advanced Search
Dubawa
12920
Ranar Isar da Sako: 2012/03/12
Takaitacciyar Tambaya
Don me ya sa Imam Ali (a.s) ya sanya wa ‘ya’yansa sunayen halifofin da suka gabace shi, tare da kuwa sabawarsa da kin sa gare su?
SWALI
Imam Ali (a.s) ya auri mata da suka Haifa masa ‘ya’ya bayan sayyida Zahara (a.s), wasu sunansu Usman dan Ali, abubakar dan Ali, umar dan Ali, uwayensu mata a jere su ne: Ummul banin ‘yar Hazam dan Daram, “Kashful Gumma, ma’arifatul A’imma” (2/66). Sai Laila ‘yar Mas’ud Addramiyya (al’irshad, s 167, mu’ujamul Khu’I 13/45), sai kuma Ummu Habib ‘yar Rabi’a (al’irsha, s 167). Kuma wane uban ne zai sanya wa ‘ya’yansa sunayen mutanen da ya fi gaba da su? Musamman idan ya kasance uba ne kamar Imam Ali dan Abu Talib (a.s). Yaya kuwa ya sanya wa ‘ya’yansa wadannan sunayen da kuke cewa yana gaba da su?! Shin mai hankali yana sanya sunan makiyansa ga masoyansa?!
Amsa a Dunkule

Idan muka koma wa tarihi da littattafansa zamu ga cewa Abubakar dan Ali dan Laila ‘yar Mas’ud assakafi, da Umar dan Ali dan Ummu habib, da Usman dan Ali dan ummul Banin (s), dukkansu ‘ya’yan Imam Ali (a.s) ne, kuma bayan mun duba sanadin ambatonsu da wadannan sunaye na halifofi uku ne zamu iya cewa:

Al’ada da tunanin mutanen wancan lokacin ba ta bayar da muhimmanci kan suna iri daya, kuma ba ta nuna yarda ko ki da wani mutum, ambaton wadannan sunayen a wancan lokacin ba ya sanya tunawa da sunayen wadannan halifofi uku.

Amma mu sani cewa a wancan lokacin wadannan sunayen sun yadu ta yadda ambaton da Imam Ali (a.s) ya yi wa ‘ya’yansa da wadannan sunayen ba ya kawo tunani game da wani daga cikin halifofi uku na farko, hada da  cewa akwai wasu daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w) da suke da wannan sunan kamar Usman dan Maz’uan da waninsa.

Wadannan sunayen sun yadu kuma sun shahara a wancan lokacin da bayansa a rayuwar Imamai (a.s) baki daya, kuma littattafan tarihi cike suke da hakan, don haka sunaye ne da suka kasance ba su da wani abin yabo ko muzantawa a wurin Shi'a a wancan zamani kamar dai sauran sunaye suke. Kamar yadda zamu ga marubuta tarihin amintattun mutane na ruwayoyi sun kawo daga ciki kusan shafe 60 na masu ruwaya da yake dauke da sunyan umar, ga ma Usman  dan Sa'id daya daga cikin wakilai hudu na Imam Mahadi (a.s) a lokacin karamar fakuwa.

Amsa Dalla-dalla

Idan muka koma wa littattafan tarihi zamu ga cewa Imam Ali (a.s) yana da ‘ya’ya daga matan da ya aura bayan shahadar sayyida Zahara (a.s) da uku daga cikin suke da sunayen halifofi uku na farko da suka yi halifanci bayan annabi (s.a.w) da suka hada da; Abubakar dan Ali babarsa Laila ‘yar mas’ud[1], da usman babarsa ummul banin dukkansu sun yi shahada a Karbala karkashin tutar dan’uwansu Imam Husain (a.s) [2], na uku kuwa shi ne umar dan Ali shi ma[3].

Idan kuma duba dalilin ambaton su da wadannan sunayen halifofi uku zamu ga akwai bayanai kamar haka:

1. Tun farko ba za a iya la’akari da sanya sunayen ‘ya’ya da dangi ba na wasu mutane dalili a kan sonsa da kaunarsa ko tarayya da shi a wata akida ko mazhaba ko siaysa da sauransu – kamar yadda rashin ambaton ‘ya’ya da sunan wani mutum ba ya nuna dalili kan rashin sonsa ko kaunarsa da sabawa da shi, sai dai zai iya yiwuwa kauna ko rashin kauna su shiga cikin wasu abubuwan irin wannan a wasu lokuta.

Hada da cewa al’ada da tuannin wancan lokacin ba su kasance suna bayar da muhimmanci mai karfi game da sanya sunayen ba, ba sa nuna yarda ko rashin yarda da mai sunan. Don haka ambaton wadannan sunayen bai kasance yana nuni ga karkakta ga halifofi ba, su wadannan sunayen kamar sauran sunaye ne kawai, sai dai da nisan tafiya a tarihi ne sai wadannan sunayen suka bayyana bayan wancan zamanin ya wuce, amma a lokacin Imam Ali ambaton ‘ya’yansa bai kasance don tunawa da wadannan sunayen na daya daga halifofi ba ko tunawa da halifa na farko.

Kamar yadda babu makawa ne mu sani cewa wadannan sunayen uku ba su kebanta da wadannan halifofi uku ba kawai, su sunayen sun yadu cikin larabawa kafin musulunci da bayansa, don haka sanya sunayen ba sa nunu zuwa ga soyayya da kauna.

Misali a Iran sunan sarkin da ya gabata (Shah) “Muhammad Ridha”, kuma ya kasance mutumin da mutanen iran suka fi kyama, sai dai wannan bai hana kasancewar wannan suna ya kasance daga sunayen da suka fi kowanne sunaye yaduwa a iran ba. Daga cikin sahabban annabi (s.a.w) akwai wanda ake kira da usman dan maz’un da waninsa, me zai hana Imam Ali (a.s) ya ambaci ‘ya’yansa saboda wadannan sahabbai masu daraja ba halifofi ba. Kamar yadda zaku iya gani idan kuka koma wa littattafan tarihin mazajen ruwaya kamar al’Isti’ab na ibn Abdulbarr da Usudu Gaba da ibn Asir, ku lura sosai sun kawo sahabbai masu yawan gaske da suke da sunan Abubakar, Umar, Usman. A nan zamu wadatu da littafin “Usudul Gaba fi Ma’arifatil Sahaba” mu kawo wadanda suke da sunayen Umar cikin sahabbai.

 1_ Umar al’Aslami, 2_ Umar al’Jam’I, 3_ Umar dan Hakam, 4_ Umar dan Salim al’Khuza’I, 5_ Umar dan Suraka… 22_ Umar dan alYamani; wadannan duk suna daga cikin wadanda ibn Asir ya kawo su.

Kamar yadda zaku gani wadannan sunayen sun yadu matukar gaske tsawon tarihin musulunci da kafinsa, sun yadu cikin mutane baki daya.

Amma tabi’ai kuwa daga wadanda aka kira su da umar suna da yawan gaske, misali muna iya kawo littafin nan na amintattun masu ruwaya da ya kawo kusan shafi 60 kan adadin masu rawayar da suke da sunan Umar.

Wadannan sunayen sun yadu haka nan a lokacin imamai ma’asumai masu daraja (a.s) kamar abubakar dan Abdullah al’ash’aari, ko abubakar al’hadhrami, sun kasance daga masu ruwaya da suke ruwaitowa daga Imam Sadik (a.s), kamar yadda haka nan muna iya ganin usman dan Sa'id daga wakilan Imam Mahadi (a.s) a lokacin karamar fakuwarsa. Wannan duka yana nuna cewar ambaton wadannan sunayen ba ya sanya tunanin mutane ya juya zuwa ga wanda yake ba mai sunan ba. A tarihi Ali ba daya ba ne, haka ma abubakar da umar da usman ba daya ba ne da Imam Ali (a.s) zai ambaci sunayen ‘ya’yansa don su, sai dai ambaton sunayen ya kasance ya yadu da ma cikin mutane kamar dai sauran sunaye.

