advanced Search
Dubawa
20963
Ranar Isar da Sako: 2007/05/03
Takaitacciyar Tambaya
minene sahihiyar fassarar jumlar {wadhiduhuna} ku buke su {wato ku buki matan ku} wadda ta zo a cikin ayar ta 34 ta cikin suratul nisa {karkatowa ko kuma jawo hankalin su ya zuwa rayuwa} ko kuma duka da ladaftar da mace?
SWALI
aya ta 34 a cikin suratul nisa na cewa; Maza, su ne suke dauke da nauyin mata sakamakon falalar da Allah ya yima wasun su akan wasu sakamakon taimakon da suke badawa na daga dukiyar su, da kuma mata salihai sune masu biyayya da kasgantar da kai kuma suna boye sirrin mazajen su alokacin da ba su nan.amma akwai wasu matayen da suke kin biyayya to kuyi masu gargadi da tsoratarwa in baiyi amfani ba to ku nisance su yayin kwanciya, in kuma bayyi amfani ba {wadhribuhunna} {ku karkato da su} idan suka amsa to kada ku zamu masu wuce gona da iri {wato matakin da ku ka dauka na nisantar kwanciya da su da kuma duka sai ku daina} ku sani Allah madaukakin sarki mai girma ne. Abun Lura A Cikin Wannan Ayar: Da farko ya kamata mu lura cewa ayar ba tana Magana da dukkan mutane ba ne, a takaita ne ga wasu ma’auratan, kuma dai ta takaita ga ma auratan da suke fuskanta matsalar zaman aure. Ko da yake da farko ayar na nuni da baki daya ne wato kowa da kowa {Maza, su ne suke dauke da nauyin mata sakamakon falalar da Allah ya yima wasun su akan wasu sakamakon taimakon da suke badawa na daga dukiyar su, da kuma mata salihai sune masu biyayya da kasgantar da kai kuma suna boye sirrin mazajen su alokacin da ba su nan}. Kalmar {qim} na daukar ma'anar wanda ke daukar nauyi tafiyar da lamuran wani, Kalmar {qawam} da kuma {qiyam} mubalaga ce a cikin qiyam. 1, saboda haka farkon ayar na tunatar da maza nauyin da ya doru kansu dangane da mata. {qiyam} daukar nauyi sun shafi dukiyar mata a cikin al'umma. kuma tana kiran mata ya zuwa ga biyayya ga maza da kuma rufe asirin da ya shafi gidajensu {mata na gari}. Acigaban ayar {.amma akwai wasu matayen da suke kin biyayya to kuyi masu gargadi da tsoratarwa in baiyi amfani ba to ku nisance su yayin kwanciya, in kuma bayyi amfani ba {wadhribuhunna} {ku karkato das u} idan suka amsa to kada ku zamu masu wuce gona da iri {wato matakin da ku ka dauka na nisantar kwanciya dasu da kuma duka sai ku daina} ku sani Allah madaukakin sarki mai girma ne. Acikin wanna ayar ana Magana ne da mazan dake jin tsoran rashin biyayyar matan su da saba masu cikin ummarni da kuma abunda ya shafi tafiyar da gida. Nushuz asalin Kalmar {nashaza} da ma'anar {kasa mai tutu} 2. Da kuma ma'anar kasar dake da tutu da gangara.amma ma'anar Kalmar a ciki mutane shi ne rashin biyayya da saba ummarni wanda ga ma aurata na nufin rashin fahimtar juna da rashin gamsuwa a cikin rayuwar yau da gobe da kuma abunda ya shafi alakar jima'I da rashin wadda da jima'I a yayin kwanciya. Acikin Kalmar {fa'azuhunna} wa'azzi sakamakon tsoro ne na nushuz 3. {rashin yadda ga kwanciya} ba shin kansa nushuz din ba. Saboda kur'ani maigirma ba yana nufin taurin kai da sabawa ba shi ne asalin mace ba shiyasa ya ce duk lokacin da suka sabo wato rashin amincewa to kuyi masu wa'azzi. Saboda haka ayar na isharane ga wadanda ke da tsoro a cikin lalacewar zamantakewa na gida, ahakika wannan ayar na Magana ne da namijin dake hangen rashin kula da kuma ko in kula a cikin rayuwar yau da gobe na aure ko kuma rashin alaga zuwa ga jima'I da matarsa ke nunawa saboda haka yana jin tsoron samun matsala a cikin rayuwarsu da gida. Mafiya yawancin irin wannan rayuwar dake tatare ma matsaloli da kuma rishin yadda mace wurin kwanciya da kuma tsoron dake tatare da miji daga garshe sakamakon karshe shi ne saki da rabuwa. Saboda haka domin kawo kyara cikin irin wannan rayuwar marar dadi da kuma kaucema sabanin da zai zo nan gaba. Da farko an bukaci muji day a tatauna da matarsa dangane da matsalolin da ke faruwa. Domin da hanyar tataunawane gaskiya zata baiyyanar masu su gane abunda ke kawo rashin fahimtar juna a tsakanin su. Ta hanyar tataunawane in akwai karanci rashin kulawa, ko rashin lafiya, ko matsalar dukiya za a'samu kyarawa ko kuma daukar matakin da yadace nan gaba. Tahanyar tataunawane za a fahimci cewa mace na da alagar ci gaba da zama da mujinta ko bata so. In bata da alagar cigaba da zama tabbas za a rabune. 