advanced Search
Dubawa
5647
Ranar Isar da Sako: 2014/10/30
Takaitacciyar Tambaya
Akwai wasu Hadisai har a cikin Littattafan Shi’a da suke hana a yi Gini a kan Kaburbura, shin duk da samuwar wadan nan Ruwayoyin ta yaya zamu iya Halatta gina Kabari, da da Kubbobi a kan Makwantan Imamai?
SWALI
Na ga wasu hadisai da suke hana a gina makwantai da kubbobi a kan kabari. Ina neman karin bayanin wannan al’amarin An ruwaito a cikin littafin (Manla yahadhuruhul Fakih) da littafin (wasa\'ilush shi’a) daga Imamus Sadik (a) ya ce: “Manzon Allah (s.a.w) ya hana a yi salla a kan kabari, ko a zauna a kai, ko a yi gini a kansa…”. kuma an karbo daga gare shi (s.a.w): “Kar ku mayar da kabarina ya zamo alkibla ko masallaci, domin Allah ya tsine wa Yahudawa a saboda sun dauki kaburburan Annabawan su a matsayin masallatai, ” kuma a cikin littafin (Furu\'ul kafi da Man la yahdhuruhul fakih da wasa\'ilush shi\'a) daga samma\'ah dan Maharan cewa ya tambayi Abu Abdullahi (a.s) game da ziyarar kabarbura da gina masallatai a cikinsu, sai ya ce "Game da ziyarasu ba laifi, ba za a gina masallatai a cikinsu ba) haka nan ya zo a cikin littafin (Man la yahdhuruhul fakih) daga Imamus Sadik (a.s): ”dukkan abin da aka dora a kan kabari wanda ba kasar kabarin bane to nauyi ne a kan mamaci” kuma a cikin littafin (furu\'ul kafiy da littafin wasa\'ilush shi\'a) daga Abu Abdullahi (a.s): ”Annabi (s.a.w) ya hana a kara wata kasa a kan kabari wacce bata fito daga cikinta ba ne, kuma akwai wata ruwaya a cikin littafin (Manla Yahdhuruhul fakih) daga Ali Amirul muminin, daga littafin wasa\'ilush shi\'ah) daga Ali Amirul Muminin (a.s) ya fadi abin da yake da ma\'anar cewa: "wanda yayi gini a kan kabari ko ya dora mutum mutumi a kai, to ya fita daga musulunci” a cikin (littafin wasa\'ilush shi\'a kuma) daga Abu Abdullahi ya ce Amirul Muminin (a.s) ya ce: “Manzon Allah ya aike ni zuwa Madina, ya ce kada ka bar wani hoto sai ka shafe shi, kada ka bar wani kabari sai ka daidaita shi.” kuma a cikin littafin (al istibsar da littafin wasa\'ilush shi\'a daga Aliyyu dan Ja\'afar (a.s) ya ce: "Na tambayi Abul Hassan Musa (a.s) game da hukuncin gini a kan kabari da zama a kai, shin ya inganta? Sai ya ce: ”bai inganta ba a yi gini a kai, ko zama, ko a fente shi, ko a sumunte shi”.
Amsa a Dunkule
Alkur'ani mai girma ya ambata a fili sosai, game da mas'alar gina masallaci a kan kaburburan As- habul Kahafi, a inda ya ambaci labarinsu, kuma ya halatta shi ne, bai hana ba, a'a sai dai ma, ya ambace shi ne, yana mai karfafa shi, a matsayin wani al-amari ne mai kyau.
 Akwai kuma ruwayoyi masu yawa, wadanda ba wai kawai suna nuna halaccin yin ibada a kusa da kabari ne kawai ba, a'a, suna ma nuna cewa yin ibadar tana da lada ninkin ba ninkin, a wani bangare na uku kuma akwai ruwayoyin da a dubi na farko za a ga kamar sun saba daga ita wannan ayar mai girma da gungun ruwayoyi na farko, sai dai kuma dole ne a fahimci cewa abubuwan da suke faruwa, da wasu al'amura na zaman takewa, kamar yin ridda zuwa ga shirka, da fankamar yawa, da alfahari, da rashin hakuri da juriya, da wasu tunanunnuka na bata wadanda ba su dace da addinin musulunci ba, da wadanda suke barazana ga al'ummar musulmi suna daga cikin jimillar dalilan da suke sa wa a hana mutane, su nuna tsananin karkata ta wajen muhimmantar da kaburbura daga imamai ma’asumai, (a.s)
 kari a kan haka kuma shi ne cewa idan muka duba gamammiyar al’adar musulmi, da kuma na Ahlul baiti (a.s) a kebance zamu gan su suna gani da idanuwansu yanda aka yi gini a kan kabarin Manzo mafi girma (Sallal lahu alaihi wa alihi) da imamai na farko kamar Imam Husaini (a.s) amma ba su hana ba, kuma matafiya da malaman tarihi sun labarta mana labarin kubbobi da yin gini a kan kaburbura, a kan idon malaman musulunci gaba dayansu, a nan ga kabarin da ake darajantawa na Abu Hanifah, a can kuma akwai kabarin Abdul Kadir, na uku kuma ga na Malam Wane, ….
 kuma dadin da dawa a kan hakan, wannan dabi’ar ta watsu a cikin dukkan kasashen duniyar musulunci, tun daga arewacin Afurka har zuwa kasar Indiya, da kasashen da suka yi makwabtaka da su.
 Ba a taba hanawa ba, sai a shekaru dari biyu da suka wuce, daga wasu da suke daukar kansu a matsayin masu kare tauhidi, kai kace dukkan Malaman Musulunci, a tsawon shekaru darurruka, ba su fahimci abin da wahabiyawa suka fahimta ba!!.
Kuma wannan yana nuna kasancewar dukkan Malaman mazhabobi, suna fahimtar ruwayoyin hanin nan da wata fassara ce ta daban, wacce ba ta kore halaccin gina kubbobi a kai ba.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa