advanced Search
Dubawa
12489
Ranar Isar da Sako: 2008/05/27
Takaitacciyar Tambaya
su wane ne zuri’ar yajuj da majuj? Ya karshen su ya zamo? Wane mataki Zulkarnaini ya dauka a kan su?
SWALI
shin zaka iya ba da bayani a kan yajuj da majuj? Su wa ne su? Shin Zulkarnain ya halaka su ne? shin nan gaba zasu sake dawowa?
Amsa a Dunkule

Tarin ayoyi na Kur’ani da Attaura da kuma bayanan tarihi a kan yajuj na nuni da cewa wannan a’umar ta rayu ne a yankin arewacin asiya sai dai sun ta kai ma yankin kudu da yamma hare hare masu tsanani. Amma lokacin da Zulkarnaini ya yi bango a tsakani su da sauran al’umma hare haren su ya yi sauki amma a karshen zamani za su sake dawowa. Wasu na ganin dawowar su shi ne zuwan magul da hare haren su ga sauran wurare kuma hakan ta faru. Amma wasu na da mahangar cewa dawowar su shi ne Allah zai sake raya su ne a karshen zamani wanda har zuwa yau hakan bai faru ba.

Amsa Dalla-dalla

Asalin tushen bayani a kan yajuj da majuj shi ne Kur’ani mai girma sai dai littattafan Attaura sun yi nuni da hakan.

Masu tafsiri da masana tarihi sun yi amfani da wadannan dalilai biyu {Kur’ani da Attaura} da kuma binciken tarihi wanda ke nuna samuwar al’ummar yajuj da majuj.

A guri biyu cikin Kur’ani ya yi bayani a kan yajuj da majuj kamar haka: Zulkarnaini ya zo tsakanin tsaunuka biyu sai ya samu wasu al’umma mazauna gurin kuma ba sa fahimtar kowane magana sai suka ce ya Zulkarnaini yajuj da majuj na barna cikin kasa shin zaka iya sa tsakani mu da su mu kuma mu dauki nauyin aiki…" Kur’ani ya bayyana yanda a kai aikin gini ya kuma cigaba da cewa: su {zuri ar yajuj da majuj} ba su da ikon tsallake ginin ko kuma su huda shi. [1]

Da haka zamu iya amfani da wannan ayar mu gane cewa yajuj da majuj al’umma ce azzaluma amma lokacin da Zulkarnaini ya gina bango zakanin tsaunuka biyu sai ya kawo karshen zaluncin su.

A wata ayar Kur’ani na cewa: ya zuwa zamani da za a bude yajuj da majuj wanda cikin sauri duk wani abu mai tsayi za su ketare shi to a lokaci ne wa adin Allah ya kusa wato [kiyama] [2]. …. Mahangar wannan ayar shi ne a karshen zamani, yajuj da majuj zasu fito tsakanin tsaunuka biyu. Abin da zamu iya fahimta a kan su cikin Kur’ani bai wuce aya biyu ba ka dai.

Amma cikin littafan ataura ma akwai magana a kan su, a ciki sifr takawini da kuma littafin hazgyal a cikin mafarkin yuhan ya zo wanda ke nuni da cewa {yajuj da majuj} al’umma ce wadda ta zamo a yankin arewacin asiya da irazi abad kuma sun kasance suna yaki da fitina da kuma mamaye wurare {garuruwa}[3]. Ba Kur’ani da Attaura ba kawai su kayi bayani a kan su ba. Wasu bayanen wanda masana tarihi da masu fassara da dukkan dalilan da suka tare amma ba wani dalili tabbatace a kai.

Allama taba taba"I cikin tafsirin mizan yana cewa: masu tafsiri da masana tarihi sun yi dikka so sai a kan wannan labaran duk suna nuni da cewa yajuj da majuj al’umma ce mai girma wadda ke rayuwa arewacin asiya[4]. Wasu kuma na cewa al’ummar yajuj da majuj suna zaune ne a yankin arewacin asiya, garuruwan su sun fara daga tibit da kasar cana har zuwa sandararan taiku na arewa daga yammaci kuma suna kusa da turkuministan wannan bayani an rawaito shi ne dag a {fakihatlkhulafa} da {tahzibal akhlag} na ibin miskawi da [risalat ikhwan safa} [5].

