advanced Search
Dubawa
10778
Ranar Isar da Sako: 2019/06/15
Takaitacciyar Tambaya
ya rayuwar Abuddarda” da kasance? mene ne Mahangar ahlul baiti a kan shi? Mine ne hukuncin ruwayoyin da a ka rawaito daga gare shi?
SWALI
ya rayuwar Abuddarda” da kasance? mene ne Mahangar ahlul baiti a kan shi? Mine ne hukuncin ruwayoyin da a ka rawaito daga gare shi?
Amsa a Dunkule

{uwaimar dan malik} wanda ya shahara da alkunyar abuddarda”dan asalin kabilar khazraj yana daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w). yana daya daga cikin mutanen khazjar da suke rayuwa a madina ya shiga musulunci bayan zuwan manzon Allah (s.a.w) madina da wasu yan watanni.
Abuddarda”yana fifita imam Ali (a.s) a kan mu”awiya,yaje wajan mu”awiya dare da abuhurera sai ya kira mu”awiya a kan yima imam Ali (a.s) biyayya, amma lokacin da mu”wiya ya fake da batun kashe usman ya kuma bukaci imam Ali (a.s) da ya bashi makasa usman, sai ya tura abuddarda”da abuhurera zuwa ga imam Ali (a.s) domin su bukaci makasan usman daga imam (a.s) mu”awiya ya yi haka ne domin yi ki amsa kiran da suka yi mashi na da”a ga imam (a.s) .
Hakanan suka yi sukaje wajan imam Ali (a.s) amma sai suka hadu da malik ashtari wanda ya zarge su kuma ya hana su ganin imam (a.s). a rana ta biyu sai suka je wajan imam (a.s)  suka bukaci makasan usman, sai suka samu sama da mutun dubu goma wadan da suke ganin sune makasa usman. Sai suka koma garuruwan su tare da yanke kauna sai suka zamu abun zargi a gun Abdurrahman bin usman.
ta kowane hali dai matakin da ya dauka a kan hukumar gaskiya yana cikin mutanen da imam (a.s)  yace {su basu taimaki gaskiya ba su kuma ba su kaskantar da karya ba}.
Ruwayoyin shi sun zo a cikin litatafen ahlussuna da na shi”a wadan da ya rawaito daga manzon  Allah (s.a.w) .
A kwai bam bancin mahanga a tsakanin maluman tariha dan gane da mutuwar shi, wasu sun ce ya mutu bayan yakin siffin[i] wasu kuma suna ganin ya mutu shekaru biyu kafin kasha usman.

 

[i] Ibin hajar, ahmad bin ali bin hajar al”asgalani, al”isabat fi tamizlsahabat, mujaladi na hudu shafi na 622, berut, darulkitab al”ilmiyat, 1415.k
Amsa Dalla-dalla

{Umaira dan malik} wanda ya shahara da alkunyar abuddarda”dan asalin kabilar khazraj[1] yana daga[2] cikin sahabban manzon Allah (s.a.w). yana daya daga cikin mutanen khazjar da suke rayuwa a madina ya shiga addinin  musulunci. Yan da abuddarda”ya karbi musulunci wata rana {abdullahi bin rawah} wanda abuddarda”yake daukar shi a matsayin dan uwan shi ya je gidan abuddarda” sai bin rawah ya dauki gatari ya fara sare gumakan abuddarda”a lokaci guda kuma yana rera wanan baitin:{ ku kuji sunayen shedan da duk wani abun da a ke bauta ba Allah bata ne}. a lokacin da abuddarda”ya dawo gida, sai matar shi ta sanar da shi abunda bin rawah ya aikata; bayan tsawon lokaci abuddarda”yana tunani sai yace: in da wanan gunkin na da alkhairi da yaba kan shi kariya. da ga karshe abuddarda”tare da Abdullah bin rawah suka je wurin manzon Allah (s.a.w) ya kuma amshi musulumcin[3]. Koda yake farkon zuwan manzon Allah a madina abuddarda”bai shiga musulumci ba sai bayan yan watanni, yaje ya amshi addini daga ma aiki (s.a.w). wasu masana tarihi na ganin cewa yakin khandak da yakokin da suka auku bayan shi, abuddarda”bai halarta ba saboda a lokacin bai shiga musulumci ba. [4]
A wani yaki manzon Allah (s.a.w)  ya yima abuddarda”kuka yana cewa:{wanan uwaimar yana da matukar alheri}.[5]
Bayan wanan ruwayar, ahlussunna suna da ruwayoyin da suke nuni cewa manzon Allah (s.a.w) ya yabi abuddarda” daya daga cikan su ance manzon Allah (s.a.w)  yace abuddarda”shine mafi hikima acikin aluma[6]
An kuma rawaito cewa manzon Allah (s.a.w)  ya hada yan uwan taka tsakanin abuddarda”da salman farisi a matsayan yan uwa na addini[7]. Alaka a tsakanin su ta cigaba har zuwa lokacin da abuddarda”ya koma siria shi kuma salman na irak sai suka yi musayan wasika ya rubuta masa: ubangiji ya ba ni dukiya da da a nan, kuma na sauka kasa mai tsarki.
Sai salman ya ba shi amsa cewa: ka rubuto mini cewa kana da dukiya da da, ka sani arzuta ba da dukiya da da ba ne.
Abu darda” ya kasance a madina har zuwa lokacin halifa na biyu har zuwa lokacin da halifa na biyu ya bayar da umarnin wani aiki sai ya fita daga madina ya tafi siriya, halifa na biyu ya dora masa nauyin alhakin yin hukunci da yin limancin salla a kasar siriya[8].
A lokacin da abuddarda” ya zama alkali mutane sun kasance suna yi masa albishir, shi kuma sai ya ce: ku yanzu kuna yi min albishir da yin alkalanci, alhalin ni yanzu na kasance a kan wurin hadari wanda ya fi nisan tsakanin nan da garin adan[9]. Da mutanen sun san abin da yake cikin alkalanci na wahalhalu saboda kiyayya da sun nisanta kansu da shi, da kuma sun san abin da yake cikin kiran salla na lada da sun yi rigima da junansu saboda kwadayin ladansa[10].
Abuddarda” wanda yake ganin fifikon imam Ali (a.s) kan mua”awiya
Abuddarda”yana fifita imam Ali (a.s) a kan mu”awiya,yaje wajan mu”awiya dare da abuhurera sai ya kira mu”awiya a kan yima imam Ali (a.s) biyayya, amma lokacin da mu”wiya ya fake da batun kasha usman ya kuma bukaci imam Ali (a.s) da ya bashi makasa usman, sai ya tura abuddarda”da abuhurera zuwa ga imam Ali (a.s) domin su bukaci makasan usman daga imam (a.s) mu”awiya ya yi haka ne domin yi ki amsa kiran da suka yi mashi na da”a ga imam (a.s) .
Hakanan suka yi sukaje wajan imam Ali (a.s) amma sai suka hadu da malik ashtari wanda ya zarge su kuma ya hana su ganin imam (a.s). a rana ta biyu sai suka je wajan imam (a.s)  suka bukaci makasan usman, sai suka samu sama da mutun dubu goma wadan da suke ganin sune makasa usman. Sai suka koma garuruwan su tare da yanke kauna sai suka zamo abun zargi a gun Abdurrahman bin usman[11]. Ko da yake wannan labarin bisa fadin cewa mutuwar abuddarda” ta kasance ne bayan siffin, amma bisa cewa wasu masu tarihin sun kawo cewa kafin hukumar imam Ali (a.s) ne ya rasu, to wannan labarin ba zai zama karbabbe ba.
Ta kowane hali dai, matsayinsa game da hukumar imam Ali (a.s) muna iya cewa ya kasance daga cikin wadanda imam Ali (a.s) yake fada game da su cewa;  su basu taimaki gaskiay ba, su kuma basu kaskantar da barna ba[12].
Haka nan wasu ruwayoyi sun zo daga littattafan hadisan shi”a kamar na, sheikh Dusi a littafin Khilaf, an kuma karbo fatawa da ruwayoyi daga gare shi kan hakan[13].
Akwai sabani game da mutuwar abuddarda”, wasu suna ganin ya mutu bayan siffin[14], wasu kuwa suna ganin ya mutu ne shekara biyu kafin mutuwar usman[15].

