advanced Search
Dubawa
1270
Ranar Isar da Sako: 2015/05/18
Takaitacciyar Tambaya
A wane lokaci ne aka hada surorin Kur\'ani da ayoyinsa aka rubuta su suka zama kamar yadda suke a yau?
SWALI
Yana daga cikin tambayar da babu wanda yake musun cewa tun lokacin da ake saukar wa Manzon Allah (s.a.w) wahayi ake rubuta Kur\'ani, da wasu mutane da ake kiran su marubutan wahayi. Sai dai tambayar a nan ita ce a wane lokaci ne aka hada surorin Kur\'ani da ayoyinsa suka zama a waje daya kamar yadda yake yanzu a hannun mutane a koina? Wadannan hadaddun surorin da ake kiran su da Kur\'ani a yau?
Amsa a Dunkule
Dangane da hada Kur’ani akwai ra’ayoyi guda uku kamar haka:
1. Masu ra’ayi na farko suna ganin an hada Kur’ani ne tun lokacin Annabi tsara (s.a.w) yana raye ta hanayr kulawarsa da kariyarsa a karkashin shiryarwar Ubangiji. Tare da cewa Manzon Allah (s.a.w)  ba shi ya rubuta da hannunsa ba, kuma ba shi ya tattaro ayoyinsa ba.[1]
2. Masu ra’ayi na biyu kuma suna ganin cewa an hada Alkura’ni ne kuma an shirya shi ne bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w)  ta fuskacin Imam Aliyu amincin Allah su kara tabbata a gare shi a lokacin da Imam Aliyu amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasance a zaune a gidansa.[2]
3. Masu ra’ayi na uku kuma su suna gnain cewa, an tattara Kur’ani ne bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w)  ta hanyar sahabbai, amma ba tare da Imam Aliyu (a.s) ba.[3]
Da yawa daga cikin malaman Shi’a musamman ma na daga baya-ba yasuna ganin cewa an hada Kur’ani ne a zamanin Manzon Allah (s.a.w)  a karkashin kulawarsa da nuninsa.[4]
Wasu kuma daga cikin ‘yan shi’a suna tafiya a kan ra’ayin magana ta biyu na ganin cewa Imam Aliyu amincin Allah su kara tabbata a gare shi shi ne da kansa ya gudanar da wannann aikin kuma ya tsaya ya shirya shi.[5]
Amma da yawa daga cikin malaman ahalus sunna sun tafi ne a kan ra’ayi na uku, a kan haka ne mustasharakun su ma suka yi riko da wannann ra’ayin. Saboda haka ne ma suke cewa Kur’ani n da Imam Aliyu amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya hada bai zama wurin da sahabbai suke dogara ba.
Abin da  ya bayyana daga ra’ayi na daya da na biyu shi ne hada Kur’ani duka ya faru ne daga umarnin Allah Madaukakin Sarki, haka kuma shirya shi da kuma jera surorinsa ya zo ne ta hanyar wahayi, saboda abin da Manzon Allah (s.a.w)   ya yi managa a kan sa ne.
Saboda duk abin da Manzon Allah (s.a.w)  ya yi umarni da shi ta fuskacin al’amuran addini ko abin da ya shafe shi, to daga wajen Allah ne kamar yadda wannann ayar mai girma take gaya mana: {Wa ma yandiku anil hawa in huwa illa wahayun yuha} (bay a yin furici bias son rai face sai wayahin da aka saukar a gare shi).[6]
Haka su ma Imaman Ahlul Baiti amincin Allah su kara tabbata a gare shi suke ma’asumai duk da cewa su ba Annabawa ba ne, amma ci gaban annabta ce kuma su ne suke ci gaba da kare sakon Ubangiji kuma su ne suka fi kowa ilimin addini.
Amma ma’abota ra’ayi na uku sun kasa tabbatar da cewa shirya Kur’ani da jera surorinsa daga Allah ne, domin a karshen lamari suna kore hakan, kamar yadda suke ganin zaukin sahabai da kusancinsu, suna da ta cewa a wannann lamarin.
A nan muna ganin cewa lallai ya kamata mu yi nuni da wadansu ‘yan maganganu kamar haka:
(1)        Allama Tabataba’i yana cewa game da tafsirin ayar nan mai girma: {Inna nahanu nazzalnaz zikra wa inna lahu lahafizin}. (lalle mu ne muka saukar da wannan ambaton (tunatarwa)  kuma mu ne za mu kiyaye shi.[7] Lallai wannann matsayin da Kur’ani ya kebanta da shi na magana da balaga da fasaha da rashin samun sabani da kuma yarda ya gajiyar da mutane ta wajen zuwa da kwatankwacinsa gaba daya. Wannann Kur’ani da yake kewayawa a hannun Musulmi a yanya tattaro duka wadannan abubuwan.[8]
Tunda yake haka ne kuwa to wannann Kur’ani da ya a hannun Musulmi a yau shi ne ainihin Kur’ani n da  yake a zamanin Manzon Allah (s.a.w) .
Duk da cewa wadannan maganganun suna nuna ba shin jirkita Kur’ani to ba shi ne kuma yake tabbatar da cewa wadannan surorin da aka jera su kuma aka tsara su haka suka zo daga wajen Allah ba. Kamar yadda ha kanba shi ne yake tabbatar da cewa yadda ayoyin nan suke a yanzu haka ma suke a zamanin Manzon Allah (s.a.w)  ba.
2- Idan zai yiwu wani mutum ya raba wadansu adadi na mu’ujizar irin mu’ujizar da muka ambata dangane da Kur’ani mai girma, saboda haka mu’ujizar ta musamman wacce ta zo daga daidaikun kalmomi ko kuma jimloli na Kur’ani dangane da shiga cikin sura ko kuma jerawar ta da wata, ma’ana samun alaka tsakanin da wata. Musamman tsakanin aya da sura ko kuma sura a kan kanta, ta yadda maganar ta zo ne daga wani mutum. To zai yiwu a tababtar da dacewa wannann jimlar da aka shigar cikin sura ba daga wahayi take ba.
Sai dai ko yaushe mu ce yadda aka jera duk ayoyin nan a cikin sura daya haka yake daga wajen Allah abu ne da ba zai yiwu ba.[9]
Don Dubawa:
Hadawi Attehrani, Mahdi, Al-Ususul Kalamiyya Lil Ijtihadi.
 

[1] A Duba Sayyid Abdul-Wahab Addakani Ulumul Kur’ani shafi. 83.
[2] A duba Sayyad Muhammad Rida Al-Jalali Na’iyani Tarihi Ijam’ul Kur’anil Karim shafi 87.
[3] A duba Sayyid Abdul-Wahabu Dakani Ulumul Kur’ani shafi. 83 Sayyad Aliyu Milani Attahakik fi nafayil tahrif an kur’ani sharif sh. 42 – 41 da sha. 46. Muhammad Hadi Ma’arafi siyanatul kur’ani minal taharifi sh. 34.
[4] Haza ra’ayi Tubanahu Akasariyatu min ahlul sunna masdar sabki shafi 51 – 19.
[5] A duba Sayyad Muhammad Rida al-Jalali Naiyani tarihi jum’ul kur’ani karim sh. 80.
[6]  Inna nahnu nazzalnaz zikra wa inna lahu lahafizin. 9.  …
[7] Wama yandiku anil hawa in huwa illa wahayun yuha.
[8] A duba allama tabataba’i almizan j. 2. sh. 104 da sh. 106 da 138.
[9] Hadawi dahirani mahdi al ususul kalamiya lil ijtihad sh. 55 – 54 mu’assasatul sikafiya baitul ukulkumdaba’atul ula 1377.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka Daular Safawiyawa, kana mai yaba wa mahukuntanta?
  4000 شخصیت های شیعی
  Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da ...
 • Me ake nufi da hukunci da fatawa? Me ye bambancinsu?
  5964 بیشتر بدانیم
  Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin. Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana ...
 • Mene ne ma'anar jagorancin malami?
  6477 کلیات
  Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci. "Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu: 1- Wuraren da wanda ...
 • Ruwayar “Allah yana aiko wa wannan al’umma wanda zai jaddada mata addininta duk shekaru dari” tana da sanadi ingantace ko kuwa?
  5340 Dirayar Hadisi
  Wannan hadisin babu shi a cikin littattafan Shi'a, sai dai cewa wsu daga malamai sun yi nuni da shi. Wannan hadisin an same shi a littattafan ahlussunna ne kawai a littafin sunan Abu Dawud (wanda yake daga manyan littattafan hadisin Sunna) kuma bisa zahiri wasu sun nakalto ...
 • Shin mutum zai iya dawwama; idan haka ne, don me ya sa bai dawwama ba a duniya?
  6803 Sabon Kalam
  Yana daga abin da yake jan hankli mai kyau a cikin kur’ani mai girma cewa yana ganin mutum wani halitta ne na sama madaukaki mai ‘yanci, kuma wannan jikin nasa ba komai ba ne sai wata sheka ta dan wani lokaci da ruhinsa ya fake a ciki ...
 • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
  4038 انسان شناسی
  Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...
 • Mene ne hukuncin wasa da tsintsaye a musulunci?
  5474 نگهداری و شکار حیوانات
  Shi wasan a kan kansa ba haramun ba ne, sai dai idan yakan cutar da mutanen da ke kusa ko na nesa kamar makoci yakan samu hukunci daban kamar yadda malamai masana tunanin dan Adam suka fada cewa ya kamata gare shi ya kula sosai da irin ...
 • Wane addini ne Cikamakon Addinai?
  3895 Sabon Kalam
  Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo. Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda ...
 • me ye sharuddan jagorancin malami?
  4000 شرائط و خصوصیات ولی فقیه
  Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka: Sharudda da siffofin jagora: 1- siffantuwa ...
 • Shin zai yiyu a sami alaKa tsakanin Mutum da Aljani?.
  6335 ارتباط انسان با جهان
  Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...

Mafi Dubawa