Please Wait
9677
- Shiriki
Marja’anci da ma’anar kasancewar malami makoma ne shi a karbar fatawa wurinsa a fikihu yana kishiyantar ma’anar koyi da malami ne. Domin a ma’anar koyi yana nufin wanda bai kware ba kan wani lamari ya koma wa wanda ya kware, wato yana nufin ke nan a koma wa makomar da ake koyi da ita kan wannan lamarin, don haka idan mutum ba shi da kwarewa to dole ne a mas’alolin kwarewa ya koma wa wanda ya kwarewa domin sanin su, wannan irin koyin lallai shi ne karbabbe kuma hankaltacce.
Ma’anar marja’anci a fikihu wanda yake nufin bayar da fatawa, yana da wata ma’ana da take daurantarsa da ake cewa da ita koyi; wato duk sa’adda wani ya zama makomar fatawa to dole ne saura su yi koyi da shi. Don haka idan mun duba ma’anar marja’anci ya zama dole mu duba ma’anar koyi.
Koyi (biyayya): yana nufin biyayya ba tare da dalili ba. Wannan kuwa shi ne ma’anarsa a Lugga.
Amma a fikihu Koyi yana nufin biyayyar wanda ba kwararre ba ga wanda yake kwararre. Don haka wannan ma’ana ce mai kyau karbabbiya hankaltacciya, sabanin ma’anar lugga da take da ma’anar bi da ka. Kuma wannan yana komawa zuwa ga ma’anar ayar nan mai cewa: “Ku tambayai ma’abota ambato idan kun kasance ba ku sani ba” [1]. Da kuma ruwayoyi da suka yi nuni zuwa ga wannan lamari karbabbe hankaltacce.
Da wannan ma’anar za cewa; koma wa malami shi ne samun kwarewarsa a fikihu da iya fitar da hukuncin shari’a daga madogarar shari’a.
Don Karin Bayani:
1- Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat ba Diyanat, Cibiyar al’adu ta Khaniyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.