 

[1] Uwaimar bin malik bin zaid bin kais bin amit bin amir bin adi bin ka”ab bin allkhazjar bin haris bin alkhazjar.
[2] .Alhasimi albasir, Muhammad bin sa”id bin muni”i, altabakatulkubura, mujaladi na bakwai shafi na 274, abdulkadir ata, Muhammad, darulkutul ilmiyat, berut, 1990/1410: husaini  tafrishi, sayid Mustafa ,nagadlrijal. Mu” asasar ahlubaiti  (a.s)  kum, bugu na farko 1418 k. Koda yake wasu sunce sunan shi amir ba uwaimar ba da ga cikin litafan a kwai ibin asir, abulhasan Ali bin Muhammad ,asadlkayat fi marifatulsahabat, kahbashf  mujaladi na hudu shafi 18, berut, darulfikr 1409 k.
[3] .Altabakatulkubura, mujaladi na bakwai shafi na 274_275.
[4]Abu umar yusuf bin Abdullah bin Muhammad bin abdulbar,al”istiab fi marifatulsahab ,mujaladi na uku, shafi na 1228, daruljil,berut,1412_1992.
[5] .Altabagatulkubura, mujaladi na bakwai shafi na 274.
[6]. Asadlgaya, mujaladi na biyar shafi na 97..
[7] A bunda ya gabata, mujaladi na biyu, shafi 268.sh
[8] .ilazari ahmad bin yahaya,futulbuldan, shafi na 204, wanda ya fasara: tawakul, Muhammad ,tehrani, yadawar nukre,1337 sh:w .r.k altabaktulkubura, mujaladi na bakwai, shafi 275.
[9]Daya daga cikin garuruwan kasar yaman.
[10] Altabakatulkubura, mujaladi na bakwai shafi na 275.
[11] Ibin kutaiba dinuri abu Muhammad Abdullah bin muslim al”imamat wal siyasiyat  wanda a kasa ni da tarihin khulafa mujaladi na daya shafi na 128 rubutawar :shiri,ali, berut, darulauza, 1410.
[12] . {bai taimaki gaskiya ba bai kuma tozarta karya ba} imam ali a.s nahjulbalaga  wanda ya kirkiro  sayid  razi wanda ya adita atardi, azizullah, shafi na 461 mu assar nahajulbalaga, bijo bugu na daya 1372,sh.
[13] Sheikh tusi, alkhilaf,mujaladi 1,shafi 376: shafi380 mujaladi 2,shafi 168 da…mai yadawa jame mudarrisin kum, bugu na farko, 1407.k.
 
 
[14] . Ibn hajar asqalani, ahmad ali , alísaba fi tamyizis sahaba, j 4, s 622, bairut, darul kutubul ilmiyya, 1415 h.
[15] . Usudul gaba: j 4, s 20.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa