Ya kai dan’uwa mai girma; Muna baka hakuri saboda jinkirin da aka samu wajen bada amsar tambayarka a sakamakon wasu larurori na aiki:- Shi ne jundubu dan janadata ko kuma a ce Abuzarril giffari yana daga cikin manyan sahabban manzo tun a farkon manzanci ya kasance ...
A kan sami ra’ayoyi guda biyu a kan maganar auren ‘ya’yan Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi). A wannan zamanin ba a sanya dokar haramcin dan’uwa ya auri ’yar’uwarsa ba, kuma ba wata hanyar kiyaye tsatso na mutane domin idan ba ta wannan ...
Ba shakka cewa Kur’ani ya bayyana a Fili cewa Annabi Isa (a.s) an ba shi Matsayi mai Girma Alhali ma yana cikin Tsumman Goyo: ’sai Ta yi nuni a gare shi sai sukace ta yaya zamu yi Magana da wanda yake cikin Tsumma, sai ya ce ni ...
Wasu suna kokarin cewa akwai fahimtoci da yawa wajen malaman musulunci game da hukumar musulunci, har ma suna kokarin gina tunanin da ke tabbatar da ‘mahangar tabbatar da shugabancin fakihi (malami), daya daga cikin fahimtoci masu yawa a cikin wannan maudu’I ta tafi a kan cewa lalle ...
A wajen malaman lugga: T R J M, wadannan nan ne bakaken da suka hada Kalmar tarjama, wato jam’in (tarjiman) shi ne wanda yake yin tarjama, yake fassara magana, ana cewa wane ya tarjama maganar wani: ma’ana ya bayyana shi ya fayyace shi, haka ma, wane ya ...
Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana ...
Game da bada amsar tambayar tilas mu lura da abubuwa biyu: Nafarko: Taimako na Ubangiji yana da sharuda na musamman. Idan sharudan basu kamalla ba to taikakon ba zai samu ba. Misali sharudan sun kammalu a yakin Badar sai tallafin Allah da taimakon Ubangiji suka samu ga ...
Sallar firgici, ko sallar Daren Binnewa, salla ce da ake yin ta ga mamaci a farkon lokacin da aka binne shi, don haka ne ma ake kiran ta da salar firgici, domin yayin da mutum yake barin wannan duniayr bai saba da waccan duniyar sabuwa ba, kuma ...
A cikin wasu daga cikin jigon litattafan Ahlussunna akwai wasu ruwayoyi kan wannan lamari wadanda suka doru kan wasu dalilan da ba za su zama karbabbu ba: An rawaito Manzon Allah (s.a.w) “Ya Allah! duk wani musulmi da na zaga to ka sanya zagin da ...
{uwaimar dan malik} wanda ya shahara da alkunyar abuddarda”dan asalin kabilar khazraj yana daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w). yana daya daga cikin mutanen khazjar da suke rayuwa a madina ya shiga musulunci bayan zuwan manzon Allah (s.a.w) madina da wasu yan watanni. Abuddarda”yana fifita imam Ali (a.s) a ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...