advanced Search
Dubawa
8569
Ranar Isar da Sako: 2011/01/18
Takaitacciyar Tambaya
Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
SWALI
Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
Amsa a Dunkule

Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma mahalicci to wannan al’amari a fili yake cewa batacce ne kuma ba zai yiwu ba. Sai dai wannan maganar zata iya yiwuwa tana nuni da wata ruwaya ce da aka karbo daga imam Ja'afar Sadik (a.s) wacce yake fada cikinta cewa; “ibada jauhari ce, badininta ubangijintaka ce” ma’anar wannan maganar shi ne isuwa zuwa ga matukar bauta da narkewa cikin zatin Allah, ba ana nufin mutum ya koma ubangiji ba.

Amsa Dalla-dalla

Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma mahalicci to wannan al’amari a fili yake cewa batacce ne ba zai yiwu ba, kuma saken zuci ne kawai da ba shi da wani tushe, kamar yadda ya zo a kur’ani mai girma cewa Fir’auna  ya yi da’awar ubangijintaka sai ya kama hanyar tabewa kamar yadda yake a fadinsa madaukaki: Sai ya ce ni ne ubangijinku mafi daukaka, sai Allah ya rike shi da azabar karshe (lahira) da ta farko[1] (duniya).

Sai dai abin da ake kawowa a bahasin irfani a babin tajallin siffofin Allah da makamancinsa wannan wata maganar ce daban da ta saba da waccan, kuma tana da alaka da ruwayar da aka karbo daga imam Sadik (a.s) cewa: “ibada jauhari ce, badininta ubangijintaka ce[2]” kuma shigen irin wannan maganar ta zo a kalaman masu irfani da suka yi bayanin sa dalla-dalla.

Wannan maganar a cikinta akwai nuni da mafi daukakar matsayi da martabobi da mutum yake kaiwa zuwa gare su, bayan ya narke cikin zatin Allah sai kuma ya wanzu ciki da wanzuwar Allah, kuma matsayin wanzuwa bayan narkewa ba yana nufin mutum zai canja ya koma zuwa Allah ubangiji ba, ko kuma ya kai ga matsayin ubangijintaka, sai dai abin da ake nufi da narkewa da sabewa (yin saba da fita) daga zatinsa shi ne mutum zai zama mahallin tajallin (bayyanar) siffofin Allah ne.

Saboda haka ba yadda mutum zai iya kaiwa zuwa ga matsayin ubangijintaka ta kowane hali, sai dai yana iya narkar da zatinsa sai ya bayyana da siffofin ubangiji da yake bayyanar da su ga wannan mutum da ya narke, kamar dai yadda arifai suke cewa “matukar samuwa ta wanzu (to shi ma zai wanzu)” ba zai yiwu ubangiji ya zama cikin bawa ba, da nufin cewa bawa yana nan dai bawa, ubanigiji kuma yana dai ubangiji, ba zai yiwu a hada su biyu ba.

Kuma an yi nuni da wannan matsayi a wasu ruwayoyin daga cikin akwai hadisin nan na kudsi shahararre da yake cewa: “Bawa ba ya gushewa yana kusanta zuwa gare hni da nafiloli da ibadoji har sai na so shi, idan na so shi sai in zama jin sa da yake ji da shi, da ganin sa da yake gani da shi, da hannunsa da yake riko da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita” [3].

Kamar yadda komawa da karanta ruwayoyin da ziyarorin da kuma kalaman da suke zuwa daga ma’asumai da matsayinsu yana nuna mana wannan matsayi mai girma, sai dai ta wata fuskar kuma akwai wasu mutane masu gazawa ga fahimtar irin wannan kalamin wadanda suke ganin sa shisshigi ne a addini, sai dai mu zamu yi bayanin wannan ruwayar wani lokacin.

Daga irin wannan akwai maganar wasu arifai da ta zo don bayanin matakai da matsayoyi cikin bayani na falsafa da hikima, daga cikinsu akwai Mulla Sadra a littafinsa “Ikazun na’imin” (farkar da masu bacci) da ya yi bayanin tafiyar masu irfani zuwa ga Allah madaukaki, yayin da ya kai ga matsayin tauhidi sai yake cewa:

“An ce wannan tauhidin shi ne suturta fuskar bauta da fuskar ubangijintaka, da boye falakin zatinsa yayin samun ranar girma da daukaka, sai ubangiji ya kasance a zahiri bawa kuwa ya kasance a boye…, kuma zai iya yiwuwa a samu canja siffar mutum da siffar Allah ban da zati, don haka duk sa’adda wata siffa (ta bawa) ta dauke ta gushe sai wata siffar (ubangijintaka) ta maye gurbinta, sai gaskiya (ubangiji) ya kasance jinsa, da ganinsa, kamar dai yadda hadisi mashhuri ya yi bayani, sai mutum ya yi tasarrufi a cikin halittu da abin da Allah ya so” [4].

Haka nan ne Mulla Ali ya rubuta a game da wannan lamarin yana mai cewa:

A lokacin ne sai bawa ya zama kamar fainsa (s.a.w) cewa: Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa surarsa, kuma matsayin surar abu shi ne matsayin fuska da inuwa daga hakikanin zatin abu da ma’abocin fuska da inuwa, kamar dai yadda imam Sadik (a.s) ya ce: Bauta Jauhari ce, badininta shi ne ubangijintaka. Da wannan ne ya yi nuni da matsayinsa a halarar ubangiji  yayin da ya ce: duk wanda ya gan ni to ya ga hakku (ubangiji), kuma imam Sadik (a.s) yana fada game da fadin Allah madukaki: duk wani abu mai halaka ne sai fuskarsa. Cewa; mu ne fuskar. Da wannan ne zamu ga alkiblar masu irfani sarkin muminai imam Ali (a.s) yana cewa: sani na da haske, shi ne sanin Allah. Domin matsayin haskensa (a.s) daga halarar zatin Allah yake, wanda yake zati ne na hasken haskaka mai rinjaye kan komai, kuma shi ne matsayin surar abu kuma fuskarsa[5].

