advanced Search
Dubawa
7593
Ranar Isar da Sako: 2006/05/31
Takaitacciyar Tambaya
Ta fuskacin abin da ya zo a tarihi akwai bayanin faduwar hukumomi da dauloli wata rana, to shin wannan dokar tarihin ta shafi hukumar Imam mahadi (a.s) ko kuwa?
SWALI
Ta fuskacin abin da ya zo a tarihi akwai bayanin faduwar hukumomi da dauloli wata rana, to shin wannan dokar tarihin ta shafi hukumar Imam mahadi (a.s) ko kuwa?
Amsa a Dunkule

Wannan lamarin ba zai yiwu ba ga hukumar duniya ta Imam Mahadi (a.s) saboda dalilin faduwar wadancan hukumomin yana komawa zuwa ga zaluncin wadannan hukumomin ko kaucewarsu ga asasin adalci, ko kuma saboda yaudarar mutane ta hanyoyin isar da sako wacce ta haifar da bambanci tsakanin mutane da hukumarsu, wadannan abubuwan dukkaninsu ba zasu yiwu ba ga hukumar lokacin Imam Mahadi (a.s) ta duniya.

Amsa Dalla-dalla

Faduwar hukumomi da rushewarsu yana yiwuwa ta fuskoki biyu ne:

a) Gushewar jiga-jigan hukuma yana kasancewa saboda zalunci da danniya da tatsiya wacce masu hukuma  a hannu suke yi ne, da ninsantar su daga hanyar kwarai da adalci sakamakon karkacewa, ko kuma sakamakon juyin al’umma da kawar da hukumomi, ko kuma saboda kasa ta samu harin wasu daga waje suka kayar da hukuma, don haka ne zamu ga mafi yawan dauloli da suka fadi a tarihi sun samu irin wadannan dalilai ne. Misailn abin da ya kawar da daular Umayyawa a hannun Abbasawa zamu ga zalunci ne da rashin adalci da ya bayyana karara a lokacin daular umayyawa.

 Ko kuma faduwar daular abbasawa a hannun Magol, ko sasanawa a Iran wacce ta fadi ta rushe saboda yakin nan na harin sojojin musulmi, wannan kuwa saboda zalunci da tatsiya da ya kai ga hatta da al’umma ta ki taimaka wa wannan hukumar saboda rashin dogaron al’umma, don haka sai al’umma ta ki taimaka mata da kare ta, kai al’umma ta kasance tana zaune cikin hakuri ne tana jiran wanda zai zo ya tseratar da ita daga dannniyar azzalumai ne ma. Haka nan ma lamarin yake game da tsarin shahin shahinci yayin da ya fadi a hannun al’ummar da ta kasance tana tsananin kishin adalci da samun ‘yanci da ‘yantuwa, bisa jagorancin marigayi jagora Imam Khomain (k.s).

Don haka ne sai muka samu hukumomi azzalumai sun fadi ta daya daga wadannan hanyoyin; imma dai ta hannun juyin al’umma ko kuma ta hanyar yakin masu hari daga waje da rushewar masu kariyar cikin gida.

b) Na biyu daga abin da yake kai wa ga faduwar hukuma shi ne yaudarar al’umma da fadar da su ta hanyar isar da jita-jita da watsa labaran karya har sai hukuma ta rusu, kamar yadda aka jarrabi hukumar Imam Ali (a.s) da wannan yakin na yada jita-jita da karerayi da makiya masu gaba da Imam Ali (a.s) suka rika yadawa, hada da yaki da hare-haren da makiya suka tilasta masa a wannan zamanin wanda ya kai ga cire wa al’umma tunani da lura da hankali cikin lamurran da suke kaiwa su komo, hada da cewa Imam Ali (a.s) kansa bai yarda da abin da ya faru na karbar sha’anin hukuma wanda ya gabata kafin zuwansa ba, ta yadda mafi yawan jagororin al’umma da zabubbun mutanen al’umma sun samu karkacewa daga adalci, sun karkace daga hanyar, sun samu ruduwa da duniya, lamarin da ya sanya aikin kawo canji da gyara da tsayar da adalci da fuskantar wadanda suka zama a saman jagorancin al’umam (da suka karkace daga karkarta ya zama abu mai wuyar gaske) har wannan kokarin canjin ya haifar da matsaloli da wahaloli da bala’o’i masu yawa da tayar da fitina don yakar Imam (a.s). Sannan a sakamakon duk wadannan abubuwan da aka kawo na tsanani da tsanantawa sai ya kasance al’umma ta kasa gane hakikanin gaskiya, sai ta ki daukar mataki mai karfi ga wannan gabar da yakin jita-jita[1], wanda daga karshe ya kai ga shahadar Imam Ali (a.s) da kawo karshen hukumarsa.

