Please Wait
7227
- Shiriki
A yanzu haka a jamhuriyyar musulunci ta Iran ana ayyana ‘yan takarar majalisar Khubrigan ta hannun shura Nigahban ne. To akwai batun sukan cewa Jagora shi ne yake ayyana ‘yan shura Nigahban, su kuma suke ayyanar cancantar shiga takara ga ‘yan majalisar khubrigan, su ‘yan majalisar khubrigan su ne suke ayyana jagoran duka, to a nan a fili yake cewa an samu jeka-kadawo ke nan.
Bayanin amsar wannan sukan a fili yake idan mun duba bambancin da yake tsakanin wadannan bangarorin, domin su ma dukkan ‘yan majalisar Nigahban ba kai tsaye ne jagora yake ayyana su ba, kuma ta wani su kuma ‘yan Nigahban suna ayyana sharuddan cancantar ‘yan Khubrigan ne kawai, ba su ne suke zabar su ba, domin mutane ne suke zabarsu kai tsaye.
Da farko kafin mu bayar da amsa zamu fara bayanin wannan lamarin sannan sai mu shiga warware shi dalla-dalla.
A zaben da mutane suke yi wa jagora wanda ba kai tsaye yake ba domin mutane suna zabar wakilansu ne a majalisar khubrigan, sannan su kuma sai su zabi jagora malami wanda ya cika sharudda daga cikin sauran malamai. Kuma a doka ta 108 ta kundin tsarin jamhuriyyar musulunci ta iran an riga an yi bayanin sharuddan wanda zai zama dan majalisar khubrigan, da aka dora alhakin yin hakan kan shura nigahban, sannan su kuma khubrigan sai suka samu alhakin zabar jagora.
Ta wani bangaren kuwa, shura nigahban bisa lambar doka ta 99 a kundin tsarin mulkin kasa suna da hakkin kula da duk wani zabe da ya hada da zaben majalisar khubrigan zasu yi wa jagora, da na shugaban kasa, da na ‘yan majalisa, da tambayar al’umma kan jin wani ra’ayi nasu da ya shafi zabe, da tambayar al’umma kan wani ra’ayi game da kasa.
Wannan lamarin kula da lamurran zabe yana kunshe cikin sharuddan da aka gindaya su game da dan takarar zabe, da yadda za a yi zaben, kuma a irin wannan lamarin ba su da wani abu sai lura da yadda za a gudanar da zaben, da gudanar da shi. Kuma ana cewa da irin wannan duba lamarin “Kula da gudanarwa” wanda a gefe guda akwai nau’in wani lura da gudanarwa da mai duba ba shi da wani hakkin raddi ko bata wani sakamako da ake kira da “Kula da dubawa”.
Kuma kari kan hakan a bisa doka ta 98, ita shura Nigahban tana da hakkin fassara ma’anar da ake nufi game da zabe a doka ta 99, kuma shi ne bayani da yake karbabbe.
Da wannan lamarin zamu gani a fili yake cewa a jamhuriyyar musulunci ta iran ana ayyana cancantar dan takarar majalisar khubrigan ta hannun shura Nigahban ne. Don haka ne aka samu suka game da hakan da cewa, ai Jagora ne yake ayyana ‘yan shura Nigahban, su kuma su ne masu tace ‘yan takarar Khubrigan, kuma su ‘yan Khubrigan su ne masu ayyana jagora don haka wannan ya zama jeka-kadawo ke nan.
Kafin bayan da amsar wannan sukan dole ne mu kula da wani abu guda; jeka-kadawo na palsafa kamar yadda ake kawo shi cewa shi ne: “a” ya zama daga “b”, sannan ita kuma “b” ta zama daga “c”, ita kuwa “c” ta zama daga “a”. Wannan shi ne ake kira jeka-kadawo, da ba yadda za a iya samun wani abu ya faru, domin “a” ya dogara da “c” ita ma ta dogara da “a” ke nan. Kuma a wannan halin babu yadda za a samu wani abu ya faru.
Amma amsar wannan sukan zamu ga da farko akwai mugalada (Badda-bani ko Jirwaye) a ciki, domin idan mun lura zamu ga akwai bambanci tsakanin wadannan majalisosi da ofisoshi ta fuskacin nauyin da ya hau kansu. Domin jagora ba dukkan ‘yan shura Nigahban ne yake ayyanawa ba, sai dai a bisa doka ta 91 a kundin dokar kasa zamu ga cewa su goma sha biyu ne da ya hada da malamai hudu da jagora ne yake ayyana su, da kuma wasu shiga wadanda suke masana doka a duniya da shugaban kotun kasa ne yake ayyana su, sai ya mika sunayensu a hannun majalisar kasa, daga nan ne sa ‘yan majalisa su zabe su, sannan sai su mika sunansu ga shura Nigahban, don haka ba duka ‘yan shura Nigahban ne jagora yake zaba ba.
Ta wani bangaren kuwa zamu ga cewa shura Nigahban ba su ne suke ayyana ‘yan Khubrigan ba, sai dai su suna karfafarsu ne ta hanyar duba cancantarsu bisa sharuddan da suka zo a kundin dokar zaben ‘yan majalisar Khubrigan, don haka ne su ‘yan majalisar khubrigan kai tsaye ana zabar su ne ta hannun mutane.
Don haka ‘yan majalisar Khubrigan suna ayyana jagora ne, kuma su kansu ba ana ayyana su ta hannun shura Nigahban ba ne, kuma ba dukkan ‘yan shura Nigahban ba ne ake ayyana su ta hannun jagora.
A takaice; alakar tsakanin wadannan bangarori da ya hada da: jagora, shura Nigahban, da majalisar Khubrigan, ba iri daya ba ne balle a zo da wani suka na neman ingancin wannan a irin mahangar nazarin Falsafa ko hakkokin wannan lamarin.
Don Karin Bayani:
1- Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat ba Diyanat, Cibiyar al’adu ta Khaniyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.