advanced Search
Dubawa
16273
Ranar Isar da Sako: 2009/01/24
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne iyakancin suturar mace gaban muharraminta, kuma mene ne gwargwadon abin da ya halatta ga namiji ya gani a jikin muharramarsa?
SWALI
Mene ne gwargwadon abin ya halatta dan’uwan uwa ya gani ga jikin ‘yar ‘yar’uwarsa? Wato; mene ne gwargwadon abin da ya halatta ga yarinya ta bude shi na jikinta ba sai ta rufe shi a gaban dan’uwan babarta ba?
Amsa a Dunkule

Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba to babu komai. Haka nan kallon fuska da jiki da gashin yarinya da ba ta balaga ba idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba, kuma babu wani tsoron fadawa cikin haram, to babu komai gareshi, sai dai bai kamata ya kalli wuraren da bisa al’ada ana rufe su ba, kamar cinya, da ciki, bisa ihtiyadi[1].

Amma kallon namiji ga jikin mace muharram, idan ya kasance ba da nufin jin dadi ba, to babu komai, sai dai ban da al’aura biyu. Sai dai kawai miji shi ne ya halatta ya kalli dukkan jikin matarsa da nufin jin dadi.

Imam khomain (k.s) yana fada a game da haka cewa: “Ya halatta ga namiji da mace muharramai su kalli jikin junansu da kallon dukkan jikin juna in bada al’aura idan ba da nufin jin dadi ba”, don haka ya halatta ga dan’uwan uwa ya kalli dukkan jikin matan da suke haramun gareshi in ban da al’aura, ba da nufin jin dadi ba[2].

Kuma bai wajaba kan mace ba ta rufe jikinta gaban muharrami, sai dai bai halatta ga namiji ba ya kalli kowane wuri ne a jikin muharramarsa da nufin jin dadi[3]. Idan kuna son karin bayani sosai to sai ku koma wa wadannan shafukan:

1- Maudu’i: Da’iratu Hijabil Mar’a, tambaya 1759 (Shafin Intanet: 2327).

2- Maudu’i: Satruz Zufri, was sha’aril must’ar an gairil muharram, tambaya 3663 (Shafin Intanet: 2923).

 


[1] Taudhihul Masa’il: Mai Hashiyyar Imam Khomain, j 2, s: 485, mas’ala: 2433.

[2] Taudhihul Masa’il: Mai Hashiyyar Imam Khomain, j 2, s: 489, mas’ala: 2437.

[3] Ya kamata a kiyaye janibin halaye na gari a cikin irin wadannan lamurran, abin da aka fada hukuncin fikihu ne kawai.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Mene ne hukuncin wasa da tsintsaye a musulunci?
  5167 نگهداری و شکار حیوانات 2012/07/25
  Shi wasan a kan kansa ba haramun ba ne, sai dai idan yakan cutar da mutanen da ke kusa ko na nesa kamar makoci yakan samu hukunci daban kamar yadda malamai masana tunanin dan Adam suka fada cewa ya kamata gare shi ya kula sosai da irin ...
 • Yaya zan tuba daga kallon film mai batsa?
  13531 توبه 2014/02/12
  Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
 • Ni saurayi ne kuma a yanzu ina da bukatuwar in san mene ne rayuwa da hadafinta.
  9305 هدف از آفرینش 2012/07/25
  Akwai nassoshi masu yawa da suka zo a cikin koyarwa da dokokin musulunci wadanda suke nuni da hadafin rayuwa da cikakkiyar manufarta. shi Kur’ani Mai girma yana daukar cewa manufar rayuwa ita ce: “bautar Allah madaukakin Sarki, wadda ta hanyarta ce za a iya isa ga kamaloli ...
 • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
  4058 پیشینه تاریخی ولایت فقیه 2012/07/24
  Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
 • Meye matsayin jagorancin malami a tsarin siyasar musulunci?
  3885 کلیات 2012/07/24
  A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance ...
 • Menene ma’anar Kalmar tarjama da ma’anar Kalmar tafsir kuma menene banbancin da ke tsakninsu?
  1223 Ilimin Kur'ani 2019/06/16
  A wajen malaman lugga: T R J M, wadannan nan ne bakaken da suka hada Kalmar tarjama, wato jam’in (tarjiman) shi ne wanda yake yin tarjama, yake fassara magana, ana cewa wane ya tarjama maganar wani: ma’ana ya bayyana shi ya fayyace shi, haka ma, wane ya ...
 • Mene ne hukuncin sallar mamaci a fikihun Ja’afariyya? Kuma yaya ake yin ta?
  482 نماز میت 2019/06/15
  Amsar malaman Shi'a game da wannan tambaya yana kamar haka ne: 1. Yin salla ga mamaci musulmi ko yaron da yake da hukuncin musulunci[1] da ya kai shekara shida, wajibi ce[2]. 2. Sallar mamaci kabbarori biyar ce ...
 • A kawo hadisan da suka yi haramta rawa da kuma madogararsu.
  7121 بیشتر بدانیم 2013/08/15
  Kafin mu ba da amsar wannan tambayar ya kamata mu lura da wani abu guda mai muhimmanci kamar haka, dan an samu ruwaya daya a cikin litattafan ruwayoyi bai wadata ba wajan kafa dalili da ita ruwayar. Domin kafa dalili da ruwaya wani abu ne da ya ...
 • shin labarin da ake cewa annabi ba ya barci har sai ya dora kansa a kan kirjin fatima ya inganta?
  27273 عزیزترین فرزند پیامبر ص 2012/07/24
  kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
 • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
  8667 معاد و قیامت 2012/11/21
  Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...

Mafi Dubawa