Amma idan mun duba hukumar duniya ta Imam mahadi Allah ya gaggauta bayyanarsa, zamu ga babu abin da yake kawar da hukumomi ya kayar da su na farko tabbas.

Haka nan abu na biyu shi ma babu shi, domin a wannan zamanin mutane zasu kai kololuwar samun wayewa da hankali da tunani, da samun matukar fahimta da wayewar da sanin makamar siyasa, kamar yadda hukumarsa zata kasance ta kame lamarin isar da sako da shiryarwa, da  gudanar da hukuncin musulunci, da aiwatar da dukkan abubuwan alheri na musulunci kamar umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna, don haka sai a rasa wani sabani tsakanin al’umma da hukumar Imam mahadi (a.s), daga karshe sai dalilin rushewar hukuma na biyu ya kawu ke nan.

Sai dai shedan zai wanzu yana mai kulle-kulle, yana yi wa mabiyansa waswasi masu biyayya ga tafarkinsa, kuma yana samun damar yaudarar wasu, sai dai galibin mutane zasu kasance ba su karkata ba, suna masu watsar da wasa da hankali da shedan yake yi da makircinsa[2].

 


[1] Dr. Sayyid Mukaddam Shahidi, Ali (a.s) a harshen Ali (a.s), ko kuma rayuwar Imam Ali na ofishin al’adun musulunci, 1379 H.Sh, shafi: 64 – 160.

[2] Duba Littafin “Mahdiye inkilabe buzurg” na Nasir Makarim Shirazi, da Ibrahim Amini, Dadgustare Jehan. Domn samun karin bayani.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

  • shin labarin da ake cewa annabi ba ya barci har sai ya dora kansa a kan kirjin fatima ya inganta?
    50213 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
  • Yaya zan tuba daga kallon film mai batsa?
    42714 Halayen Nazari 2014/02/12
    Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
  • shin mutanen da suke rayuwa a cikin koguna danganensu na komawa zuwa annabi Adam kuwa?
    11212 Tafsiri 2012/07/25
    Hakika zabar koguna da duwatsu domin rayuwa ga tsatson Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi lamari ne da alkur'ani ya tabbatar da shi, amma dangane da abin da ya shafi mutanen da suka gabaci Adam amincinAllah ya tabbata a gare shi, akwai abubuwa masu yawa ...
  • Me ye alaka tsakanin Zuhudu da ci gaban zamani?
    10375 Halayen Nazari 2012/07/24
    Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin ...
  • DOMME AKE WA KA’ABA RIGA DA YADI MAI BAKIN LAUNI KAWAI?
    10896 Sirar Manya 2012/07/26
    Ana kiran wannan bakin kyalle da ake rufe Ka’aba da shi a wannan zamani da suna suturar Ka’aba ko rigar Ka’aba. A wannan zamani ne ake wa Ka’aba rika da bakin yadi, da aka yi masa zayyanar ayoyin Kur’ani da aka saka da launin ruwan gwal. Amma ...
  • Yaya asalin mutum yake?
    20886 Tafsiri 2012/07/25
    Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
  • Shin akwai wani bayani da ya zo game da hadisin kisa’I a cikin littafin Muslim kuwa? Idan dai haka ne to juzu’I na nawa ne, shafi na nawa?
    3498 2019/06/15
    Hadisin Kisa’ ya zo a littafin Sahih Muslim, amma da dan wani bambanci da yadda ya zo a littattafan Shi”a, a littafin Muslim ya zo ne kamar haka: حَدَّثَنَا أَبُو بَکرِ بْنُ أَبِی شَیبَةَ، وَ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللهِ بْنِ نُمَیرٍ – وَ اللَّفْظُ لِأَبِی بَکرٍ - ...
  • Shin addini ya zo ne don ya mayar da mu masu 'yanci ko kuma don ya dabaibaye mu?
    14874 Sabon Kalam 2012/09/16
    Zai yiwu mu fara bayani a kan al’amarin 'yanci ta hanyar bincike da karatu dangane da ra'ayin addini ta fage biyu: 'yanci na ma'ana da 'yanci na zamantakewa da siyasa. Hakikanin mutum idan mun danganta shi ga ma'ana mai nisa (mai zurfi) ita ce nafsin ko ruhin ...
  • Yaya aka samu tunanin akidar Rashin addini mai cewa siyasa daban take da addini?
    7311 Sabon Kalam 2012/07/24
    A lokacin samun canjin turan kiristoci sun samu matsala da ta kai su ga cewa addini yana da tawaya, kuma ba zai iya biyan bukatun mutane sababbi ba a fagen siyasa da zaman tare, don haka sai suka kai ga tunanin raba addini da siyasa.
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6014 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...

Mafi Dubawa