advanced Search
Dubawa
13398
Ranar Isar da Sako: 2012/03/14
Takaitacciyar Tambaya
Wasu kungiyoyi ne Addinin musulunci yake umartan a yake su kuma wasu kungiyoyi ne, yake umartan ayake su har sai sun musulunta, ko su ba da jiziya.
SWALI
Wasu kungiyoyi ne Addinin musulunci yake umartan a yake su kuma wasu kungiyoyi ne, yake umartan ayake su har sai sun musulunta, ko su ba da jiziya.
Amsa a Dunkule

Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya shari’ar annabi muhammadu (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) ita ce cikamakin shari’o’i wacce ya wajaba ga dukkan mutane, da sauran mabiya addinai na Allah, da ma addinan dab a na Allah ba, su yi bautan Allah da ita wannan shari’ar, su yi aiki a bisa dacewa da ita, kuma Allah madaukakin sarki ya dauki hakan a matsayin wani al’amari ne da

ya wajaba a kan kowa ya aikata (Wanda ya nemi wanin musulunci a matsayin addini to ba za a karba masa ba kuma aranar lahira yana daga cikin masu asara. )

kungiyoyin da masulunci ya fuskance su, masu sabani da shi, su uku ne su ne:

  1. Mushrikai da masu bautar gumaka.
  2. Munafukai.
  3. Ahlul kitabi.

Hakika addinin musulunci ya dogara ne akan wasu ginshikai muhimmai guda biyu wajen mu’amala da su.

  1. Ginshiki na farko: girmama hakkin dan Adam,
  2. Ginshiki na biyu, kira zuwa gaAllah ta’ala da hikimah da wa’azi mai kyau.

Da kulla yarkeniyoyi na zaman lafiya da alkawura da yarjeniyoyi daban daban da su. Bayan haka kuma

hakika hujja na mandik wanda ake dogara da shi wajen wa’azin musulunc sai ya fuskanci ko wace kungiya da irin mu’amalar da ta cancance ta.

Su kungiyar mushrikai, Musulunci ya jafar masu da alkawarinsu, ya kira su kuma da su tuba, sanan ya ba su dama na watanni hudu don yin tunani da komawa kan gaskiya. Ba shakka kuma hakan ba wai ya zo ne kurum ba, sai dai ya faru ne bayan wasu shekaru masu tsawo wanda musulunci yabi hanya ta hujja, da mandik da hankali, da hikima, da yin mahawara da hujjar da tafi kyau, kuma musulmi sun yi juriya sosai, na irin tsananin azabar da mushurikai suka gana masu, da azabar kaura, na barin gari, da kisa, da aka dinga musu, da kwace dukiyarsu da sauransu.

Sanan kuma, jefar musu da wadanan alkawura din daga bangare daya na kin yarda da alkawari ga mashurikai ya kebentu ne ga wadanda dalilai suka nuna irin shirye shiryen da suke yi game da warware alkawarinsu.

kuma hakan suka bayyana a filli, saboda haka ne ma ita ayar ta kange wani kaso daga cikinsu saboda cika alkawarisu, sai ayar tace: (sai dai ga wadanda ku kayi musu alkawari daga cikin mashurikai) [i].

Amma su jama’ar munafukai, wasu jama’a ne wadanda an ba su zabi, matukar munafuncinsu ya bayyana, tsakanin ko dai su dawo kan gaskiya, su shiga musulunci da gaskiya, su kuma nisanci ayukan munafunci, ko kuma ayi fito na fito dasu, wani abu ne tabbatace, cewa Annabi (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) bai yake su yaki na makami da makami ba, bayyi fito na fito dasu ta hanyar takobi ba, domin shi munafuki shi ne wanda yake bayyana musulunci, a soboda haka, yana more wa dukkan hakoki na musulmai, da kariya na doka na musulunci, duk da kuwa kokari yake yi na ya rusa musulunci a boye.

Abubuwan da za a amfanu da su daga ruwayoyi da maganganun masu tafsiri, shi ne cewa, abin da ake nufi da yakar munafikai shi ne a dinga sa musu shingaye, da wasu hanyoyi daban na jihadi, amma ba jihadin yaki da makami ba, misali: kamar a dinga zarginsu, da wofantar dasu, da yi musu narko, da kunyatar dasu.

