A cikin koyarwar musulunci, mata suna da matsayi na musamman, ruwawoyi na manzon Allah da a imam[a. s] sun yi bayanin a kan hakan. Ya zo a cikin ruwayoyin mu cewa mata salihai tushe ne na alkhairi da albarka kuma suna cikin abubuwa masu daraja da kima ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Matanin da ahlussunna suka cirato daga sahihul Muslim da Turmuzi da musnadi Ahmad wanda ke cikin wannan littafan ya zo ne kamar haka “littafin Allah da ‘yan gida na” kuma wannan shi ne matanin da ya shahara a wajen ahlussuna. Amma akwai wani matanin da ba wannan ...
Jagorancin malami wani isdilahi ne na fikihu da yake nuni da fagagen aiki da jagoranci da kuma wadanda suke karkashin wannan jagora, kuma babu wata iyaka a wannan fagen. Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kowace irin iyaka ko wasu ka'idoji a aiwatar da jagoranci ...
Sauko da kur'ani a cikin zuciyar manzon Allah mai tsira da aminci alokaci daya {daf'i} tabbas ya faru ne a cikin dare na lailatulgadari {daya daga cikin darare na watan azumi mai alfarma}. Idan akai bincike a cikin ruwayoyi da kuma dalilai, za 'a iya ...
Gwamuwar jin tsoron Allah da kaunarsa, a wasu lokutan kuma kaunarsa kawai, dangane da Allah ba wani al’amari ba ne da yake bako, domin shi ya cika dukkanin bangarorin rayuwarmu, amma saboda tsananin bayyanarsa sai mu din muka rafkana da shi. Mu sani cewa har ...
Hakika zabar koguna da duwatsu domin rayuwa ga tsatson Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi lamari ne da alkur'ani ya tabbatar da shi, amma dangane da abin da ya shafi mutanen da suka gabaci Adam amincinAllah ya tabbata a gare shi, akwai abubuwa masu yawa ...
Kida {muzik} da rawa wasu abubuwa biyu ne da suke da hukunci ma bambamcin juna inda alokaci daya mutun zai hada rawa ta haram da kida na haram, to ya aikata laifi {zunubi} biyu ne daban daban a lokaci daya. Mafiyawanci malaman figihu kida {muzik} wanda ya ...
Bama musun yiyuwar wannan ruwaya kai tsaye sai dai wannan ruwaya ba a cika samunta ba sai a litattafan da suka yi nisan zango da zamanin amirul muminin (a.s) nisanda mafi karanci shi ne shekara dubu, marubucin <Auwal musha sheen> na daga marubutan karshe ya ciro wannan ...
Dangane da tabbatar da mustahabbancin karanta kur'ani ga mamata akwai nau'in dalili kan hakan guda biyu: nau'in farko shi ne riwayoyi da suke gamammen bayani kan tunawa da mamata domin su mamata suna amfana da kyawawan ayyukanku sannan bayyanannen al'amari ne cewa karatun kur'ani yana daga cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...