Nufin Allah da iradar sa na da tsari da kaidoji (ko dokoki), kuma ayyukan sa ba mara sa ma’ana da manufa ba ne, ballantana ma bisa tsarin na hikima da ilimi da tausayi yake zaratar da komai. Don haka ne ma yake zabar wasu daidaiku daga ma’abota ...
Ba shakka cewa Kur’ani ya bayyana a Fili cewa Annabi Isa (a.s) an ba shi Matsayi mai Girma Alhali ma yana cikin Tsumman Goyo: ’sai Ta yi nuni a gare shi sai sukace ta yaya zamu yi Magana da wanda yake cikin Tsumma, sai ya ce ni ...
Bisa la'akari da tambayoyin da suka gabata amsa ta farko da ta biyu zasu kasance kamar haka ne: a- Ba a yi bayani karara ba kan batun rashin shigar malami jagora a cikin doka ba. Don haka idan irin wannan ne jagora malami zai iya ...
Addinin muslunci na ganin tsarin tausayi da jin kai da tausasawa ita ce hanyar da ta fi tasiri fiye da ragowar hanyoyi, duk da cewa a wasu wurare ya zama tilas idan yaro aikata wani nau'in kuskure a ladabtar da shi ta hanyar dukansa a sakamakon aikin ...
Musulunci bai bar kowanne vangare daga cikin vangarorin rayuwa kara zube ba saboda kasancewarsa gamammen addini ga dukkan duniya, matuqar wannan vangaren zai taimaka ma xan Adam a yunkurinsa na samun kamalar da zata masa jagora zuwa ga rabautar duniya da lahira. Kamar yanda ya ...
Gwamuwar jin tsoron Allah da kaunarsa, a wasu lokutan kuma kaunarsa kawai, dangane da Allah ba wani al’amari ba ne da yake bako, domin shi ya cika dukkanin bangarorin rayuwarmu, amma saboda tsananin bayyanarsa sai mu din muka rafkana da shi. Mu sani cewa har ...
Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya ...
Bahasi kan alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) yana daga bahasosi masu zurfi da wuya ta wata fuska wacce tana bukatar karanta dukkan ruwayoyin da suka zo game da haka, sai dai abin da aka fahimta daga ruwayoyi –ko da kuwa a dunkule ne- shi ne kasa wadannan ...
"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin. Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...