advanced Search
Dubawa
13704
Ranar Isar da Sako: 2018/10/01
Takaitacciyar Tambaya
ya zamanin hallitar annabi Adam (a.s) kusan shekaru 5764 a baya zamu kwatanta su da kasusuwan da a ka samu na mutanen da suka rayu sama da {shekara miliyan 25}?
SWALI
daga lokacin zuwan annabi Adam a doran kasa zuwa yau shekaru 5764 ke nan. Tsofafin kasusuwan da a ka samu a doran kasa na mutanen da a wannan zamani yana komawa ga shekaru miliyan 25 da suka wuce, ka ba da amsa tare da dalilai.
Amsa a Dunkule
: ba wani matsala tsakanin wadannan abubuwa biyu. In da za a ce hallitar Adam yana kamawa kusan shekaru dubu shida ko bakwai da suka wuce. mai yiyuwa ne a nan ana nuni da cewa sabuwar hallitar mutum ne, don haka ba mamaki kafin wannan lokaci an hallici mutane da dama a shekaru masu yawa da suka wace kuma ya zamo ba ba su a doran kasa. Akwai alamomi masu yawa da ke nuni da cewa kafin hallitar annabi Adam (a.s) wasu mutane sun rayu kuma ba su cikin zuriyar annabi Adam (a.s).
Koyarwar addini da wasu ruwayoyi na musulunci na nuni da hakan
Amsa Dalla-dalla
Ba wani matsala tsakanin wadannan abubuwa biyu. In da za a ce halittar Adam yana kamawa kusan shekaru dubu shida ko bakwai da suka wuce. Mai yiyuwa ne a nan ana nuni da cewa sabuwar halittar mutum ne, don haka ba mamaki kafin wannan lokaci an halicci mutane da dama a shekaru masu yawa da suka wuce kuma ya zamo babu su a doran kasa. Akwai alamomi masu yawa da ke nuni da cewa kafin halittar annabi Adam (a.s) wasu mutane sun rayu kuma ba su cikin zuriyar annabi Adam (a.s).
Koyarwar addini da wasu ruwayoyi na musulunci na nuni da hakan[1].
Allama tabataba'i a cikin suratul nisa aya ta daya yana cewa: ayar a fili tana nuna cewa {nafsi wahid} ana nufin Adam sai {zaujiha} kuma a na nufin hauwa wanda su ne iyayan mutane wanda muka fito daga cikin su[2], zamu iya gane cewa ayar na nuni da cewa dukkan mutane asalin su daga wadannan mutum biyun ya ke wato Adam da hauwa. A fili ya ke ayar na nuni da cewa mutane da ke rayuwa a doran kasa yanzu asalin su Adam ne da hauwa, wadannan mutum biyun su ne kadai suka yada zuriyar dan Adam a doran kasa.
A cikin tarihin yahudawa ya zo cewa daga lokacin da a ka halitta dan Adam adoran kasa zuwa yau kimanin shekaru dubu bakwai kenan hankalima zai iya gasganta hakan. Wato a hankalce za a iya cewa halittar bata wuce wadannan shaikarun ba. Sai dai masana ilimin kasa suna ganin cewa irin mutum ya kai sama da miliyoyin shekaru da suka wuce.
A mahankar su ke nan, amma sai dai dalilan baya da da wani inganci wanda zai tabbatar da cewa duddugar kasusuwan da masu bincike suke samowa a cikin kasa na nufin cewa asalin kakanin mutanen wannan zamanin ne, kuma ba wani dalili da zai kore cewa kasusuwan da a ke samawa ba na mutanen da suka zauna doran kasa kafin dan Adam ba, saboda mai yiyuwa ne hakan ta faru wato wasu halitu na mutane kafin wadannan na yanzu sun zauna a doran kasa, wanda ba wani alaka a tsakani wadan nan hallitu biyu. Mai yiyuwa ne wasu matane kafin hallitar annabi Adam sun rayu a doran kasa kuma ya zaman to zuriyar su ta kare, da haka samuwar hallitar mutane ta zama wasu su zo su wuce har zuwa zamani hallitar Adam.
Kur’ani mai girma baiyi bayani a fili cewa ya samuwar mutane ta zamo ba shin bayyanar mutane a doran kasa ya takaita ne kawai da wannan al'ummar da muke ciki kadai, ko kuwa an yi zamani da dama ana hallitu suna wuce wa har zuwa lokacin yau, shin al'ummar yanzu su ne karshen hallitu?
Mai yiyuwa ne a wasu ayoyin na Kur’ani sun yi nuni da cewa kafin hallitar Adam wanda shi ne baban mutane an yi wasu mutane a doran kasa kamar yadda yake cewa: a zamani da Allah madaukaki ya ce da mala'iku zan sa madadina a bayan kasa sai suka ce kamar ya zaka sake sa masu barna da zubar da jini a doran kasa. [3]
Allama tabataba'i ya ce: suratul bakara aya ta 30 zamu iya fahimtar cewa kafin hallitar Adam wasu matane sun rayu wanda ya sa mala'iku suka tambayi Allah a kan sake hallitar masu barna da zubar da jini domin mala'ikun sana da sani a kan aikin da wannan hallitu suka aikata[4].
Wannan ayar na nuni da cewa kafin hallitar Adam wani zamani ya faru wanda mutane suka zauna a doran kasa kuma mala'iku su ka ga abin da suka yi na barna da zubar da jini.
A cikin wasu ruwayoyi na imamai (a.s) akwai wasu abubuwa da ke nuni cewa kafin mutanen wannan zamani an yi wasu mutanen daban.
Sheikh saduk a cikin littafin tauhid ya rawaito daga imam sadiq (a.s) cewa: shin abin mamaki ne a kare ku cewa Allah madaukaki ya yi wasu matane ba ku ba? A 'a bahaka ba ne, an dai hallita dubanin mutane wanda ku ne karshen su[5].
Marikayi suduk a cikin littafin khasal, daga imam bakir (a.s) ya rawaito cewa: ranar da Allah madaukaki ya halitta duniyoyi bakwai {sannan ya gama da su} dukkan wadannan duniyoyin babu daya wadda zuriyar Adam suka zauna a ciki Allah madaukaki ya hallita wannana duniyoyi kuma ya sa zuriya bayanzuriya kowace zuriya ya hallita mata duniyar ta daban, wanda daga karshe a ka hallita Adam baban mutanen wannan zamani wanda daga gare shi ne al'umma da yadu. [6]،[7]
A bisa haka ne, za a ce da za a samu sauran wani abu wanda ke nuni da wasu hallitu wadanda suka rayu sama da miliyoyin shekaru to wannan baya na nufin cewa ya shafi hallitar mutanen yanzu ba ne domin, a fili ya ke cewa hallitar annabi Adam (a.s) bai wuce shekaru 7000 ba[8].
Karin bayani a duba tambaya lamba ta: 506. Da kuma lamba ta: 731.
 

[2] Tarjamar almizan jildi na 4,shafi na 214,qom, bugawa ofishin yada musulunci,1417.
[3] Bakara 30.
[4] Tarjamar mizan jildi na 4, shafi na 223.
[5] Shaikh suduk, tauhid ,shafi na 277, jildi na 2,bugun Tehran.
[6] Sheikh suduk, khasal, jildi na 2, shafi na 652, jildi na 54.
[7] Daga fuyiko fursiman kur'ani.
[8] A na iya dubawa cikin{sayit tambaya da 701} shekarun nau'I mutum cikin kur'ani.
 
 
 
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa