Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka: Sharudda da siffofin jagora: 1- siffantuwa ...
Halaccin takalidi na daga cikin lamuran da ke wajabta wa mai yin takalidi ya yi iya kokarinsa a cikin lamarin kuma lalle fatawar mujtahidi ba ta isar wa mai yin takalidi, saboda haka wannan mas’alar na daga cikin mas’ala mafi girman mihimmanci. Sananne ne cewa ...
Musulunci ya zo ne domin ya kafa dokoki da alakar dan adamtaka. Madinar Manzon Allah (s.a.a.w) ta kasance samfuri na al’umma mai bin dokoki, ta yanda ta tsara dukkanin alakar dan Adam karkashin inuwar dokoki. A mahangar Shahid Sadar (r.a) yana cewa, musulunci ya ajiye ...
Ba zai yiwu ba ilimin da hankalin Dan Adam su riski wasu tabbatattun abubuwa ba, hassada ma na cikin waDancan abubuwan da hankali da ilimi basa iya tabbatarwa alal aKalla, hakama kuma hankali da ilimi basu samu dalilin kare hakan da watsi da shi ba. Idan muka ...
Shari’a ba ta hana mutum yai koyi ko ya kware kan wata sana‘ar ba bayan wacce yake yi ko ya iya ko yin aiki sama da yadda ya saba abin kawai da shari’a ta hana kuma take kara tsoratarwa a kansa shi ne son duniya da nace ...
A auren dole idan bayan an yi auren (ko da kuwa gwargwadon sakan ne) sai matar ta ji cewa ta yarda da auren to ya inganta, amma a ko wane hali Dan da ta ambata ba zai zama ba na shar’a ba, domin samun Karin bayani a ...
Musulunci yana da kalmomi da suka hada da "kasa" da kuma "yanki" da "al'umma. Kasa a tunanin fikirar musulunci wuri ne guda daya, kuma dukkan iyakokin da ake da su ba su da wani tasiri wurin rusa kasancewar kasar musulunci da musulmi abu guda ne. kuma wannan ...
Tarin ayoyi na Kur’ani da Attaura da kuma bayanan tarihi a kan yajuj na nuni da cewa wannan a’umar ta rayu ne a yankin arewacin asiya sai dai sun ta kai ma yankin kudu da yamma hare hare masu tsanani. Amma lokacin da Zulkarnaini ya yi bango ...
Ra’ayoyin wasu malamai daga muraji’an taklidi a kan mas’alar kawar da wannan ta hanya hasken wuta (radiation) su ne kamar; AYATULLAHI SYSTANY (MZ) Idan cikin ba zai haifar da kallo ko shafa ta haramci ba kuma babu cutarwar da zata ...
Bayani kan menene (hulul) shiga jiki da ittihadi (hadewa) hulul a harshen larabci ya samo asali daga kalmar halla da ma’anar sauka[1] amma Kalmar ittihad ita kuma tana da ma’anar abubuwa biyu su hade su zama abu guda daya[2] Kashe kashen ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...