Abin da ake nufi da Kalmar ”Rawukan da suka sauka a Farfajiyarka” su ne Shahidai, wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai (A.s) a Filin Karbala. Wadannan su ne Dalilan da suke Tabbatar da haka; A bisa Al’ada masu Ziyara wadanda ...
Wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin ba wata hujja ta al’ada da ta hankali da ta hana ‘ya’yan kani su girmi ‘ya’yan wa, mussam idan ya zamana tazara tsakanin yan’uwa biyun ba mai yawa ba ce kamar yadda ya kasnce tsakanin Hasan da Husain (a.s). ...
Musulunci shi ne addinin karshe kuma mafi kamala, don haka ne a kowane fage na rayuwar mutum ko ta daidaiku ko ta jama'a muke ganin samun shiryarwa a dukkan wadannan fagage. A cikin tunanin fikirar musulunci akwai mahanga mai isarwa matsakaiciya game da gamewar addinin musulunci. ...
Abin da ake nufi da ruwaya ta farko shi ne duk da kasantuwar masallatai su ne fiyayyun wurare na tsai da salla kuma salla a cikinsu yana da lada mai yawa. Sai dai fiyayyen masallaci ga mata shi ne dakunansu. Saboda yin hakan zai hanasu cakuduwa da ...
An samu ruwaya game da kallon mace wacce ba musulma ba ga mace musulma daga imam Sadik (a.s) yana cewa: Bai kamata ba ga mace musulma ta yaye lullubinta a gaban mace bayahudiya ko kirista, domin su suna ba wa mazajensa bayanin siffofin jikinta
An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
Ya zo a cikin muhimman litattafan fiqihu {hukunci} cewa mustahabbi ne a cikin tashahud na biyu karanta wannan zikiri kamar haka: {Bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairul asma' lilLah, ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharikalah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil-haq bashiran wa ...
Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin ...
Hujr bin Adi Al-kindi; ya na cikin sahabban manzon rahama {s.a.w} sannan bayan wafati ya kasance cikin kebantattun sahabban imam Ali (as) mai cika alkawali, hakika hujr bin adi ya halarci yakokin da imam Ali {as} ya jagoranta bayan wafatin manzon rahama ya kuma taimakawa imam da ...
AYATULLAHI KHAMNA’IY (MZ) Idan tsaretan shi ma zai cutar da ita bai halatta ba MUKARIMUSH SHYRAZY (MZ) Idan babu makawa sai an tsare ta babu laifi MAHDY HADAWY (MZ) Idan za’a ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...