Amma su jama’a ta uku wato Ahlul kitabi, bayan an kafa masu hujja, an kuma kirasu da hikima da kyakkyawan wa’azi, da bayyana hujjoji da dalilai, wadanda suke tabbatar da gaskiyar addinin musulunci mai tsarki, to adalilin dogewa, na wasu daga cikin wadannan, akan taurin kansu, da kin mika wuya ga gaskiya, sai musulunci ya biyo da su ta wata hanya tsaka tsaki tsakanin mushurikai da musulmai, shi ne aka ba su zabi, kodai su zauna cikin addininsu, da bayar da jiziya, ta yanda a wanan lokacin gwamnatin musulunci zata dauke masu Nauyi, na ba su cikakken tsaro, ko kuma su zabi ayi fito na fito.

Ta hanyar yin tunani game da wadannan ra’ayoyin, za mu iya fahimtar akida ta musulunci, akida ce wacce ta sanya mas’alar yin yaki a cikin wasu iyakoki, da katanga na dabi’a, wanda ya yi dai dai da hankali, amma ba yaki ya zamo wani aiki ne na nuna jabberanci ta amfani da karfi ba, don a tauye hakki na ‘yancin dan Adam, da kuma zabin da dan Adam yake da shi, a’a, sai dai a matsayin wani aiki ne na shinfida dokoki daga gwamnatin da take ci, a wani yanayi na tsari mai kyau, a cikin amsoshi na dalla dalla za’aga karin hujjoji akan haka.

 


[i]Masdarin farko

 

Amsa Dalla-dalla

Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gabadaya, kuma ayoyi masu albarka sun karfafa wanan al’amari din, daga cikin ayoyin akwai fadin Allah ta’ala: (Ayau na cika muku addininku na cika muku ni’imomina akan ku, na kuma yarje maku da musulunci a matsayin addininku) [1]

Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya shari’ar annabi muhammadu (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) it ace cikamakin shari’o’i wacce ya wajaba ga dukkan mutane, da sauran mabiya addinai na Allah, da ma addinan dab a na Allah ba, su yi bautan Allah da ita wannan shari’ar, su yi aiki a bisa dacewa da ita, kuma Allah madaukakin sarki ya dauki hakan a matsayin wani al’amari ne da ya wajaba a kan kowa ya aikata (Wanda ya nemi wanin musulunci a matsayin addini to ba za a karba masa ba kuma aranar lahira yana daga cikin masu asara). [2]

Kafin mu fara bayanin azuzuwa da gungu gungu na mutane, wadanda suke rayuwa a zamanin farkon kiran musulunci, muna ganin dole ne mu yi ishara zuwa ga wani muhimmin al’amari.

Hanyar shiyarwa ta addinin musulunci tana tsayawa ne akan wasu ginshikai muhimmai guda biyu.

  1. Ginshiki na farko: girmama hakkin dan Adam, da karrama shi, ko da yaya yake: (Hakika mun karrama dan Adam, mun dauke shi akan doron kasa da kuma a kan ruwa kuma mun azurtasu da abubuwa masu dadi sannan muka fifita su akan halittun mu masu yawa da babban fifiko kuwa). [3]

Kuma shi dan Adam ba a halicce shi don a kashe shi ko a zalunce shi ko akwace dukiyarsa ba.

Sai dai kawai Allah ya turo da annabawa ne gaba dayansu, da Annabi mafi girma (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam), don rayar da dan Adam, da dawo da shi akan lafiyayyen yanayinsa, domin ya maida shi cikakken yanayinsa na zama halifan Allah madaukakin sarki a bayan kasa (YAKU WADANDA SUKA YI IMANI KU AMSA MA ALLAH DA MANZONSA IDAN YA KIRA KU GA ABIN DA ZAI RAYAR DAKU) [4]