 Da ambaton sunayen ya kasance da umarnin Allah (s.w.t) ne na musamman don wadannan sunayen da sai ya samu tsarki da daraja ta musamman kamar yadda yake a sha’anin sunayen ‘ya’yan Imam Ali (a.s) da Fadima (a.s) wato Hasan da Husain (a.s).

Don haka wani abu ne da ya kasance sananne cewa wannan sunan da wadancan sunayen na halifofi sun kasance daga sunayen da suka yadu a cikin larabawa lokacin jahiliyya da musulunci duka, jin wadannan sunayen a wancan zamanin ba ya sanya tunani ya juya ya koma zuwa ga halifofi sam. Don haka ba zai yiwu a yi amfani da sunayen domin nuna cewa akwai wata alaka da sosayya ta musamman tsakanin Imam Ali (a.s) da sauran halifofi ba don a rufa duk abin da ya faru na tarihi da musunta abubuwan da suka wakana[4].

2. Muna iya gani cewa Imam Ali (a.s) ya boye dukkan matsaloli da musibun da suka same shi don hikimarsa da basirarsa da rinjayarwarsa ga maslahar baki daya, sai ya tsayu da tafiya tare da halifofi da hukumarsu don kiyaye musulunci da maslahar al’umma, kuma ya kasance sau tari yana taimaka wa halifofi yana karfafar su yana ba su hannun taimakawa gare su, har ma sau tari umar yana cewa: “Ba don Ali ba da Umar ya halaka” [5], to akwai tsammanin cewa wannan sunayen da Imam Ali (a.s) ya sanya yana daga cikin hikimominsa da iya zamansa da mutane, domin shi yanayi ne da yake iya kaiwa ga samun wata kafar sulhu, da kawar da kokwanto da juna, da karanta matsaloli da sabanin da yake cikin al’umma, ba don wai yana karfafa ayyukansu ko son su ba. Ko mai dai me ye “Da mun yi duba da idon basira zuwa ga wancan lokacin mai duhu da dimuwa, da kuma tsananin da yake kan Shi'a a wannan lokaci, da mun ga cewa imamai ma’asumai (a.s) sun zama – bisa tilas – saboda kiyaye rayuwar mabiyansu – su yi aiki da takiyya ta hanyoyin kamar; ambaton sunan ‘ya’yansu da sunayen halifofi ko aure da manyan sahabba don su boye halin tsoro da takura da take kan shi’awa, domin hukumar Banu Umayya da Banu Abbas masu zalunci suna son su samu damar rashin wayewa da karancin tunanin mutane da sunan cewa imamai (a.s) ba su yarda da halifofin farko ba, sai su yi amfani da wannan damar don dada takura musu da tsanantawa da kisa da kora”[6].

Kamar yadda nuni zuwa ga wannan lamari yana da muhimmanci matukar gaske, idan mun duba littattafan tarihi ba mu ga wani bayani ko daya daga yke nuna cewa Imam Ali (a.s) shi ne da kansa ya sanya wadannan sunayen, don haka akwai tsammanin cewa sanya wadannan sunayen ya kasance daga iyayensu mata ne ko wasu makusantansu, kuma Imam Ali (a.s) bai hana su ba don ya girmama su.

 


[1] Mu’ujamus sikat, j 21, s 66, bisa mahangar dan Ashuubul Auham.

[2] Al’irsha, s 484.

[3] Mu’ujamus sikat, j 13, s 45.

[4] Attabri, Muhammad, jawabus shabil shi’I, s 55 – 56.

[5] Sai na ga hakuri a kan haka shi ya fi, sai na yi hakuri alhalin akwai kwantsa a ido, akwai shakewa a makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa. Nahajul balagap; subhi salih, s 48, huduba ta uku.

[6] Attabri, Muhammad, jawabis shabil shi’I, s 56 – 57.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa