advanced Search
Dubawa
5233
Ranar Isar da Sako: 2012/06/20
Takaitacciyar Tambaya
Me ake nufi da hukunci da fatawa? Me ye bambancinsu?
SWALI
Me ake nufi da hukunci da fatawa? Me ye bambancinsu?
Amsa a Dunkule

Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin.

Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana daga dokokin shari’a da tsarin musulunci da lura da zurfafa tunani tare da la’akari da sharudda game da wata mas’ala ta musamman domin ayyana matsayin al’umma ko wasu kungiyoyi, ko wasu jama’a daban.

A mahangar shari’a biyayya ga hukuncin ubangiji da fatawar malami wanda ya cika sharudda, kamar biyayya ga jagora mai jibintar lamarin musulmi wani abu ne na tilas. Sai dai akwai cewa fatawar malami ga malami ko mai koyi da shi wata aba ce da ta zama tilas su bi ta, yayin da game da hukunci ya zama dole ne ga kowa ya yi biyayya ga malami jagoran hukuma.

Amsa Dalla-dalla

Yayin da mujtahidi yake komawa zuwa ga madogarar shari’a (littattafan shari’a) domin tsamo hukuncin shari’a na ubangiji kan wata mas’ala ta hanyar amfani da hanyoyin da suke na musamman domin wannan aikin na fitar da hukuncin shari’a, bayan ya fitar da hukuncin sai ya sanya shi hannun masu koyi da shi, to wannan muna kiran shi da sunan “Fatawa”. Don haka ne zamu iya cewa: Fatawa ita ce fitar da hukuncin shari’a a wannan addini ta hanyar koma wa madogara wannan addinin ta hanyar amfani da wasu hanyoyin yin hakan na musamman[1].

A lokacin jagoran musulmi ya fitar da doka kan wata mas’ala  kan al’umma, ko wasu kungiyoyi, ko wasu jama’a, yana mai la’akari da dokokin shari’a da tsarin musulunci, da duba mai zurfi da kula da sharudda yanayin wannan mas’ala, to sai mu kira wannan da hukunci. Don haka zamu ga a hukunci ana la’akari da dokoki da al’adun da tunanin duniyar musulmi bisa yanayi da sharudda na musamma, kuma matukar wannan yanayin bai canja ba to wannan yana nan yadda yake gun jagora ko mataimakinsa.

A mahangar shari’a biyayya ga hukuncin ubangiji da fatawar malami wanda ya cika sharudda, kamar biyayya ga jagora mai jibintar lamarin musulmi wani abu ne na tilas. Sai dai akwai cewa fatawar malami ga malami ko mai koyi da shi wata aba ce da ta zama tilas su bi ta, yayin da game da hukunci ya zama dole ne ga kowa ya yi biyayya ga malami jagoran hukuma.

 

Don Karin Bayani:

1- Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat ba Diyanat, Cibiyar al’adu ta Khaniyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.

 


[1] Imam Khomain (k.s) yana cewa da wannan hanyar “Ijtihadin Jawahiri” ko “Fikihun Al’ada” (Mahdi Hadawi Tehrani, Fikhu Hukumati ba Hukumate Fikh, game da Risalar wucewar shekara ta biyar da juyayin imam Khomain (k.s), shafi: 10 – 11, watan Khurdad 1373).

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • yaya halittar mutum take a a mahangar musulunci?
  3629 Sabon Kalam 2012/07/23
  Ta mahangar Kur’ani mutum halitta ce da yake fizguwa zuwa ga ubangjinsa bisa fidirar halittarsa, kuma yake da jawuwa zuwa ga jiki, wannan halittar tana jansa zuwa ga ilimi da sani da alherai, a daya bangaren jiki tana kiransa zuwa ga sha’awa da sharri. Rayuwar mutum wani ...
 • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
  9429 دلائل ولایت فقیه 2012/07/26
  Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
 • Shin addini ya zo ne don ya mayar da mu masu 'yanci ko kuma don ya dabaibaye mu?
  8288 Sabon Kalam 2012/09/16
  Zai yiwu mu fara bayani a kan al’amarin 'yanci ta hanyar bincike da karatu dangane da ra'ayin addini ta fage biyu: 'yanci na ma'ana da 'yanci na zamantakewa da siyasa. Hakikanin mutum idan mun danganta shi ga ma'ana mai nisa (mai zurfi) ita ce nafsin ko ruhin ...
 • shin mutanen da suke rayuwa a cikin koguna danganensu na komawa zuwa annabi Adam kuwa?
  6085 خلقت انسان 2012/07/25
  Hakika zabar koguna da duwatsu domin rayuwa ga tsatson Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi lamari ne da alkur'ani ya tabbatar da shi, amma dangane da abin da ya shafi mutanen da suka gabaci Adam amincinAllah ya tabbata a gare shi, akwai abubuwa masu yawa ...
 • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
  3359 انسان شناسی 2012/07/25
  Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...
 • mene ne bambanci tsakanin Dabi’u da Ilimin Dabi’a?
  7867 Halayen Nazari 2012/07/25
  dabi’u a luga jam’I ne na ‘’kulk’’ dabi’a/hali/al’ada. Gamammiyar ma’ana saboda kasancewarta al’ada ko hali mai kyau ko mummuna. Amma ‘’Akhlak’’ dabi’u a cikin istilahi ma’anarsa malaman akhlak sun ambaci ma’anoni masu yawa. Bai yiwuwa a gwama tsakaninsu yanda ya dace. Amma sai dai musulmi ...
 • Ta wace hanya za mu iya kare kanmu daga kanbun baka?
  1938 Halayen Aiki 2017/05/20
  Kanbun baka na da tasiri a ruhin mutun wanda babu wani dalili da za a iya kore samuwar sa da shi, ballantana ma an ga faruwar abubuwa masu yawa da suka tabbatar da samuwar kanbun baka ko maita. Marigayi shekh Abbas Kummi ya yi wasici da a ...
 • Shin a mazhabar ja'afariyya ana yin sujada a tsakiyar salla yayin da aka ji an karanta ayar Sujada?
  3836 • دیگر احکام مرتبط با نماز 2013/08/12
  Bisa mahangar fikihun Shi'a wannan mas'alar ta zo ne kama haka: Idan mai salla ya karanta daya daga cikin surori hudu da suke da ayar da wajibi ne a yi sujada in an karanta su, kuma da gangan, to sallarsa ta bace
 • WADAN NE BAITOCI NE ABBAS YAKE RERAWA A LOKACIN DA YA ZO DIBAN RUWA?
  5813 اهل بیت و یاران 2012/07/26
  Mayaka yayin mubaraza a zamanin da su kan yi amfani da wani zaurance (don shaida juna ko ba da sako a tsakaninsu) don haka su kan rera baitotocin waka don samar da karfin gwiwa ga mutanensu da raunana abokan gaba. Imam (a.s) da mutanensa sun yi amfani ...
 • mene ne mahanga Kur’ani a kan halayen musulmi na zaman lafiya zakanin su da sauran mabiya addine?
  8413 Tafsiri 2012/07/25
  {Zaman lafiya tsakanin mazahabobi} na daya daga cikin fikra ta asali a musulunci ayoyi da yawa sun zo cikin Kur’ani mai girma ta fuskoki daban daban, a bayyane suna yin nuni da hakan {zaman lafiya}. A mahanga Kur’ani yaki na mazahaba saboda bambancin akida kamar yadda yake ...

Mafi Dubawa

Linkoki