  1. Ginshiki na biyu, hakika hujja na mandik wanda ake dogara da shi wajen wa’azin musulunci shi ne hujja na hikima da kyakkyawar magana da yin muhawara da hujjar da tafi kyau. ”Kayi kira zuwa ga ubangijin ka ta hanyar hikima da kyakkyawan wa’azi, kayi muhawara dasu da hujjar da tafi kyau, hakika ubangijin ka shi ne mafi sani ga wanda ya bace daga hanyarsa kuma shi ne mafi sani daga shiryayyu”[5] wadan nan su ne hakika din, to amma, wasu abokan gaban musulunci, suna kokarin su nuna musulunci wani addini ne wanda ya samu nasara ta hanyar yakin takobi ne, kuma yana tilasta kansa akan mutane ne da kaifin takobi da mashi, wanda kuma wannan al’amarin ne, da bincike a kansa suke bukatar dogon bayani da kididdiga wanda kuma wanan gurin bazai ba da dama a tabo su ba.

To amma dai kungiyoyin da masulunci ya fuskance su wadanda kuma suna ci gaba da kalubalantarsa za a iya kasa su ne zuwa kaso uku.

  1. Mushrikai da masu bautar gumaka.
  2. Munafukai.
  3. Ahlul kitabi.

Su bangare na farko za a iya rabasu zuwa gida biyu,

  1. jama’ar da ba su da wata alaka da Annabi (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) ta wata yarjejeniya ko alkawari. Babu wata yarjejeniya da take tilastawa Annabi (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) na yin wasu abubuwa game da wadanan al’umma din.
  2. Su ne wadanda Annabi muhammadu (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) ya yi yarjejeniya dasu, yarjejeniya na sulhu, kamar yanda ya faru a hudaibiyya da wadansu wajajen. Wadan nan alkawura din da wadannan yarjeniyoyi wasunsu an iyakance su ne da wani lokaci na musamman, wasu kuma anyisu ne a sake game da lokaci. To a nan za mu samu wasu da a kayi al’kawari dasu dinnan sun cika al’kawarinsu kuma sun yi aiki da shi, a cikinsu kuma akwai wadanda suka saba al’kawari, ba su kuma bi sharuddan da aka tsara na yarjejeniyarsu da musulmi ba. bama haka ba, har ma suka hada kai da wasu kungiyoyin da suke husuma da Addinin musulunci, da abokan gaban musulunci, don su karfafa su ga yin fito na fito da wannan jaririn sakon.

Hakika suratul bara’a ta bayyana wannan al’amarin na wadannan mutanen sosai, bayan an kira su zuwa ga tuba, da komawa ga gaskiya, da dawowa cikin musulunci, da barin yin husuma, da barin taurin kai”Idan kun tuba to shi ne alheri a agareku”[6]sannan kuma ta fuskantar da kashedi mai tsanani ga masu taurin kai da yan husuma, ”Idan kun juya baya to ku sani hakika ku ba zaku gagari Allah ba kuma kayi albishir ga wadanda suka kafurta da azaba mai zafin gaske”[7]bayn haka kuma ayar ta yi ishara, akan taka alkawarin yarjejeniyoyin da aka yi, ta yi bayani game da jefar da alkawuran da aka yi yarjeniyoyi tsakanin wadannan al’ummomin guda biyu. ”Allah da manzonsa sun barranta ga wadanda kuka yi alkawari da su na mushrikai”[8]

Sannan kuma sai ta ba su lokaci na watanni hudu don su tsayar da shawarar da ta dace

Dasu”Ku yi tafiya a cikin kasa har na tsawon watanni hudu kuma ku sani ba zaku fi karfin Allah ba hakika Allah zai kunyata kafirai”[9]a

sai dai, ita wannan surar ta togace wan nan kungiyar da take da alkawri iyakantacce da musulmi, da iyakantaccen alkawarina lokaci, a inda Allah ta’ala yake cewa: ”sai dai wadanda kuka yi alkawari da su a cikin mushrikai sannan ba su tauye muku da komi ba kuma ba su taimaka wa kowa a kanku ba to ku cika musu alkawarin su zuwa ga lokacin su Hakika Allah yana son masu tsoron Allah”[10]

wani abin lura mai muhimmanci, shi ne ganin yanda Allah ta’ala ya bayar da dama ga kungiya ta farko, wata dama don yin tunani, da komawa ga gaskiya, a dai dai lokacin da babban buri ne, na musulunci, akan ya rushe bautan gunki da bautan sassake sassake, da tumbuke jijiyoyinta gaba daya daga kasa, da shiryar da mutane ga tauhidin Allah daya, makadaici, to amma duk da haka yana basuirin wannan dama din mai tsananin muhimmanci don tsayar musu da hujja.

A hakikanin gaskiya, hakika Allah subhanahu wa ta’ala, yana son ne ta wannan babbar shela din a cikin makkatul mukarrama, a wannan babban rana, yana so ne ya toshe duk wata kafa da mushrikai da makiya zasu fake a cikin ta, da rufe bakin mabarnata, don ka da suce an shammace su da yaki da kai musu farmaki, da cewa hakan ya saba wa mutunci da gwarzantaka.

Haka nan Kalmar cewa”zuwa ga mutane”a madadin ya ce “zuwa ga mushirikai” tana nuna wajabcin isar da wannan “shelar”da wannan sanarwar, ga dukkan mutane wadanda suke halarce a makka a wannan ranar, don wadanda ba mushrikai ba su ma su shaidar da hakan.

Sannan zancen da ke cikin wannan ayar, sai ta fuskanci su mushrikai din da kansu cikin kwadaitarwa da tsoratarwa, don su shiryu, sai ayar tace: ”Idan kun tuba ta shi ne alheri”wato amsawa ga sakon tauhidi, wanda a ciki akwai islahinku, kuma a ciki a kawi alheri gareku da al’ummar ku, a duniyar ku da lahirar ku, idan kunyi tunani sosai kuma da gaskiya da zaku ga cewa karbar da’awar musulunci, shi ne bandejin dukkan raunun nukan ku, amma ba wai Allah ne da manzonsa za su samu wani amfani ba. [11] Ba shakka kuma hakan ba wai ya zo ne kurum ba, sai dai ya faru ne bayan wasu shekaru masu tsawo wanda musulunci yabi hanya ta hujja, da mandik da hankali, da hikima, da yin mahawara da hujjar da tafi kyau, kuma musulmi sun yi juriya sosai, na irin tsananin azabar da mushurikai suka gana masu, da azabar kaura, na barin gari, da kisa, da aka dinga musu, da kwace dukiyarsu da sauransu.

Sanan kuma, jefar musu da wadanan alkawura din daga bangare daya na kin yarda da alkawari ga mashurikai ya kebentu ne ga wadanda dalilai suka nuna irin shirye shiryen da suke yi game da warware alkawarinsu.

kuma hakan suka bayyana a filli, saboda haka ne ma ita ayar ta kange wani kaso daga cikinsu saboda cika alkawarinsu, sai ayar ta ce: ”Sai dai ga wadanda ku kayi musu alkawari daga cikin mashurikai”[12].

Amma su jama’ar munafukai, wasu jama’a ne wadanda an ba su zabi, matukar munafuncinsu ya bayyana, tsakanin ko dai su dawo kan gaskiya, su shiga musulunci da gaskiya, su kuma nisanci ayukan munafunci, ko kuma ayi fito na fito dasu, kuma wannan shi ne abin da aya mai albarka ta yi ishara akansa tace: ”ya kai wannan Annabi kayi jihadi akan kafurai da munafukai kuma ka gallaza musu”[13]

abu ne tabbatace, cewa Annabi (Sallal lahu alaihi wa alihi wa sallam) bai yake su yaki na makami da makami ba, bayyi fito na fito dasu ta hanyar takobi ba, domin shi munafuki shi ne wanda yake bayyana musulunci, a soboda haka, yana more wa dukkan hakoki na musulmai, da kariya na doka na musulunci, duk da kuwa kokari yake yi na ya rusa musulunci a boye. kamar a yanzu zaka ga mutane da yawa wadanda ba su da rabon komi a musulunci, amma ba zai yiwu mu yi musu mu’amala irin ta kafurai ba.