4. wannan ayar na riga kafi ne a kan kada asamu rabuwa {wato saki}. amma idan mace ta nuna alaga da so ga mijinta da kuma abunda ya shafi tafiyar da gida da kuma dake wajan kiyaye tsarin tafiyar da gida, sai dai kuma bata da alaga wurin al'amarin jima'I, to gila tana fama da rashin lafiya ne. idan muka lura da ayar bata yi hukunci kai tsaye bag a matan dake kin yarda da mazan su wurin kwanciya kuma batayi nuni da azabar ubangiji ba akan su, domin kin yin hakan na nuni da yiyuwar samuwar rashin lafiya. Amma farko ayar tana gargadi ne ga miji a matsayin sa na namiji akan ya kiyaye da kuma daukar nauyin gida kuma nauyin matar sa {qawamuna alalnisa} saboda haka bai dace ba namiji ya rabu da matar sa don rashin lafiya ba. Sabboda haka kur'ani mai kirma ya kawo wata hanyar domin samun mafita shi ne bada iko baki daya hannun miji, akan ya nisanci wurin kwanciya da matar sa, yin hakan zai sa ya samu karfin zuciya domin ya yi galaba akkan tsoran dake tatare da shi ta wata fuskar ba mamaki sakamakon yin hakan {wato nisantar kwanciya} yasa matar ta nuna alaga wajen cigaba da rayuwa da kuma alaga zuwa ga jima'I. in kuma wannan matakin baiyi amfani ba, hanya ta ukku shi ne {wadhribuhunna} {wato ku buge su} wannan hanyar bayan an gwada hanyoyin biyu baa dace ba. 5. kamar yadda ya bayyana a baya cewa wannan ayar ta shafi wasu bangare ne na mutane kawai; A, ta shafi ma auranta da suke da matsala kawai, ba wai dukkan maza da mata ba ne ta shafa ba. b. ta shafi ma aurantan da macen ba ta kiyaye tsarin tafiyar da gida, saboda haka bata shafi ma auranta da suke da matsalolin da ba su shafi wannan ba. c. saboda haka wannan ayar na Magana ne da mutumin da matar sa bata lafiya wanda sakamakon hakan ne ta ke gujewa mijinta wurin kwanciya: 1, ko kuma namijin dake gujema tashin hankali amma kuma ya gaza ya kayo kyara a cikin matsalolin dake fuskarta gidan sa. 2, ko kuma amfani da tsanani da take hakin kansa ko na matar sa domin dawo da zaman lafiyar cikin gidan shi. Amma kur'ani mai girma a cikin ayoyi da dama yana hani ga tsanani da tashin hankali. Acikin wannan ayar yana cewa; kar ku wuce gonad a iri {wato take hakin juna} saboda wuce gona da iri shi kan shi nu'ine na zaluntar kai {6} saboda haka ana hani da shi. A bisa fadin kur'ani namiji da mace dole ne su tsaya kan gaskiya. Kuma dole ne ya zamo cikin halayen sub a cutar da juna: ba cuta ba cutarwa sai dai amfani da anfanarwa. Saboda haka indan kur'ani ya yi ummarni da aikata abu to abun ba zai sabama hankali ba domin ummarni kur'ani aiki ne da takalifi. {6} saboda haka ayar ba tana ba namiji ummarni dukan matar sa ba, kuma ba tana nufin take hakin mace ba ne.sai dai tana nu ni da nauyin da ya rataya akan miji da kuma kare hakin mace {qawamuna alnisa}. Kalmar {zaraba} {bugu} tazo da ma'anoni da dama a cikin kur'ani misali akace da musa ka bugi dutsi da sandar ka, wani wuri kuma tazo da ma'anar tafiye tafiye {kuyi tafiya} awani wurin kuma kuyi tafiya domin Allah, ko kuma da ma'anar buga tambari, an buga masu tambarin kaskanci, ko kuma da ma'anar buga misali haka ne Allah yake buga misali. Amma a cikin ayoyi biyu ya zo ne da ma'anar karkatowa; a cikin suratul baqara ayata 72, bayan anyi masu tuni akan wani wanda yai kisa kuma yake boyewa, cewa ku bugi matacen da kashin saniya sais u kayi hakan, sai Allah ya tayar da matacen. Acikin wannan ayar {zaraba} tazo ne da ma'anar duka a cikin suratul anfal aya ta 50 kuma.tazo da ma'anar karkatowa da nufin kyara rayuwa. Kuma a cikin suratul nisa aya ta 34. Saboda haka a cikin