Babu wani kokwanton cewa Allah (s.w.t) ya san komai, kuma a kowane hali, kuma babu wata ma’ana ga boye wa Allah wani abu, haka nan Allah (s.w.t) ba shi da hukuncin namiji ajnabi game da mace yayin addu’a? sai dai yayin ibada mutum yana samun kansa a ...
Marja’anci da ma’anar kasancewar malami makoma ne shi a karbar fatawa wurinsa a fikihu yana kishiyantar ma’anar koyi da malami ne. Domin a ma’anar koyi yana nufin wanda bai kware ba kan wani lamari ya koma wa wanda ya kware, wato yana nufin ke nan a koma ...
Ana iya tabbatar da Wilaya da jagorancin ma'asumai (a.s) a cikin madogarar dalilai hudu na shari'a da ya hada da Littafi, Sunna, Hankali, Ijma'. Dukkan malaman Shi'a kalmarsu da maganarsu ta hadu gaba daya ba ma tare da koma wa maganganunsu ba, kai hatta da ...
Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin. Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana ...
Sallar firgici, ko sallar Daren Binnewa, salla ce da ake yin ta ga mamaci a farkon lokacin da aka binne shi, don haka ne ma ake kiran ta da salar firgici, domin yayin da mutum yake barin wannan duniayr bai saba da waccan duniyar sabuwa ba, kuma ...
A cikin Kur'ani mai girma muna karanto wannan ayar {lalle ba ku yake su ba, sai dai Allah ne ya yake su kuma Ba kai ne (ya kai wannan Annabi) ka yi jifa ba (a lokacin da ka jefe su da kasa da duwatsu) a lokacin da ...
Ba shakka cewa Kur’ani ya bayyana a Fili cewa Annabi Isa (a.s) an ba shi Matsayi mai Girma Alhali ma yana cikin Tsumman Goyo: ’sai Ta yi nuni a gare shi sai sukace ta yaya zamu yi Magana da wanda yake cikin Tsumma, sai ya ce ni ...
an tambayi daftrorin marja’ai masu alfarma kan tambayar da ka yi kuma ga amsar da suka turo. Ofishin mai girma Ayatullah sayyid Ali Khamna’i (Allah ya tsawaita rayuwarsa): Kalllon finafinai masu tada sha’awa na sa mutun ya karkata zuwa tafarkin shedan na son zuciya kuma yana raunana ...
Gaskiya tana nufin hanya matsakaiciya, wato ana nufin maganar daidai da bin hakika, gaskiya ita ce sanya komai da hikima bisa mahallinsa da ya dace da shi. Sannan bin gaskiya da tafiya kanta bisa tafarkinta a fagen tunani yana nufin tanadin makamin ilmi da mantik ...
Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...