Abubuwan da za a amfanu da su daga ruwayoyi da maganganun masu tafsiri, shi ne cewa, abin da ake nufi da yakar munafikai shi ne a dinga sa musu shingaye, da wasu hanyoyi daban na jihadi, amma ba jihadin yaki da makami ba, misali: kamar a dinga zarginsu, da wofantar dasu, da yi musu narko, da kunyatar dasu.

Kuma mai yiwuwa jumlar da tace: ”ka gallaza musu”ta na nuni ne da wannan ma’anar.

Kuma zai yiwu tafsirin wannan aya tana nufin cewa su munafukai, suna more dukkan hukunce hukuncen musulunci, da hakkokinsa da kariyarsa, matukar asiransu idan suna boye ne, ta yanda al’amarinsu bai bayyana ba, to amma idan yanayinsu ya bayyana, asiransu suka tonu, to za a yi musu hukunci ne da hukuncin kafurai masu yaki da musulunci, to awannan yanayin zai yiwu a yi jihadi a kansu har ma da jihadi na takobi.

To, amma abin da zai raunana wannan fassarar ita ce zaton sanya musu wannan sunan ba zai yiwu ba a wannan yanayin, domin za a dauke su ne a matsayin kafirai masu yakar musulunci, domin munafiki shi ne wanda yake bayyanar da musulunci, amma yake boye kafirci. [14]

To amma su kungiya ta uku (ahlul kitabi), kasancewar ita da’awar musulunci, gamammiya ce, wacce ta game kowa da kowa, ba a togace wata al’umma aka bar wata ba, saboda haka da’awar ta fuskanci suma ahlul kitabin, kuma kamar yanda yake a bisa dacewa da dabi’a, bayan an kafa masu hujja, an kuma kirasu da hikima da kyakkyawan wa’azi, da bayyana hujjoji da dalilai, wadanda suke tabbatar da gaskiyar addinin musulunci mai tsarki, to adalilin dogewa, na wasu daga cikin wadannan, akan taurin kansu, da kin mika wuya ga gaskiya, sai musulunci ya biyo da su ta wata hanya tsaka tsaki tsakanin mushurikai da musulmai, shi ne aka ba su zabi, kodai su zauna cikin addininsu, da bayar da jiziya, ta yanda a wanan lokacin gwamnatin musulunci zata dauke masu Nauyi, na ba su cikakken tsaro, ko kuma su zabi ayi fito na fito.

Kamar yanda yake cikin fadarsa madaukakin sarki: ”ku yaki wadanda ba su yin imani da Allah ko ranar lahira kuma ba su haramta abin da Allah da manzonsa suka haramta kuma ba su addinantuwa da addinin gaskiya daga wadanda aka ba su littafi har sai sun ba da jiziya hanu da hanu suna kaskantattu”[15]

To, a hakikanin gaskiya kiran su da aka yi na su yi imani tana nufin kira ce a kan su tsaftace akidunsu, daga abubuwan da aka lillika masa na tatsuniyoyi, da ayyukan shirka, da al’amuran da ba su dace da hankali da asalin dabi’ar halitta ba[16].

Kuma wannan abu ne da za mu iya fahimtarsa idan anyi dan karamin sharhi,

Ya wajaba mu yi darasin hanyar da musulunci yake bi a aikace, wajen sanya mutane su bi hukuncinsa, da farko ya kan yi tsari ne na share hanya, don ya isar da su cikin akidunsa na tunani da aiki, ta hanyar kiransu su yi tunani da nazari da tattaunawa, da cikakkiyar muhawara wacce za ta tsayar wa hankali, al’amuran da aka bijiro da su, don a yi nazarinsu cikin nutsuwa da bin hujjah, don yazamo rashin yarda, ko kuma karfafawaya zamo sun fito ne daga tunani sahihi, wanda ba ya da wani kulli daga duk wata alamar tambaya da ta fito a gaban akidu da natija ta karshe da ake mu’amala da su, sai dai zai ci gaba da rayuwa a tare da kofofin ilimi, wanda dama ana daukan su a matsayin hakki ne ga mai neman su har ya isa ga yakini, da sharadin su zamo al’amura ne da suke misalta ilimi, ba wai taurin kai ba, don mas’alar taurin kai bata da alaka da ‘yanci, sai dai ta na zuwa ne daga wani kulli na rai, wanda yakan motsu ne a dalilin tunani na ta’addanci.

Idan shi binciken bai isa ga natija ba, kuma ya zamo ba za a iya yin tarayya akan wata akida guda ba wacce hukuma ta doru a kai ba, ko dai saboda rashin samun yarda, ko don saboda taurin kai, to a nan, ita hukuma ta shari’a mai ci tana da damar ta kare samuwar ta da ci gabanta, da daidaituwar ta, ta hanyar sanya wadannan mutanen su karbi halaccin kafuwar gwamnatin, a cikin abubuwan da suke na aikace, ko dai ta hanyar su rungumi akidar, wato su bayyana shiga musulunci, a matsayin shi ne mai ba da dokoki, su kuma yarda da aikata bin dokokin gaba daya da gaske, ko kuma su yarda da bayar da wani haraji na musamman, bisa wasu dokoki na musamman, -shi ne abin da ake kira da jiziya, - a dalilin haka ita kuma da gwamnati za ta dauki nauyin lura da su da kiyaye su daga barin duk wani ta’addanci da muzgunawa ko take musu mutuncin su, yin hakan don a shigar da su cikin alkawarin musulmai, tare da yafe musu duk wasu nauyace nauyacen da ba su dace da biyayyar su ga addinin su ba, kamar a shigar da su a cikin sojojin da zasu yaki wasu ‘yan uwansu na cikin addinin su, ko kuma bai dace da maslahar gwamnatin ba gaba daya, to, idan ba su amince da hakan ba, kuma suka ki duk wata hanya ta bin dokoki, da sharuddan da ake nema don zama cikakken dan kasa. wannan ya zamo dalili ne akan cewa sun yi shelar tawaye ga musulunci da musulmai. to a wannan yanayin ya halatta a yake su, don a hana tawaye da ta’addanci a kan tsarin al’umma, har sai sun ba da jiziya da karfi da yaji, a bayan sun ki mikata a cikin zaman lafiya da fahimtar juna.

A karkashin wannan bayanin ne za mu, za mu fahimci cewa idan an samu yanayi na yarda da yarjejeniya a tsakanin su da musulmai, ta hanyar ba da jiziya da yarda da hukuncin yarjeniyoyi, wadanda zasu kiyaye musu matsayin su na ‘yan kasa a cikin yanayi mai kyau to, a nan babu wani yaki da za a yi da su. [17]

Wannan ke nan ya nuna cewa shi musulunci ba ya halatta yin yaki don kawai a bautar da al’ummu, a sace kadarorin su, a mamaye kasuwannin su, kamar dai yanda ‘yan mulkin mallaka suke aikatawa, a cikin yakukuwan da suke haddasawa, da zubar da jini, da sanya ci gaban ilimi a hanyar yin barna da rusau da ta’adi, da daukan rayuka, don sata da kwace, da shugabantar da zalunci da ta’addanci.

Shi musulunci abu ne mai kyau kawai, babu wani muni a tare da shi, shi yana yakar duk wanda ba ya addinantuwa da addinin gaskiya da adalci, wanda yake neman aikata barna a duniya.

Kuma kafirce wa Allah zalunci ne da barna a mahangar addinin musulunci da shari’arsa. [18]

Kuma dukkan hakan sai bayan an tsayar da hujjah da dalilai akan gaskiyarsa, da hakikar sa.

 


[1] Suratul ma’idah, 3.

[2] Suratu ali imran, 85.

[3] Suratul isra’I, 70.

[4] Suratul anfal, 24.

[5] Suratun nahal, 125.

[6] Suratut taubah, 3.

[7] Aya ta sama.

[8] Suratut taubah, aya ta 1.

[9] Suratut taubah, aya ta 2.

[10] Suratut taubah, aya ta 4.

[11]Littafin al amsal fi tafsiri kitabillahil munzal, wallafar makarim shirazi, juzu’I na 5, shafi na 531, na madrasatul imam aliyyu bn abi talib (a) kum, bugu na farko, shekara ta 1421, hijira kamariyya.