Allama husaini tahrani a cikin littafin shi maad shinasi {sanin lahira} a kan tabbatar da Kalmar yajuj da majuj da kuma sauran ruwayoyi da suka zo a kan su ya fidda sakamako cewa: {asalin kalmomin biyu " [munkuk da munjuk} ne amma da harshen ibrani da larabci sai suka koma yajuj da majuj a cikin harshen girka suna cewa {kuk da makuk} saboda kamanin kalmomin zamu fahimci cewa Kalmar lafazi ne na harshen kasar cana. Sannan suka zama mangul da magul. Don haka magul su ne yajuj da majuj wadanda suka rayu arewa maso gabas na asiya wadannan al’ummu masu girma sun kasance suna kai hare hare ma kasar cana wani lokaci kuma ta kogin kafkaz suke bi domin kai ma armanistan da arewacin Iran hari, wani lokaci bayan gina bango sai suka rika kai ma kasashen turai na arewa hari mutanen turai suna kiran su da {sit} wasu daga cikin su sun kai hari ga kasar roma kuma sukaci nasara a kan romawa. Turawan girka na kiran su da {si tihin} wannan suna ya zo cikin littafin darush cikin istkhar farsi[6].

A fili Kur’ani bai yi nuni da halakar su ba, abin da zamu iya amfana da shi a cikin Kur’ani cewa lokacin da a kai gina bango sai hanyar su ta hare hare ta rufe. Amma cewa suna da rai har yanzu ba zai yiyu a yi amfani da aya ko ruwaya ba a kan haka. Sai dai ibin abbas cikin suratul anbiya ya yi nuni da mutuwar su. Saboda ibin abbas Kalmar {hadab} wadda ke nufin wuri mai tsawo {jaddasa} ya bayyanata wanda ke nufin kabari. In haka ne ma’anar wannan ayar zai zamo: ya zuwa lokacin da yajuj da majuj za su fito daga kaburburan su da sauri[7]. Wasu ruwayoyi cikin tafsirin wannan ayar sun ce: a karshen zamani yajuj da majuj za su sake dawowa wannan duniya[8]. haka na nufin cewa a yanzu ba su cikin wannan duniyar sai dai nan gaba zasu dawo.

Masana sun samu bambamci fahimta dangane da sake kai hare haren su. Wasu masu bincike suna ganin labarin Kur’ani da yake cewa karshin zamani yajuj da majuj za su fito, na nuni da hare haren tatar {magul} da su ka kai yammacin asiya a tsakiyar farkon karni na bakwai na hijira. Saboda awannan lokaci ne magul suka bayyana da zubar da jini kashe rayukan mutane, lalata garuruwa barna da kwace dukiyoyi sun aikata ta’addanci da tarihin dan Adam bai taba ganin makamancin shi ba. Kasashe kamar su cana da turkuministan da Iran da Iraki da Sham da Kafkaz har zuwa asiya karama sun kasance cikin kasashen da magul suka bata da kuma kashe rayuka da dama na mutane[9].

Sai dai wasu masu bincike na ganin cewa in ya zaman to yajuj da majuj bayan da aka yi bango kuma lokaci mai tsawo da ya wuce sun mutu amma karshen duniya za su dawo ba zamu ce magul ba ne domin fitowa kabari bai tabbata a kan su.

Akarshe duk abin da aka fadi a kan su zai zamo zato ne kawai babu tabbaci a kai sai dai mu dogara da abin da Kur’ani ya yi bayani kadai.

 

 


[1] kahafi,93-97.

[2] Anbiyya, 96-97.

[3] Husaini tahrani sayyid Muhammad Husain, ma'ad shinasi, jildi na 4,shafi na 85 ko sayit na mu'asas tarjima da yadawa na daura ulum da ma'arif islami.

