Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
Marja’anci da ma’anar kasancewar malami makoma ne shi a karbar fatawa wurinsa a fikihu yana kishiyantar ma’anar koyi da malami ne. Domin a ma’anar koyi yana nufin wanda bai kware ba kan wani lamari ya koma wa wanda ya kware, wato yana nufin ke nan a koma ...
Bisa mahangar fikihun Shi'a wannan mas'alar ta zo ne kama haka: Idan mai salla ya karanta daya daga cikin surori hudu da suke da ayar da wajibi ne a yi sujada in an karanta su, kuma da gangan, to sallarsa ta bace
samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
{uwaimar dan malik} wanda ya shahara da alkunyar abuddarda”dan asalin kabilar khazraj yana daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w). yana daya daga cikin mutanen khazjar da suke rayuwa a madina ya shiga musulunci bayan zuwan manzon Allah (s.a.w) madina da wasu yan watanni. Abuddarda”yana fifita imam Ali (a.s) a ...
Ka iya samun wani mutum yana kokarin cin mutuncin wani da yake adawa da shi ko ta hanyar bata masa rai da tsawa da tada hankali. To shi Musulunci yana ba da damar ramuwa, watau “ramuwar gayya”. Sai dai a garin ramuwar bai dace a ci mutunci ...
AYATULLAHI KHAMNA’IY (MZ) Idan tsaretan shi ma zai cutar da ita bai halatta ba MUKARIMUSH SHYRAZY (MZ) Idan babu makawa sai an tsare ta babu laifi MAHDY HADAWY (MZ) Idan za’a ...
Jagorancin malami wani isdilahi ne na fikihu da yake nuni da fagagen aiki da jagoranci da kuma wadanda suke karkashin wannan jagora, kuma babu wata iyaka a wannan fagen. Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kowace irin iyaka ko wasu ka'idoji a aiwatar da jagoranci ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...