kur'ani Kalmar {zaraba} na da ma'ana goma sha hudu. In muka lura zamu ga cewa {zaraba} {wato duka} wani aiki ne wanda acikisa akwai wani hadafi wanda ake son cimmawa. Don haka a cikin wannan ayar {izribuhunna} {ku buge su} wane hadafi ne ake son cimmawa? In muka lura za mu ga cewa hadafi anan shi ne karkato da mace ya zuwa ga dadin rayuwa da kuma girmama hakokin ta {mace} da kuma hakokin mijinta {wannan shi ne asali a cikin kur'ani} amma inda manufar wannan Kalmar shi ne dukan mace da ladaftar da mace, to afili yake cewa an take hakkin mace ne da kuma hakkin namiji {6} wanda hakan ta sabama koyarwa ta kur'ani mai girma. Saboda haka manufa a cikin {wazribuhunnan} ku buge su} shi ne tayar da mace da kuma karkato da ita ya zuwa ga jin dadin rayuwa. Lokacin da ya zamo dalili duga shi ne dawo da mace zuwa ga rayuwa saboda haka ba za ace ma hakan tsanani ko kuma takurawa ba sai dai ya zamo wani nau'I na jayo hakali da karkatowa ya zuwa ga jindadin zamantakewa ta auratayya da kuma jin dadin jima'I a tsakanin ma'aurata. Sai ayar taci gaba da cewa; yayin da suka mika wuya to kar ku wuce gonad a iri wato alokacin da suka dai na kujema miji ayayin kwanciya {jima'i} suka dawo cikin biyyaya to namiji bai da hakin ya cigaba da matakin farko {wato karkato da ita} ba, saboda in ya cigaba da hakan to ya fita daga hadafi na farko wato karkatowa ya shiga wani abun daban wato tsanani da takurawa. Domin hadafi a cikin takurawa shi ne kaskantar da mutun kuma wannan hadafin ya sabama hakkin mace da namiji. Don haka takurawa a cikin gida ko ayayin kwanciya ya kamata ta zamo cikin soyayya da kuma nuna kyauna.in ta zamo hakan to ma'aurata zasu ji dadin auren su kuma suci gaba da rayuwa ta zaman lafiya ba tare da takurawa ba. Shin wannan fassarar ayar tayi dai dai? 1} tarjamar almizan suratul nisa aya ta 34 2} tafsirin namune suratul nisa aya ta 34 3} acigaban ayar ta 35 nisa akwai mahangar cewa kamar yanda ya zo a cikin ayar, {idan ku kaji tsoron rabuwa ko sabani a tsakanin ku, to ku dauko alkali daga bangaren miji da kuma bangaren mata domin suyi bincike a cikin lamarin, idan wadannan alkalan suna da nufin kyarane to Allah madaukakin sarki zai taimake su abisa abunda su ka yi nufi, saboda Allah masanine kuma yana da labara abisa niyar kowa. 5} akwai wani nau'I na rashin lafiyar ruhi {jindadi ayyukan wahala} irin wannan ciwon ya fi yawa a cikin al'ummar dake rayuwa cikin tsanani da wahala har takai ga suna ganin tsanani da wuya wani abune mai tsarki, kuma suna ganin takurama kai wani nau'ine na ibada suna ganin haka hanyace ta zuwa ga aljanna. Wasu masana ilimin kwakwalwa, suna ganin wahalar da mace ke sha yayin daukar ciki da tarbiyar yaro suna yin abune da jin dadi da kuma farin ciki wannan na daya daga cikin alamomin irin wannan ciwon amma wanda bai da hadari. Amma irin wannan ciwon ana samun shi cikin abunda ya shafi al'amari jima'I a bangaren mata. wanda suke bugata zuwa ga motsa su da tayar da hankalin su domin biyan bugata ta sha'awa wanda irin wannan motsarwar na iya kaiwa ga tagurawa ko duga wanda sakamakon hakan ba zai zo da kyau ba. 6} shishigi da wuce gona da iri a cikin al'amuran mutane a mahangar kur'ani zaluntar kai ne;misali wannan ayar na cewa a cikin tafsirin nawin suratul baqara aya ta 231; Ayayin da ku ka saki matayen ku kuma suka kai ranakun karshe na al'ada ko kun rike su ta kyakyawar hanya ko {kuyi sulhu} ko kuma kun rabu dasu ta hanyar da ta dace, ba kuma kun rige su bane domin cutarwa da take hakkin su, wanda ya aikata hakan {wato ya tsare su domin takurawa da cutarwa} to ya zalunci kan sa {domin aikata haka take dokokin Allah ne} shin kuna rigon ayoyin Allah ne da wasa ku tuna ni'imonin ubangiji zuwa ga re ku, da kuma littafi da ilimin da aka sauko maku daga sama muna tsoratar daku da shi kuma kuji tsoron ubangiji ku sani Allah masanine abisa komai {yasan wadan da suke take dokokin sa}.
Amsa a Dunkule

