advanced Search
Dubawa
14436
Ranar Isar da Sako: 2006/06/03
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne ma’anar shirin Ubangiji wato (makru) a cikin Kur’ani mai girma?
SWALI
Mene ne ma’anar shirin Ubangiji wato (makru) a cikin Kur’ani mai girma?
Amsa a Dunkule

(Almakru) Yana zuwa da ma’anar shirya wani abu da kuma neman wani abu wanda yake shiga cikin ayyukan alheri da na sharri saboda haka ne aka yi amfani da ita a cikin Kur’ani mai girma abar jinginawa da siffa mummuna wato makirci.

Tanadin Ubangiji: Da akwai ayoyi masu yawa wadanda suke jingina tanadi zuwa ga Allah Madaukaki ita tana yin duba ne zuwa jujjuyawa gamammiya ga Allah Madaukaki domin cewa shi ne mamallakin jujjuyawa ba a samun wani abu da aka juya wanda ya fita daga kewayen jujjuyawarsu mai fadi saboda haka ne Allah Madaukaki ya kasance a saman dukkan wani mai shirya al’amura (Allah shi ne mafi alherin masu shiyar al’amura) Allah Madaukaki yana cewa:

﴿وقد مكر الذين من قبلهم فلله المكر جميعا يعلم ما تكسب كل نفس وسيعلم الكفار لمن عقبى الدار﴾

Ma’anar wannan aya shi ne: “Hakika wadanda suka gabace ku sun yi shirya al’amura to Ubangiji shi yake da shiri gaba daya, ya san abin da kowacce rai take aikatawa da sannu kafirai za su san wane ne yake da karshen makoma”.

Wannan ayar tana yi bayani karara a kan cewa jujjuya al’amari na gaba daya, yana ga Allah Madaukaki kuma jujjuya al’amuran wasu wanda yake fuskantar nasa ba shi da wata alama da za a ambata.

Amsa Dalla-dalla

Abin da ake nufi da (makru) ita kalmar makru a harshen Larabci tana zuwa da ma’anar jujjuyawa, wannan kuwa ya hade ma’anar tana nufin abu ne kyau ko kuma mara kyau,[1] wannan jujjuyawar ta kasance a cikin mummunan aiki ko kuma kyakkyawa tare da cewa wasu daga cikin malamai sun fasasra kalmar da ma’anar yaudara, amma yayin da ake jingina ta ga Ubangiji nan kuma tana zuwa da ma’anar sakamako da kuma ukuba.

TANADIN UBANGIJI:

Yayin da muke la’akari da ayoyin da aka yi amfani da kalmar (makru) a cikinta za mu ga cewa abin da ake nufi da (makru) shi ne jujjya al’amura da kuma bincike shig ada wand ake fita wani lokacin yana kasancewa a cikin al’amuran alheri wani lokacin kuma yana jawo ma’anar cuta.[2] Misalin wannan abin da ya zo a cikin aya mai girma a cikin fadinsa Madaukaki:

﴿ويمكرون ويمكر الله والله خير الماكرين﴾[3]

Ma’anar wannan aya shi ne: “Suna shirya makirci, Allah kuma yana yi musu shiri, Allah shi ne mafi alherin masu tanadi”[4].

Abin nufi da fadinsa: “suna shirya makirci” yaudara da abin da mushirikai suka kukkulawa na tanade tanade don su dauki fansa a kan Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi kamar shirin da suka yi don su kashe shi ko kuma su sanya shi a cikin kurkuku da makamancin hakan, amma abin nufi a cikin fadinsa: “Allah yana yin nasa shirin” shi ne shirin Allah mai girma da bwaya madauakakin sarki kamar umartarsa da ya yi da yin hijira ga misali.

A yayin da muke samun kalamr “makru” a cikin Kur’ani mai girma a inda ake siffanta ta da mummunan abu[5] wannan yana nufin cewa kalmar a wani lokacin tana kasancewa fuskantar sharri da mummunan abu a wani lokaci kuma da ma’anar fuskantar alheri da kyakkyawan wani abu a bisa wannan tushe ne cewa ayoyi masu yawa wadanda suke danganta (makru) zuwa ga Allah Madaukaki tana duba ne zuwa shirinsa gamamme kuma shi ne mamallaki, kuma mai kewaye da dukkan wani shiri da zai taba yiwuwa   ba a samu wani shiri ya fita daga kewayen jujjuyawarsa ta allantaka awcce take mai fadi gamammiya da wannan hasashe ne cewa Allah Madaukaki yake a saman dukkan wani mai kintsa shiri.[6] Hakika aya madaukakiya wacce take cikin suratur Ra’adi[7] tan ashiryarwa a zahirance da kuma bayanai a kan cewa jujjuyawa gamammiya tana kewaye ga Allah shi kadai kuma shirin wadansu ba komai ba ne idan aka danganta shi da shirin Allah Madaukaki ba zai yiwu ya tuke zuwa wani abu ba ma’abocin hankali.[8]

 


[1] Karshi sayyid aliyu akbar, kamusul kur’an j – 6 shafi 265.

[2] Almunjid madatuk makaru.

[3] A’arafi 99 da 123: fadir 10 da 43 ra’adu 33 da 42 saba’i 33 yunus 21 ali-imrana, 54 nahal 26 da 45 da namli 50 da 51, nahu 22, ibrahim 46 – yusuf 13 gafir 45.

[4] Anfal 30.

[5] Fadir 43.

[6] Ali Imrana, 54

[7] Ra’adu

[8] Allama taba-taba’i almizan tarjamar almusawi alhamdani. j – 12 shafi 20, 355, mujalladi, nashir, al-intisharat islamiyya.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa