advanced Search
Dubawa
1365
Ranar Isar da Sako: 2010/12/21
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne manufar Annabi (s.a.w) da ya ce: “Bai kamata a yi jayayya a gabana ba” abin da ya fada bayan yin jayayya a tsakanin sahabbai dom me ya nemi takarda? .
SWALI
An riga an san cewa fiyayyen annabi (s.a.w) a rashin lafiyarsa ta karshe ya nemi a bashi tawada da alkalami da takarda domin ya rubuta musu wasiyarsa. saidai abin bakin cikin shi ne, yadda sahabbai suka rarraba, wasu na cewa amika masa, wasu na hanawa. da annabi ya yi fushi sai ya ce: “Ku tashi ku bani guri, bai kamata ayi jayayya a gabana ba” me ake nufi da wannan zancen?
Amsa a Dunkule
Wannan zancen yanki ne daga cikin hadisin kawo tawada da alkami ko takarda, wadda sassa biyu suka ruwaito (Shi’a da Sunna) a ruwayoyi daba-daban masu yawa; A wannan ruwayar akwai nuni ga abinda wasu sahabbai suka yi na nunu zaurin ido ga Fiyayyan Manzo (s.a.w) wanda Allah Ya suffan tashi da cewa “Baya furuci na son rai” Amma abin bakin cikin lokacin da ya yi umur da neman a binda zai yi wasiya da shi, sai wasu suka tuhumceshi da cewa sambatu ya ke yi. Annabi bai jure wannan cimmutuncin da zageranci da suka nuna ba. Don haka sai ya ce musu su fice daga gurinsa. “Ku tashi ku bani guri bai kamata a yi jayayya a gabana”.
Amsa Dalla-dalla
Wannan zancen yanki ne daga cikin hadisin (mai taken) kawo tawada da alkami ko takarda, wadda bangare biyu suka ruwaito (Shi’a da Sunna) a ruwayoyi daban-daban masu yawa. Buhari ya ruwaito labarin a wurare shida, Muslim ya kawo a wurare uku. Zamu kawo hadisin a ruwayar Buhari ta han’yo’yi daban-daban:
 1. Kabisata ya ba mu labara daga Ibin Unainata daga Sulaiman Ahwal daga Sa’id bin Jubairu; ya ce: Ibin Abbas ya ce: “Kaico ranar Alhamis kenan. Ka kuwa san ran Alhamis? ! Sai ya fashe da kuka yana ta yi sai da gemanyarsa ta jike. Sai ya ce: “Rashin lafiya ya tsananta ga Manzon Allah (s.a.w) a ran Alhamis din ya ce: “Ku kawo mun abin rubutu in rubuta muku wani littafi da in kun yi riko da shi ba zaku bace a bayana ba, har abada. Amma sai zuka yi jayayya, alhali bai kamata a yi jayayya a gaban wani annabi ba. Sai suka ce: “Ai Annabin Allan (s.a.w) sabmatu yake. Sai ya ce: Ku kyaleni halin da nake ciki yafi abinda ku ke dangantani da shi”[1]
 2. Kutaiba ya ba mu labari daga Sufyanu daga Sulaiman Ahwal daga Sa’id Bin Jubairu; ya ce: Ibin Abbas ya ce: “Kaico ranar Alhamis. Ka kuwa san ran Alhamis? ! Sai ya fashe da kuka ya na ta yi har sai da gemanyarsa ta jike. Sannan ya ce: “Rashin lafiya ya tsananta ga Manzon Allah (s.a.w) a ran Alhamis din sai ya ce: “Ku kawo mun abin rubutu in rubuta muku wani littafi da in kun yi riko da shi ba zaku bace a bayana ba har abada. Amma sai zuka yi jayayya, alhali bai kamata a yi jayayya a gaban wani annabi ba. Suka ce: “Shin sambatu yake yi ne? Suna tambayarsa. Sai suka rika kai-kowo a kansa. Sai ya ce: “Ku kyaleni halin da nake ciki yafi abinda ku ke dangantani da shi”[2]
 3. Ibrahim bin Musa ya bamu labara, Hisham ya bamu labara daga Mu’ammar, kuma Abdullahi bin Muhammad ma ya bani labara Abdurazak ya bamu labara Mu’ammar ya bamu labara daga Zuhuri daga Ubaidullahi dan Abdullahi daga Ibin Abbas (RA) ya ce: “Yayin da Annabi (s.a.w) ya zo gargara, a cikin gidan akwai wasu muta ne, cikinsu akwai Umar dan Haddabi. Sai Annabi ya ce: “Ku kawo mun abin rubutu in rubuta muku wani littafi da in kun yi riko da shi ba zaku bace a bayansa ba har abada” Sai Umar ya ce: “Hakika ciwa ya tsananta ga Annabi (s.a.w) ai kuna da Alkura’ani; littafin Allah!! Sai mutanen da ke cikin gidan suka yi ta hayaniya, akwai masu cewa ku mika wa Annabi (s.a.w) ya ya rubuta muku littafin da ba zaku bace ba a bayansa ba, kana a cikinsu a kwai mai fadin abinda Umar ya fada!! A yayin da suka yawaita hargowa da sabani gaban Annabi (s.a.w) sai Manzon Allan (s.a.w) ya ce; “Ku tashi ku fice”. Ubaidullahi ya ce: “Ibin Abbas ya kan ce baban abin bakin ciki shi ne hana Manzon Allah (s.a.w) ya rubuta musu wannan takardar saboda sabaninsu da hayaniyarsu”[3]
Wannan shi ne tawaye da wasu musulmi su ka yi a gaban Manzon Allah (s.a.w), ba wai sun takaita da yi masa tawayen kin kawo tawada da alkalami ba kawai, saida suka masa tsaurin ido batare da la’akari da girman matsayinsa ba (s.a.w) har suka furta zantuttuka na cin zarafi. Da hakan ya tsananta ga Annabin Girma (s.a.w) ya uzzura masa, sai ya dauki mataki don dakatar da wannan cin zarafin da tsagerancin da wasu suka yi. Hakika ruwayoyi sun fayyace martani iri biyu da annabi (s.a.w) ya nuna:
 1.  Da ya ce: “Ku tashi ku fice” ai bai kamata a yi jayayya a gabana ba”[4]. Wannan ya nuna matukar bacin rai da ya samu Annabi (s.a.w) sanadiyar mummunan kalamansu da cin zarafi ga matsayinsa na Annabi Maigirma (s.a.w).
 2. Sai a sanda jayayya ta tsananta da husuma tsakanisu suka fadi abinda suka fada na kazaman kalmomi sai Annabi ya umurce su da su fice ya ce: “Ku kyaleni halin da nake ciki yafi abinda ku ke dangantani da shi”[5]
A takowace fuska dai zancen Annabi (s.a.w) a bayyane yake, ya bayyana wa al’umma aikinda ya kamta su yi a dukkanin wadanan matakan. Daga ciki a kwai mataki na Imamanci da bayyana wanene halifa, saboda shi (s.a.w) ya yi ta ishara a wurare da dama ya na nunnuna Imam Ali (a.s). Sai dai a wannan lokacin Annabi (s.a.w) ya ga wasu mutane awamman fafatawar da suke yin tirjiya da bijire wa umrnin Annabi (s.a.w) da nufin hana hakan ta yiwu a ta hanyar datse umurnin koda hakan zai shafi jigon annabta ya kuma shafi wanda Alkur’ani ya masa kirari da cewa: “Baya furuci bisa son rai” Sai aka rika cewa ya na sambatu ne ko rashin lafiya da sauransu. A nan ne fa (s.a.w) ya katse musu hanzari na wannan cin zarafin, inda ya kori yan tsageran daga gurin. Don karin bayani sai ka dubi:
 

[1] Sahihul Bukhari j3, sh 111, sh 2888 wanda ya rubuta shi ne Muhammadu bin Isma’il Abu Abdullah Albukhari, ya yi wafati 256H, bugun Daru Ibin Kasir, Berut 1407. 1987. bugu na uku tahakikin Dr. Mustapha Dabulfa’a.
[2] Sahihul Bukhari j 4, sh1612 sh 4158.
[3] Sahihul Bukhari j 5, sh 2146, sh5345, babu kaulil maridi kumu anni.
[4] Sahihl Bukhari, j 4, sh 16246, sh 4168, babu kaulil maridi kumu anni.
[5] Sahihil Bukhari j4, sh16246, sh 4168, babu kaulil maridi kumu anni. J 4, sh 1612, Sahihul Bukhari j 3,sh 1111 sharhi na 2888 wanda ya rubuta shi ne Muhammadu bin Isma’il Abu Abdullah Albukhari ya yi wafati 256H, bugun Daru Ibin Kasir, Berut 1407. 1987. bugu na uku takikin Dr. Mustapha Dabulfa’a
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
  4655 انسان شناسی
  Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...
 • Shin Ammar Dan Yasir ya temaka wa Imam Ali (a.s) kan lamarin da ya faru a SaKifa ko kuwa?
  1169 سقیفه بنی ساعده
  Mutane da dama sun tafi kan cewa Imam Ali shi ne shugabansu, amma yanayin yanda suke yi masa biyayya kuma suka sallam masa ya banbanta, babu tantama tun a farko Ammar ya kasance matemaki kuma mabiyu wanda ya sallamawa imama Ali (a.s) duk da cewa ta yiyu ...
 • Me ake nufi da hadisi rafa’i
  9961 مبانی فقهی و اصولی
  An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
 • SHIN WAJIBI NE A JI TSORON ALLAH KO KUMA A SO SHI?
  11386 محبت و دوستی
  Gwamuwar jin tsoron Allah da kaunarsa, a wasu lokutan kuma kaunarsa kawai, dangane da Allah ba wani al’amari ba ne da yake bako, domin shi ya cika dukkanin bangarorin rayuwarmu, amma saboda tsananin bayyanarsa sai mu din muka rafkana da shi. Mu sani cewa har ...
 • A lokacin da hura wa Annabi Adam (a.s) rai me ya fara cewa?
  1774 Hdisi
  An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
 • Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
  1843
  Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
 • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
  4799 پیشینه تاریخی ولایت فقیه
  Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
 • duk da cewa mace zata iya shiga cikin majalissar kwararru ta zaben shugaba, shin zakuma ta iya zama shugaba?
  4346 نهادهای حکومت دینی
  Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake ...
 • Shin zama hannu rabbana daga kan ruwayoyi tare da wadatuwa da al kur’ani mai girma ya isa hadin kai wajan al ummar musulmai?
  1340 Dirayar Hadisi
  Wannan magana ko kuma muce wannan bangare bawai sabon bangare bane, asalinsa ya faro tun daga karshen rayuwar Manzo (s.a.w) inda wasu daga alamomin wadannan mutane ya bayyana, daga masu tunani kan mganar cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu riko” ta farune tun daga lokacin da Manzo ...
 • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
  9496 Halayen Aiki
  Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...

Mafi Dubawa