunya da ‘Abu YaKazan” kuma ya kasance abokin rantsuwa ne shi (wato ...
Kanbun baka na da tasiri a ruhin mutun wanda babu wani dalili da za a iya kore samuwar sa da shi, ballantana ma an ga faruwar abubuwa masu yawa da suka tabbatar da samuwar kanbun baka ko maita. Marigayi shekh Abbas Kummi ya yi wasici da a ...
Bai’a na da bangarori biyu, mai bai’a (sauran mutane) da wanda ake yi wa bai’ar (wato su ne manzo (s.a.w) da imamai (a.s)). Tare da cewar manzo (s.a.w) shi ne hujja kuma shugaba, don haka shi za a yiw mubayi’a a matakin farko wato shi ne farkon ...
Idan muka yi duba a nutse, a kan irin lokutan da wadancan Imamai guda biyu (a.s) suka yi rayuwar su, za a fahimci dalilin da zai sa zai yi wuya a samu daman rubuta hadisansu cikin wani littafi na musamman. Amma dai wannan baya nufin cewa al’amarin ...
Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya ...
Bama musun yiyuwar wannan ruwaya kai tsaye sai dai wannan ruwaya ba a cika samunta ba sai a litattafan da suka yi nisan zango da zamanin amirul muminin (a.s) nisanda mafi karanci shi ne shekara dubu, marubucin <Auwal musha sheen> na daga marubutan karshe ya ciro wannan ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...