Dangane da fassara ko tafsirin jimlar {wadribuhunna} ta cikin aya ta 34 suratul nisa, karkatowa ko farkarwa. Dole ne mu ambaci cewa wannan fassarar ko tafsirin bayada tushe da sanadi na fassara, sai ma dai dalilai na lafazi da suke sabani da hakan.

1} Kalmar {zaraba} a cikin harshen larabci tana da ma'ana duka ne, kuma ma'anarta ta asali shi ne duka na jiki. Sai dai in akwai dalili na lafazi ko wani dalilin daban to za ta iya daukar wata ma'anar daban bat a duka ba. Kamar wannan ayar mai tsarki na cewa {sai muka buga masu misali} [1] saboda haka a cikin wannan ayar zamu fahimci cewa Kalmar misali da tazo tana nuni ne da buga misali ba wai bugun jiki ba. Kamar kuma wannan ayar {muka buga masu tabbarin kaskanci} [2] anan zamu fahimci buga tabbari ne {sitam} da dai ire iren wadannan misalai.

2} a cikin ayar {wadribuhunna} {ku buge su} afili yake ba bu wani dalilin lafazi wanda yake nuni da cewa ba ana nufin dukan jiki bane. Amma sai dai in anyi la'akari da karina wadda akayi amfani da ita domin a cikin ayar an fare ne da cewa kuyi masu wa'azi sai mataki na biyu ku nisance su sai mataki na ukku ku doke su saboda haka sakamakon ya sabama abunda ake nufi.

