advanced Search
Dubawa
4718
Ranar Isar da Sako: 2016/12/30
Takaitacciyar Tambaya
Idan Manzo (s.a.w) ya la’anci daya daga cikin musulmai ya kore shi daga rahama shi wannan la’anar daga karshe za ta canja ta zama kyakkyawan aiki kuma sakamako na gari ga wadanda aka la’anta?
SWALI
A cikin litattafan Ahlussunna na asali awaki wasu ruwayoyi kamar haka “) “Ya Allah duk wani musulmi da na zaga to ka sanya zagin da na yi masa ya zama kusanci zuwa gare ka ranar alkiyama” menene matsayin irin wadannan ruwayoyi kuma shin irin wadannan ruwayoyi zasu iya zama ingantattu?
Amsa a Dunkule
A cikin wasu daga cikin jigon litattafan Ahlussunna akwai wasu ruwayoyi kan wannan lamari wadanda suka doru kan wasu dalilan da ba za su zama karbabbu ba:
  1. An rawaito Manzon Allah (s.a.w) “Ya Allah! duk wani musulmi da na zaga to ka sanya zagin da na yi masa ya zama kusanci zuwa gare ka ranar alkiyama”! [1]
  2. Ummu sulaimi: tana da yaro maraya, a lokacin da Manzo (s.a.w) ya ga yaron sai ya ce kai ne? lalle ka girma, kada Allah ya kara yawan hakoranka; sai yaron ya fashe da kuka bai zame ko in aba sai wajen babarsa ummu sulaimi ta ce me ya faru? Yaron ya ce “Manzon Allah (s.a.w) ne ya yi min addu’a kada hakora na su kara girma don haka ba zan kara girma ba ma, nan da nan sai ta yafa mayafi ta fito da sauri, ta tafi wajen Manzon Allah (s.a.w) ta ce: ya Ma’ankin Allah ka la’anci maraya na! Manzo (s.a.w) ya ce:  “me ya faru ummu sulaimi?!”  ummu sulaimi ta ce: da na yana da’awar cewa ka tsine masa don kar ya kara girma sai Manzo (s.a.w) ya yi dariya sannan ya ce : shin ba ki san cewa na gayawa Ubangiji  cewa ni ma kamar sauran mutane na ke daya ne daga cikinsu wani lokacin na kan yi farin ciki wani lokaci kuma na kan yi fushi, don haka duk wanda na tsinewa (na la’anta) kuma be cancanci hakan ba to ka sanya ta ta zama tsarki da tsarkaka da kusanci zuwa gare ka”. [2]
  3. A mada’in Huzaifa ya yiwa mutane huduba a ciki yana cewa an ce Manzon Allah (s.a.w) ya yi magana kan sahabbansa lokacin da ya ke cikin fushi. Sai wasu mutane daga sahabbansa suka gayawa Salmanu hakan sai Salmanu ya ce huzaifa bai da masaniya kan abin da yake fadi sai suka tafi wajen huzaifa suka gaya masa mun gaya wa Salmanu abin da ka fada amma bai gasgata abin da ka fada ba kuma be karyata ba!.
Sai huzaifa ya tafi wajen Sulaiman ya ce da shi: don me ba ka gasgata abin da aka ji daga Manzo (s.a.w) kuma aka nakalto daga gare shi ba? haba Salman! Ka sani wani lokaci Manzo (s.a.w) kan yi fushi kuma ya kan fadi wani abu (mara kyau) kan sahabbai kuma wani lokaci ya kan zama cikin farin ciki sai ya fadi wani abu (na gari) kan wasu daga cikin sahabbansa! Saboda me ka sani cewa abin da ka yi zai sa mutane su rika ganin wasu daga cikin sahabai mutanen kirki wasu kuma mutanen banza sannan su rika banbanta tsakaninsu!? Ashe ba ka ji Manzo (s.a.w) yana cewa ba: “ni daya ne daga cikin ‘ya’yan Adam (a.s) kuma mutum ne kamar kowa ina yin fushi duk da cewa Allah Ta'ala ya aiko ni rahama ga bayinsa. Don haka duk wani mutum da na fadi mummunar kalma a kan sa ko na la’ance shi (na stine masa) cikin halin fushi daga cikin al’umma ta Allah ka sa hakan ya zama addu’a a gare shi”. [3]
Akwai ruwayoyi makamantan wadannan a cikin litattafin Ahlussunna. [4]
Amma idan aka duba sosai za’a fahimci cewa wadanda suka kirkiri irin wadannan ruwayoyin mutane ne kamar su banu ummayya (dangin mu’awuya) suka kirkira, wandanda Manzo (s.a.w) ya la’ance su ya tsine musu a sarari. Don haka dalilai na hankali da na nakali sun tabbatar da cewa dukkanin wadannan ruwayoyin ba su yi kusa da ingantattan ruwayoyin da za a karba ba. ga dalilai kamar haka:
  1. A cikin wannan ruwayar an ambaci cewa Manzo (s.a.w) ya ce tunda ni Dan’adam ne ina yin kuskure! Da wannan dalilin da za mu iya cewa Manzo (s.a.w) ya yi kuskure hatta a la’anar da ya yi kan wadanda ba musulmai ba!? Shin idan Manzo (s.a.w) ya yi kuskure (kan la’antar wasu mutane sai kuma sakamakon haka ya zama shi ne a canja musu wannan la’anar da lada!? Shin wai malaman Ahalussuna sun yi imani da wannan maganar?!
  2. Manyan litattafai da suke makoma ga ahlussuna sun nakalto wasu ruwayoyi wadanda kai tsaye ko ba kai tsaye ba suna kishiyantar ruwayoyin da su ka gabata.
“Duk mutumin da ya la’anci mumini tamkar wanda ya kashe shi ne”.[5]
“idan mutum ya la’anci wani, idan wannan mutumin ya cancanci a tsinuwa, da sannu zata riske shi, idan kuma be cancance ta ba to wannan la’anar zata koma kan wanda ya yi ta”. [6]
“zagin musulmi kafirci ne”. [7]
Dukkanin wadannan ruwayoyin sun zo a cikin manya-manyan litattafan Ahlussunna wanda bisa asasinsu ya zama lalle mu kudurce cewa idan har Manzo (s.a.w) ya tsinewa wani musulmi a cikin fushi tamkar ya kashe shi ne, la’anrsa zata koma zuwa gare shi kuma daga karshe - Allah ya kare- zai zama fasiki.
Shin akwai wanda zai iya yin da’awar cewa shi musulmi ne sannan ya jinginawa Annabin sa iran wannan mummuninan aiki?!
  1. Daga karshe shi’awa sun kudurce da cewa Manzo (s.a.w) ma’asumi ne kuma har abada ba zai taba la’antar mutumin da be cancanci la’ana ba kuma kadai wadanda suka cancanci tsinuwa yake tsinewa ko da kuwa asarari suna da’awar cewa su musulmai ne alhali a bisa hakika su wadannan mutanen ba musulmai ba ne kuma ba muminai ba.
Kari a kan haka idan wasu daga cikin malaman Shi'a sun tafi kan cewa ya halatta Manzo (s.a.w) ya yi “rabkanuwa” kan abubuwa na al’ada kamar rage adadin abin hawa ko kuma mance sunan mutum, [8] amma ba su taba yarda cewa Manzo (s.a.w) na yin kuskure irin na ya yi zagi ko ya tsinewa wanda bai cancanta ba har abda.
 

[1]  Bukhari Muhammad  dan isma’il, a jami’ul musnad assahihul mukhtasar mun umuri rasulil lah, wa sunanihi waayyamihi, (sahihu buhari) muhakka, annasir Muhammad  zuhair nazisir j 8 shafi na 77 bairut, darul daukin najat bubu na daya 1422. Da abubukar baihaki Ahmad dan Husain dan Ali munanul kubra wanda aka yiwa tahkiki, abdulkadir ada’u j 7 sh 97 bairut darul kutubul ilmiyya bugu na uku 1424.
[2] Kaishari, nishaburi muslim dan hajjaju, musnadis sahihil mukhtasar adali ya dakalto daga adali zuwa Manzon Allah (s.a.w) (sahihu muslim) wanda abdulbaki ya yiw tahkiki Muhammad  Fu’adu  j 4 sh 2009, bairut darul ihya’I turasul arabi. Ba shakarar bugawa.
[3] Bukhari Muhammad  dan isma’ila , al’adabul mufraradi, wanda abdulbaki ya yiw tahkiki Muhammad  Fu’adu j 1 sh 91, bairut darul busha’irul islamiyya bugu na uku, 1409. Da kuma sajastani abu dauwuda sulaiman dan ash’as sunanu abi dauwud, wanda abdulhamid ya yi wa tahkiki Muhammad  muhyid dini  j4 s 215, bairut almaktabatul asriyya. Ba shakarar bugawa.
[4] A koma zuwa abu sa;id bin a’arabi, Ahmad dan Muhammad  dan ziyad, mu’ujam bin a’araabi, wanda Husain abudulmuhsin dan Ibrahim dan Ahmad ya yi wa tahkiki j 1 sh 288 saudiyya darul bni jauzi, 1418. Alkhara’id assamiri abubakar Muhammad  dan ja’far almuntaka daga littafin makarimul akhlak wa ma’aliha wa muhamudu dara’ifiha, wanda Muhammad  mudi’ul hafiz da kuma gazwatu badir suka yi wa tahkiki j 1sh 87, damashka darul fikir 1406.
[5] Bukhari j 8 shafi na 15.
[6] Abubakar baihaki, Ahmad dan Husain, a cikin shu’abul imani j 7 sh 149, Riyadh, maktabatur Rashid linnashri wattauzi’i, bugu na farko 1423. Da dan banbanci kadan a bugun: abu kasim dabarani sulaimanu dan Ahmad, addu’u wanda abdukadir ada’u Mustafa ya yi wa tahkiki, j 1 shafi na 575. Bairut darul kutubul ilmiyya, 1413.
[7] Shaibani, Ahmad dan Muhammad  dan hanbali a cikin assunna, mai tahkiki alkahdani, Muhammad  said saalim, j 1 shafi na 364, aldammad daru ibnil kayyum, 1406.
[8] A koma jigo mau suna:  sahwun nabiyyi wa didgahe matakallimin (rabkanuwar Annabi da ra;ayin malaman kalam).
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa