advanced Search
Dubawa
6778
Ranar Isar da Sako: 2006/05/31
Takaitacciyar Tambaya
Shin yawan masu karkata daga addini tana nuna lalacewar mahangar nan ce ta cewa akwai dabi'ar halittar karkata zuwa ga addini ga mutum?
SWALI
Yayin da muke duba wannan duniyar baki daya zamu ga mafi yawan mutane suna da karkata daga addini, ko ma sun gama karkacewa zuwa ga fasadi da bata da son kecewa da holewa, sun zabi hanyar faduwa da kama hanyar wuta, wannan karkatar ta al'umma mai girma ba ta dace ba ta kowane hali da mahangar nan ta addini mai cewa jin cewa akwai addini da Allah da karkata zuwa ga kadaita Allah da ayyuka na gari da cewa dabi'a ce ta halittar dan'adam da aka kimsa masa a halittarsa, kuma da haka ne don me ya sanya zamu ga wannan lalacewa da daidaicewa da karkacewa zuwa ga kyamar addini da rashin sanya addini cikin rauwar al'umma da muka ga shi ne ya yi kamari kuma yake tafiyar da mafi yawan kasahen duniya a dokance, don haka shin ba zai yiwu mu ce karkata ga addini ba wani abu ne na daib'ar halittar dan'adam ba, kuma mutum ya fada cikin fasadi ne da karkacewa da mugwayen halaye bisa dabi'ar halittar zatinsa domin shi abin halitta ne mai munin zati?
Amsa a Dunkule

An halicci mutum yana kan karkata zuwa ga riko da addini, kuma mafi yawan mutane sun amsa wannan kira, mutum a bisa zatin dabi'ar halittarsa yana kokarin fuskanta ne zuwa ga gaskiya da son hakika, sai dai yana fada wa kuskure ne a tsakiyar tafiya.

A bisa hakika da gaskiya akwai wasu abubuwa daga waje da cikin samuwarsa da suke sanya mutum ya samu karkacewa da rashin fuskantar gaskiya ne, daga cikinsu akwai shedan, da ran mutum mai umarni da mummuna ta wata fuskar, ta wata fuskar kuwa akwai kafafen sanarwa da yada labaru da kalle-kalle masu halakarwa da lalatarwa, kuma dukkan wadannan abubuwan suna kokarin su ga sun kange mutum ne daga gaskiya da samun shiriya. Rashin yarda da addini a rayuwar mutum da nisantar da shi daga siyasa da zaman al'umma duk yana daga cikin abin da yake na kuskure da coci-coci suka yi yayin da suka nuna addini da mummunar kama matuka. Kai sun nuna addini da yanayin da ya saba wa tunani da dabi'ar halitta ta gari, wannan lamarin ne kuma ya san aka samu damar wannan karkacewar ta fuskacin coci a matsayin wata dama da masu gaba da ita suka samu domn kawar da addini daga siyasa da zaman rayuwar al'umma, ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai da hanyoyin isar da sako da koyarwa, wannan lamarin kuwa ya kai ga samun karkacewa mafi yawan al'umma a yammacin duniya, sai dai wannan lamarin bai iya gamawa da jin nan nan addini da yake cikin zatin dabi'ar mutane ba, yayin da zamu ga mafi yawan mutane suna riko da wannan shu'urin da suke ji, kuma da wannan ne zai bayyana cewa ba daidai ba ne a ce mafi yawan mutane 'yan jahannama ne!!. domin su suna masu rayuwar addini da wannan jin na halitta, sai dai su yayin da suke motsawa ne don neman gaskiya sai su fada cikin kuskure saboda ba zasu iya gano gaskiya ba, su sun samu takaituwa ne ba takaitawa ba, don haka su masu jahilci ne na takaituwa ba na takaitawa ba, don haka suna da nasu uzuri.

Amsa Dalla-dalla

An halicci mutum yana mai dauke da halittar son karkata da riko ga addini da son kyawawan halaye, kuam mafi yawan mutane sun amsa wannan krain halittar, sun amsa wa jin riko da addini da yake tare da su, kuma malaman musulmi bisa biyayya ga kur'ani mai girma da ruwayoyi madaukaka sun yi nuni da wannan lamarin, sai dai wannan ba ya hana mutum fadawa cikin farfagandar da ake watsawa wacce take kira da kin addini da watsi da kyawawan halaye, wannan ne yakan sanya mutum karkacewa daga tafarkin gaskiya wani jikon wanda yakan kai mutum ga karkacewa wuirn zabar gaskiya a yayin dabbaka wannan karkata zuwa ga addini a zahiri. Da za a samu kawar da wannan shamakin da ya rufe gaskiya, wanda zai kawar da wannan farfagandar kafofin sadarwa da isar da sako, aka kawo gaskiya kamar yadda take ga mutane, da an samu mutane suna karkata kai tsaye zuwa ga gaskiya.

Don haka za a iya cewa: mafi yawan muatnen ba sa karkata zuwa ga fasadi da kin gaskiya, domin sun fada karkashin farfaganda ne mai kiyayya ga gaskiay, sun yaudaru da tunanin karkata mai gaba da addini, sai suka fada cikin munanan halaye maimakon su samu gaskiya, kuam sai suka rudu da aikin shedan da waswasinsa da rai mai umarni da mummunan aiki.

A wannan zamanin an samu mummuan jita-jita da yada farfagandar karya ta kyama da kin addini, da kuam yada kin kyawawan halaye musamman a tsakiyar karni na ishirin , kuma coci coci sun taimaka wurin samar da wannan yanayin ta hanyar  nuna addini da wata sura mummuna ta hanayr zartar da dokoki da suka haifar da hakan game da addini da riko da addini, sai aka samu kyamar addini saboda munanan halayen malaman coci coci da kuma kawo dokokin da suke saba wa hankali da addinin kansa, sai dukkan wannan ya taimaka wa tunanin kin addini da guje masa da aka fi sani da Ulmaniyya ta samu kasuwar baje kulen ta da samun masu saya da cinikayya, amma duk da haka wannan ulmaniyya ba ta iya gamawa da tunanin riko da addini ba, kuma ta bayar da iyakacin kokarin ta kan hakan amma wannan dabi'ar halitta ta ci gaba da samuwa ga mutum.

Muna iya ganin abin da ya samu dan Adam a tsawon wannan lokacin da sunan kwaminisanci da abin da al'umma ta samu na kiyayya da gaba da tsanani da zalunci da danniya da kisa mai tsanani don kawai ta bar addini da kyawawan halaye, amma duk da haka masu karfi da iko ba su iya galaba kan wannan halittar ta son karkakata zuwa ga addini ba.

Sai ma muka ga bayan rushewar tarayya  sobiyot mutane sun koma wa dabi'ar halittarsu sai fulawar addini ta  sake budewa, wannan kuwa ba don komai ba, sai albarkacin wannan halittar da suke dauke da ita ta son karkata zuwa ga addini da Allah ya halicce su da ita.

Amma batun cewa mafi yawan mutane 'yan wuta ne wannan magana ce ba sahihiya ba, kuma ba ta doru bisa ilimi ba, sai dai mafi yawan mutane zasu kai ga aljanna ne, wannan kuwa domin musulunci ya kasa mutane gida biyu, bangare na farko su ne masu kin gaskiya bayan sun gane ta, sai suak yi gaba da ita don kin gaskiya, da kuma wasu jama'ar da su sun jahicli gaskiya ne, kuma suna son su kai gare ta, sai dai su a aikace sai su fada cikin kuskure, to musulunci ya bambanta tsakanin wadannan jama'o'I guda biyu.

Don haka ne yayin da musulunci yake sanya iyaka tsakanin akida ta gaskiay wacce manzon Allah (s.a.w) ya yi kira zuwa gare ta ya yada ta, da kuma akidar bata da mabiya shedan suke yadawa, sai dai yana da wani tausasawa ga masu jahilci wadanda suka takaitu ba suka takaita ba, domin wanda yake cancantar azabar Allah a mahangar musulunci shi ne wanda yake ya takaita ba wanda ya takaitu ba, wato su ne wadnda sako ya zo musu suka fahimce shi, suka gane shi, amma sai suka ki shi suka yi gaba da shi. Amma wanda sako bai zo masa ba, ko kuma ya zo masa amma a jirkice da jirwaye, sai suka yi riko da addininsu da aiki da gaskiya bisa akidarmu, to wadannan suna daga masu tsira.

A bisa gaskiya idan muka duba badinin samuwa muak nisanci zahiri, to zamu samu mafi yawan mutane suna karkata zuwa ga addini ne, kuam su zasu kasance daga mutanen aljanna daga karshe, ko da kuwa sun yi kuskure wurin dabbaka wannan tunanin nasu, wannan duk ba ya hana su amam samun azaba a kabari ko kuma a lahira , sai dai muhimmi shi ne daga karshe zasu samu zuwa da komawa zuwa ga aljanna, don haka masu dawwama a wuta su ne wadanda suka lalata fidirar halittarsu suka lalata halittar nan ta karkata a addini.

1- don karin bayani a duba littafin: fidira na shahid allama mutahhari, intisharat sadra, da kuma tafsirul maudhu'I alfitira fil kur'an, na sheikh jawadi amuli.

2- abin da ake nufi da kafiri a nan cewa wanda ya yi musu asasin addini ko wani laruri nasa, don haka ya hada dauk wani kafiri mai shisshigi da mai jahilici, sai dai mai shisshigi shi ne wanda ya ya yi musun ilmi da gaskiya da gangan, amma kafiri jahili shi ne wanda ya yi musu bisa jahilci ta yadda da ake gaya wa wanda ya yi musu bisa jahilci, wanda da ya gane gaskiya da ya karkata zuwa gare ta.

3- adalcin Allah na shahid mutahhari, kisimi na takwas, s 319 – 427, da kuma shafi na 424 – 427, a bayani mai taken ; khulasa wa natija.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Wane addini ne Cikamakon Addinai?
  4125 Sabon Kalam
  Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo. Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda ...
 • me ya sa Allah madaukaki ya bayyana mata da cewa su wasu halittune da suke girma cikin kawa?
  5555 زن
  Ayar da ta zo cikin tambaya, tana bayani ne a kan tunani da akida na kafiran jahiliya da suke cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. Allah madaukaki a cikin wadannan ayoyin ya yi amfani da dalillai wadan da kafirai suka yadda da su domin ya nu na ...
 • Menene hukuncin miji da mata wadanda suke kallon fim din blue fim a tare?
  1378
  an tambayi daftrorin marja’ai masu alfarma kan tambayar da ka yi kuma ga amsar da suka turo. Ofishin mai girma Ayatullah sayyid Ali Khamna’i (Allah ya tsawaita rayuwarsa): Kalllon finafinai masu tada sha’awa na sa mutun ya karkata zuwa tafarkin shedan na son zuciya kuma yana raunana ...
 • wanene mu”azu dan jabal?
  2528 برخی صحابیان
  Mu”azu dan jabal dan amru dan ausu dan a”izu, ane masa alukunya da baban Abdurrahman, sannan ya na daga cikin mataimakan manzon Allah {s.a.w}.[1] mu”azu dan jabal tare da mutane 70 na daga cikin wadanda sukai mubaya”mar akaba sannan suka yi tarayya cikin yakoki ...
 • menene abin sha mai tsarkakewa?
  12520 شراب طهور
  "Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
 • Ta fuskacin abin da ya zo a tarihi akwai bayanin faduwar hukumomi da dauloli wata rana, to shin wannan dokar tarihin ta shafi hukumar Imam mahadi (a.s) ko kuwa?
  4491 بعد از ظهور
  Wannan lamarin ba zai yiwu ba ga hukumar duniya ta Imam Mahadi (a.s) saboda dalilin faduwar wadancan hukumomin yana komawa zuwa ga zaluncin wadannan hukumomin ko kaucewarsu ga asasin adalci, ko kuma saboda yaudarar mutane ta hanyoyin isar da sako wacce ta haifar da bambanci tsakanin mutane ...
 • shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka Daular Safawiyawa, kana mai yaba wa mahukuntanta?
  4196 شخصیت های شیعی
  Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da ...
 • Me ake nufi da hadisi rafa’i
  9569 مبانی فقهی و اصولی
  An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
 • Ta yaya Mutum zai iya samun ikon fassara Mafarki?
  25028 خواب
  Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
 • Saboda Allah madaukaki ya fada a hadisin kudsi cewa: duk wanda na kashe shi, to ni ne diyyarsa?
  10115 انسان و خدا
  Bayanin da aka ambata shi wani bangare ne na hadisin kudsi da aka sani da ya zo kamar haka: “Duk wanda ya neme ni zai same ni, wnadaya same ni ya san ni, wanda kuwa ya san ni ya so ni, wanda ya so ya yi bege ...

Mafi Dubawa