Saboda inda akace ku karkato dasu ana nufin ta hanyar Magana da soyyaya ne, batun kuyi masu wa'azi wanda ya zo a cikin ayar bai da wata ma'ana domin wannan matakin na wa'azi matakin farko ne sai na biyu nisantar kwanciya in shima bai yi amfani ba, sai kuma asake komawa matakin farko na wa'azi?.

Idan kuma ku karkato dasu yana nufin ta hanyar bayar da kyauta, to wannan fassarar ma ta sabama tsarin tartibin da ya zo cikin ayar domin ance ku nisance su gurin kwanciya sannan kuma adawo ace kuyi masu kyauta wannan ya sabama hikimar ayar.

3} abun nufi da duka na jiki wanda ya zo a cikin litattafan fiqh {hukunce hukunce} dole ya zamo duka marar cutarwa wanda ba zai kai ga karaya ba ko jin rauni ko bayyanar tabo akan fata[3]. Domin abunda ake bugata a duka na jiki shi ne domin akyara zaman gida da na aure, don haka duka anan yana nufin karkatowa zuwa ga rayuwa.

4} a mahangar kur'ani mai girma zalunci, cuta da wace gona da iri abubuwane wanda akai hani dasu, sai dai ba kowane tsanani da takurawa bane yake zama zalunci ba, misali kare kai daga abokin gaba ko da kuwa zai kai ga yaki da zubar da jini[4] dukuwa dacewa tsanani ne da takurawa amma ba zalunci bane, saboda haka ba kowace aya bace a cikin kur'ani wadda ke hani ga zulunci zamuyi amfani da ita domin hani ga tsanani da takurawa ba domin ba kowace takurawa take zama zalunci ba.

5} kur'ani mai girma acigaban {ku doke su} sai ya kawo idan sun yi biyayya sakamakon dukan to kada ku yuce gona da iri ga matan ku. Don haka in muka lura da ayar zamu ga cewa kur'ani baiyi hani ga duka na jiki bane, sai dai abun nufi shi ne idan dukan ya biya bukata sai adaina domin cigaba da shi zai zama wuce gona da iri wato zalunci.

6} kamar yadda akayi nuni kur'ani yana son warkar da wani nau'I na ciyo wanda wasu matan ke dauke da shi kamar yadda masana ilimin kwakwalwa suka tabbatar mai suna {neman cutarwa} wanda idan wannan ciyo ya taso masu to dole sai an doke su domin su koma halin su na farko[5].

Wannan na daya daga cikin mu'ujizozin ilimi na kur'ani mai girma ta yadda akawo hanyar magance wannan nau'in cuta matakin farko in cutar batayi tsanani ba sai bi tahanya Magana {wa'azzi} domin magance ta, in kuma Magana bai yi amfani ba sai adauki mataki na biyu wato janyewa daga kwanciya dasu in shima wannan mataki bai biya bukata ba wato in ciwon yai tsanani shi ne sai a dauki matakin karshe wato duka. Saboda haka da ace ma'anar ku buge su bayana nufin duka na jiki bane da irin wannan nau'in cutar in tayi tsanani so sai bazata warke ba.

7} idan ya zamo irin wannan matakin wato na duka bai zamo abun karbuwa ba, ta yaya ku ka yadda da matakin janyewa daga wurin kwanciya wato mataki na biyu har kuma kuke kafa dalili da cewa gujema mace wurin kwanciya yana karama miji yadda da kai kuma ya kalaba akan tsoron da yake tattare da shi, domin haka afili yake dukan mace shima zai iya kawo sakamakon da matakin da ku ka yarda da shi {wato matakin nisantar kwanciya}

 


[1] Ra'ad 17

[2] Ali imran, 112.

[3] Tafsirin namune, jildi na 3 shafi na 415.

[4] Ku yaki kafirai gaba daya kamar yadda suka yake ku gaba daya, 36, tauba.

[5] Tafsirin namune, jildi na 3, shafi na 415.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa