Dubawa
5091
Ranar Isar da Sako: 2011/01/10
Takaitacciyar Tambaya
Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai?
SWALI
Salamun Alaikum, Don Allah Ina Son A Amsa Mun Wannan Tambaya: Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai, Wato Shin A Take Ya Zamo Musulmi Ne Ko Mutum Ne Kawai?
Amsa a Dunkule

Mutumtakar Mutum A Tare Da Samuwar Sa Take, Ta Yanda A Dukkan Yanayi Ba Zai Yiwu A iya Raba Ta da Shi Ba, Sabanin Shi Musuluncinsa shi Ba a Danfare Da Samuwarsa yake Ba, Sai Dai Zuwa yake Yi, Wato zamu iya Suranta Samuwar Mutum Wanda Ba Musulmi Ba, Kamar Dai Sauran Mutanen da ba Musulmai Ba, A Daya Bangaren Kuma Dan Da Mutum Ya Haife Shi Shi ma Mutum Ne, To Amma Musuluncinsa, A Lokacin Da Yake Yaro Marar Wayo, Bai Karbi Musulunci A bisa Fahimta Ba, Shi Ba Musulmi Ba ne, To, Amma idan Dukkan Mahaifansa Musulmi Ne, Ko Dayan Mahaifansa, Ko Kakansa Musulmi Ne, Za a Yi Masa Hukuncin Shi Musulmi Ne[1].

Ko Da Yake A Bisa Ga Nassoshi Na Ruwayoyi[2] Duk Wani Da Ana Haifarsa Ne A kan Addinin Tauhidi, Wanda Allah Ya Halicce Shi A kai, Saboda Haka Idan Ya Samu Zarafi A bisa Tarbiyyar da ya Samu, Tabbas Zai Riki Musulunci Ne A Matsayin Addini, Amma Ba Wani Abu Daban ba, Sai Dai Zai Yiwu Iyayensa, Ko Al’ummarsa Su Nisantar da shi daga Barin Wancan Halitta Na Tauhidi da aka Masa Ta Hanyar Koyarwa da Gurbataccen Ilimi.

 


[1] Taudhihul masa’il cikin hashiya na Imam Khomein juzu’i na 1 shafi na 78 mas’ala ta 108: Idan dayan iyaye ko kaka namiji na yaron da bai balaga ba, kafiri ne, to, shi ma dan najasa ne, idan kuma dayansu musulmi ne to shi ma dan zai bisu a zamowa musulmi.

[2] Shekhus-saduk, man la yahadhuruhul fakih juzu’I na 2 shafi na 49 hadisi na 1, 668 intisharat jami’atul mudarrissin, kum, 1314hijira kamariyya: ko wani abun haihuwa ana haifarsa ne a kan addinin tauhidi sai dai iyayensa ne suke sashi ya zamo yahudu ko kirista ko bamajuse”

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • mene ne hanyar debe kewa da Kur’ani
  4814 Halayen Aiki 2012/07/25
  idan ya zama tilawar da mutum zai yi ta Kur’ani don neman kusanci ne zuwa ga Allah, da tadabburi da bibiyar aiki da shi, to zai zama tilawar ta kusantar da shi ga manufar Kur’ani sosai, zai zama son Kur’ani zai tsananta. ...
 • Mene ne ma'anar jagorancin malami?
  5867 کلیات 2012/07/24
  Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci. "Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu: 1- Wuraren da wanda ...
 • Zuwa wane haddi ne daula (gwamnati) ko doka zasu iya iyakance 'yancin mutum?
  4649 Tsare-tsare 2012/07/24
  Ana amfani da Kalmar 'yanci da ma'anoni daban-daban kamar zabi, barin 'yancin sha'awa da makamantansu, sai dai abin da yake ma'aunin bincikenmu a nan shi ne abin da ake gani a matsayin 'yancin dan Adam, ko kuma 'yancin al'umma a siyasance. Wasu mutane sun yi ...
 • duk da cewa mace zata iya shiga cikin majalissar kwararru ta zaben shugaba, shin zakuma ta iya zama shugaba?
  3517 نهادهای حکومت دینی 2012/07/25
  Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake ...
 • Saboda me samuwar tunani daya gamamme don bayanin musulunci yake dole?
  3171 Sabon Kalam 2012/07/24
  Zuwa yanzu malaman addini suna da masaniya mai yawa da aka tattara ta game da ilimin musulunci wanda yake kunshe da dokoki da ka'idoji. Akwai tafarkin ganin abubuwa ta mahanga tsukakkiya da kuma ta hankali, wannan lamari ne ya sanya aka rasa wata makama mai fadi game ...
 • da lokacin saukar da kur'ani ta sauka lokaci daya da kuma ta sauka a hankali ahankali zuwa yau shaikara nawa ne?
  10019 Ilimin Kur'ani 2012/11/21
  Sauko da kur'ani a cikin zuciyar manzon Allah mai tsira da aminci alokaci daya {daf'i} tabbas ya faru ne a cikin dare na lailatulgadari {daya daga cikin darare na watan azumi mai alfarma}. Idan akai bincike a cikin ruwayoyi da kuma dalilai, za 'a iya ...
 • su wayi shuwagabannin samarin gidan aljanna?
  139 2019/06/16
  Imam Hasan da Husain jikokin manzan Allah (saw) shawagabannin ne ga dukkanin ‘yan aljanna kuma su shugabannin samarin gidan aljanna ne. amma shugabancin su ya fi karfi kan samarin da suka yi shadan a lokacin samrtarsu, kuma wannan bai ci karo da shagabancin sauran manzanni da Annabawa ...
 • A kawo hadisan da suka yi haramta rawa da kuma madogararsu.
  6873 بیشتر بدانیم 2013/08/15
  Kafin mu ba da amsar wannan tambayar ya kamata mu lura da wani abu guda mai muhimmanci kamar haka, dan an samu ruwaya daya a cikin litattafan ruwayoyi bai wadata ba wajan kafa dalili da ita ruwayar. Domin kafa dalili da ruwaya wani abu ne da ya ...
 • Me ye alaka tsakanin Zuhudu da ci gaban zamani?
  5469 Halayen Nazari 2012/07/24
  Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin ...
 • me ake nufi da rayuwar addini? Shin akwai karo-da-juna tsakaninta da rayuwarmu ta yau da kulum?
  7546 بندگی و تسبیح 2012/07/25
  Da zamu koma ga Kur’ani mu tambaye shi kamar haka: - Me ya sa aka halicci aljannu da mutane? Kur’ani zai ba mu amsa cewa: Ban halicci aljannu da mutane ba face sai don su bauta mini”1 Sai mu sake yin tambaya mene ne ma’anar ...

Mafi Dubawa