Hakika ma’abota irfani sun yi magana a baitocinsu da kalamansu game da wannan lamari, daga cikinsu akwai sayyid haidar amuli yayin da ya rubuta musamman game da matsayin wilaya ta musamman a irfani yana mai cewa: wilaya ta musamman ita ce narkewar bawa a cikin gaskiya, waliyyi shi ne wanda ya narke a cikin hakku (ubangiji) kuma ya wanzu da shi.

Ba ana nufin narkewa ita ce rasa bawa baki daya ba, sai dai abin da ake nufi da wannan shi ne fuskacin da yake bawa zata narke cikin fuskancin ubangijintaka, domin kowane bawa yana da fuskacinsa a halarar ubangiji da ita ce aka yi nuni da ita a fadinsa maduakaki “Kowa yana da fuskacinsa da yake jibintarta”, aya. Wannan kuwa ba ya samuwa sai dai cikakken fuskanta zuwa ga janibin fuskacin ubangiji sake babu wani kaidi da sharadi, don da wannan ne fuskancin hakirkarsa ta ubangijintaka zan ta karfafa sai ta yi rinjaye kan fuskacin halittarsa har sai ta rinjaye ta, ta narkar da ita baki daya, kamar dai wata kwayar gawayi ce da aka sanya ta cikin wuta.

A bisa haka ne mutum kamili ya kasance shi ne mai alamta siffofin Allah baki daya, kuma idan mutum ya kai kololuwar kamalar karshe to zai iya kasancewa halifan siffofin Allah a duniya, domin siffofin Allah suna bayyana ga mutum a martabar narkewa. Wannan kuwa ba yana nufin magana ne kan ubangijintakar mutum ba, wannan yana nuna bayyanar alamtuwar Allah ne a mutum, wannan kuwa ba yana nufin sun hade da Allah ba, ko kuma mutum ya canja ya koma ya sauya zuwa ga Allah ba, kamar yadda muka yi nuni da haka a baya.

 


[1] Annazi’at: 24, da 25.

[2] Misbahus shari’a, s 7, mu’assasar al’a’alami lil matbu’at, 1400 k.

[3] Awalil la’Ali, j 4, s 103, manshurati sayyidus shuhada, kum, 1405 k.

[4] Mulla Sadra, Ikazun na’imin, s 58, anjamane hikmat wa falsafeye iran.

[5] Nuri, almaula Ali, ta’alikat alal mafatihul gaib, s 742, muassasar tahkikate farhangi.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Da”awar shi”a kan riddar sahabban mazon Allah {s.a.aw} bayan wafatinsa da wacce ma”ana sahabban su ka yi riddar? Shin wannan da”awa za ta iya karbuwa kuwa?.
    12161 Tsohon Kalam 2014/01/27
    samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
  • Mene ne ma'anar jagorancin malami?
    12834 Sabon Kalam 2012/07/24
    Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci. "Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu: 1- Wuraren da wanda ...
  • Shin mutum zai iya dawwama; idan haka ne, don me ya sa bai dawwama ba a duniya?
    11634 Sabon Kalam 2012/07/24
    Yana daga abin da yake jan hankli mai kyau a cikin kur’ani mai girma cewa yana ganin mutum wani halitta ne na sama madaukaki mai ‘yanci, kuma wannan jikin nasa ba komai ba ne sai wata sheka ta dan wani lokaci da ruhinsa ya fake a ciki ...
  • Menene hukuncin miji da mata wadanda suke kallon fim din blue fim a tare?
    6979 2018/11/04
    an tambayi daftrorin marja’ai masu alfarma kan tambayar da ka yi kuma ga amsar da suka turo. Ofishin mai girma Ayatullah sayyid Ali Khamna’i (Allah ya tsawaita rayuwarsa): Kalllon finafinai masu tada sha’awa na sa mutun ya karkata zuwa tafarkin shedan na son zuciya kuma yana raunana ...
  • WADAN NE BAITOCI NE ABBAS YAKE RERAWA A LOKACIN DA YA ZO DIBAN RUWA?
    11564 Sirar Manya 2012/07/26
    Mayaka yayin mubaraza a zamanin da su kan yi amfani da wani zaurance (don shaida juna ko ba da sako a tsakaninsu) don haka su kan rera baitotocin waka don samar da karfin gwiwa ga mutanensu da raunana abokan gaba. Imam (a.s) da mutanensa sun yi amfani ...
  • don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) amintacce?
    6189 تاريخ بزرگان 2019/06/12
    Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    14051 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • Wasu irin hadisai ne suka zo a kan Hukuncin dan zina?
    14544 Dirayar Hadisi 2012/07/25
    Ruwayoyi na musulunci daga annabi (saw) sun yi magana da bayyana hukunce hukuncen dan zina, za mu kawo irin babobinsu Gadon dan zina;- Babin cewa dan zina, shi wanda ya yi zinar ba zai gaje shi ba, da ita mazinaciyar, ko wanda ...
  • Ta wace hanya za mu iya kare kanmu daga kanbun baka?
    26372 Tafsiri 2017/05/20
    Kanbun baka na da tasiri a ruhin mutun wanda babu wani dalili da za a iya kore samuwar sa da shi, ballantana ma an ga faruwar abubuwa masu yawa da suka tabbatar da samuwar kanbun baka ko maita. Marigayi shekh Abbas Kummi ya yi wasici da a ...
  • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
    8568 Irfanin Nazari 2012/07/25
    Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...

Mafi Dubawa