[4] Taba'taba'i sayyid Husain, almizan fi tafsir kur'an, tarjamar, musawi hamdani, sayyid Muhammad baqir,jildi na 13,shafi na 542 yadawar taftare nashre islami 1374.

[5] Husaini tehrani,sayyid Muhammad Husain ma'ad shinasi jildi na 4, shafi na 87.

[6] Adreshi na sama shafi na 87.

[7] Najafi khumaini, Muhammad jawad, tafsirin asan jildi na 12, shafi na 366, yadawar iskamiya 1398 k.

[8] Majalisi ,biharul anwar, jildi na 12, shafi na 179, wafa'a, 1404,k.

[9] Taba'taba'i sayyid muhammad Husain,almizan fi tafsir alkur'an, tarjamar musawi hamdani,sayyid muhammd baqir,jildi na 13,shafi na 542.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Yaya zan tuba daga kallon film mai batsa?
  20577 توبه
  Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
 • Shin addini ya zo ne don ya mayar da mu masu 'yanci ko kuma don ya dabaibaye mu?
  10017 Sabon Kalam
  Zai yiwu mu fara bayani a kan al’amarin 'yanci ta hanyar bincike da karatu dangane da ra'ayin addini ta fage biyu: 'yanci na ma'ana da 'yanci na zamantakewa da siyasa. Hakikanin mutum idan mun danganta shi ga ma'ana mai nisa (mai zurfi) ita ce nafsin ko ruhin ...
 • Me ake nufi da hadisi rafa’i
  9573 مبانی فقهی و اصولی
  An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
 • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
  1647 زن
  Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
 • Akwai tuhumar da ake wa Annabi cewa ya koyo kur’ani daga wani mutum ba’ajame, mene ne labarin wannan kissa?
  1336 Ilimin Kur'ani
  Kur’ani littafi ne da yake matsayin littafin cikamakin annabawa (s.a.w) wanda yake kumshe da mu’ujizozi masu tarin yawa, ayoyin da suka fara sauka daga cikin kur’ani yawancinsu sun gigita zukatan mutane, daga fasahar su da balagarsu wanda ya kasance tare da ma’anoni cikin zirin lafuzza kyawawa takaitattu ...
 • su wayi shuwagabannin samarin gidan aljanna?
  1358
  Imam Hasan da Husain jikokin manzan Allah (saw) shawagabannin ne ga dukkanin ‘yan aljanna kuma su shugabannin samarin gidan aljanna ne. amma shugabancin su ya fi karfi kan samarin da suka yi shadan a lokacin samrtarsu, kuma wannan bai ci karo da shagabancin sauran manzanni da Annabawa ...
 • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
  2288 ویژگی ها و مناقب
  Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
 • Ku gaya mana wani hadisi game da iyakokin lullubin Mace
  6406 زن
  Ayar 31 daga Surar Nur da ruwayoyi masu yawa sun kawo lamarin hijabi lullubin mata da yadda yake, yayin da Allah madaukaki yake cewa: (Surar Nur: 24: 30-31) "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne ...
 • Yaushe Aka Haifi Ammar Dan Yasir Kuma Wace Irin Rawa Ya Taka A Kwanakin Musulunci Na Farkon?
  1027 تاريخ بزرگان
  Ya Dan’uwa mai girma muna masu baka hakuri sakamakon jinkirin da aka samu wajen aiko maka da amsar tambayarka/ki a sakamakon yanayin ayyuka da suka sha kanmu. “Ammar Dan Yasir Dan Aamir” ana yi masa alkunya da ‘Abu YaKazan” kuma ya kasance abokin rantsuwa ne shi (wato ...
 • Mene ne Dalilin wilayar Ma'asumai (a.s)?
  7667 ولایت، برترین عبادت
  Ana iya tabbatar da Wilaya da jagorancin ma'asumai (a.s) a cikin madogarar dalilai hudu na shari'a da ya hada da Littafi, Sunna, Hankali, Ijma'. Dukkan malaman Shi'a kalmarsu da maganarsu ta hadu gaba daya ba ma tare da koma wa maganganunsu ba, kai hatta da ...

Mafi Dubawa