[12]Littafin al amsal fi tafsiri kitabillahil munzal, wallafar makarim shirazi, juzu’I na 5, shafi na 531, na madrasatul imam aliyyu bn abi talib (a) kum, bugu na farko, shekara ta 1421, hijira kamariyya.

[13]Suratut taubah, aya ta 73.

[14] Littafin al amsal fi tafsiri kitabillahil munzal, wallafar makarim shirazi, juzu’I na 4, shafi na 125 -126, na madrasatul imam aliyyu bn abi talib (a) kum, bugu na farko, shekara ta 1421, hijira kamariyya.

[15] Suratut taubah, aya ta 29.

[16] Littafin al amsal fi tafsiri kitabillahil munzal, wallafar makarim shirazi, juzu’I na 5, shafi na 584 na madrasatul imam aliyyu bn abi talib (a) kum, bugu na farko, shekara ta 1421, hijira kamariyya.

[17] Littafin tafsir, min wahayil kur’an, juzu’i na 11 shafi na 83-86

[18] Tafsirul kashif, wallafar muhammad jawad, mughniyyah, juzu’i na 1 shafi na 297.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene abin sha mai tsarkakewa?
    16942 Tsohon Kalam 2012/09/16
    "Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
  • Meye matsayin jagorancin malami a tsarin siyasar musulunci?
    7255 Tsare-tsare 2012/07/24
    A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance ...
  • SHIN YA HALASTA A RADA WA JARIRI SUNA MUHAMMADU YA’ASIN (YASIN) ?
    9020 Sirar Ma'asumai 2012/07/26
    Dangane da rada sunan (Ya’asin) akwai zantuka da aka ruwaito da ke nuna rashin yardar Imamai (a.s), game da amfani da sunan ga mutane. Kan hakan za mu iya kawo ruwayar da Imam Sadik (a.s), ya ke ce wa: “Muhammadu dai an muzu izini su rada, to ...
  • Me ake nufi da hadisi rafa’i
    14142 Dirayar Hadisi 2012/07/26
    An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
  • Shin a kwai wata madogara ta addini da ke nuna cewa turara kanyen esfand ko harmal na maganin riga kafi daga sharrin hassada?
    7746 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2017/05/20
    Ba zai yiwu ba ilimin da hankalin Dan Adam su riski wasu tabbatattun abubuwa ba, hassada ma na cikin waDancan abubuwan da hankali da ilimi basa iya tabbatarwa alal aKalla, hakama kuma hankali da ilimi basu samu dalilin kare hakan da watsi da shi ba. Idan muka ...
  • don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) amintacce?
    4674 تاريخ بزرگان 2019/06/12
    Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana ...
  • A lokacin da hura wa Annabi Adam (a.s) rai me ya fara cewa?
    4560 Hdisi 2017/06/17
    An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
  • a kan matan aljanna {hurul'in} shin mata zasu samu hurul'in ka yi bayani?
    18225 Tafsiri 2012/07/24
    Daya daga cikin ni'imomin ubangiji a ranar lahira ga wadanda suka yi imani da kyakyawan aiki shi ne sakamako da aljanna da ni'imomin ta. Ba bambanci wuri shiga aljanna tsakanin mace da namiji daga cikin ladar da sakamakon da ubangiji zai ba ‘yan aljanna akwai {hurul'in} wanda ...
  • Shin addini ya dace da siyasa?
    11649 Sabon Kalam 2012/07/23
    Addini ya zo ne domin rabautar mutum har zuwa karshen duniya, don haka ba yadda zata yiwu ya kasance bas hi da wani mataki game da abin da al’ummar duniya take bukata daya hada da jagorancin hukuma. Ta wani bangaren kuma yanayin dokokin musulunci sun tilasata wajabcin ...
  • Idan wasiyyin Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi an san shi tun farko, to me ya sa Annabi rataya mas'alar wasiyya da mas'alar amsawar su da amsa kiran Annabi?
    13223 Tsohon Kalam 2012/09/16
    Matafiyar shi'a game da abin da ya shafi Imama taken rairayu a matsayin cewa mukami ne kuma baiwace ta Allah Allah madaukakin sarki Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ne kawai yake isar da wannan sakon saboda wajibi ne Imami ya ...

Mafi Dubawa