Please Wait
26774
Bahasi kan alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) yana daga bahasosi masu zurfi da wuya ta wata fuska wacce tana bukatar karanta dukkan ruwayoyin da suka zo game da haka, sai dai abin da aka fahimta daga ruwayoyi –ko da kuwa a dunkule ne- shi ne kasa wadannan alamomin gida biyu:
Alamomin da suke na tilas: wadannan su ne alamomin da faruwarsu dole ne da suka hada da: Bayyanar Sufyani, Bayyanar Yamani, Tsawa daga sama, kashe Nafsuz Zakiyya, kisfe rundunar Sufyana a Baida, Bayyanar Dujal. Amma sauran alamomin su ba dole ba ne su faru, suna iya faruwa ko su ki faruwa.
Ko ma dai miye ana iya kasa alamomin gida hudu kamar haka:
a- Alamomin Zaman rayuwar al'umma: Wadannan su ne alamomin da za a iya cewa suna nuna yadda za a samu lalacewar wayewar dan adam ne da faduwar ci gabansa warwas.
b- Alamomin Addini da Akida: Su ne suke nuna rushewar addinin Allah da mayar da shi sama a kasa.
c- Alamomin Dabi'un Halittu: Wannan yana nuna yadda za a samu canje-canje a juyawar yanayi da zai faru a duniya.
d- Alamomin daidaiku da mu'ujizozi: Kamar tsawa daga sama, da kashe Nafsuz zakiyya, da sauransu.
Kuma kowanne daga wadannan nau'o'in akwai bayanin ruwayoyi da suka zo game da shi da bahasi dalla-dalla a littattafai da suka yi bayani kan hakan.
Bincike kan lamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) suna daga cikin mafi zurfin ilmi mai wahala, wannan kwua saboda ruwayoyi masu ywa ne da suka zo daga bangare biyu na sunna da shi'a da ma dukkan littattfai saukakku, da addinan da suka gabata da suka hada da kiristanci da yahudanci da zartutanci, da sauran addinai da mazhabobin Hindu, wanda lamari ne da yake bukatar bahasi da karatu da bayani cikakke, hada da cewa wadannan ruwayoyin ya kamata su kasance an yi dirasar su da bahasi na sanadi da na matani.
Abubuwan da za mu iya fahimta daga ruwayoyin da suak zo ta hanyar shi'a shi ne an kasa alamomin bayyana zuwa gida biyu na asasi, da suka hada:
1- Alamomin tabbas: wadannan su ne alamomin da tabbas sai sun faru ba tare da wani sharadi ba, wannan alamomin su ne; bayyanar sufyani, fitowar yamani, tsawa daga sama, kashe nafsuzzakiyya, kisfewa a baida da za a da rundunar sufyanai, fitar dujal.
2- alamomin marasa tabbas: wadannan su ne alamomin da za su iya faruwa amma bisa sharudda, idan wadannan sharuddan suka tabbata to wadannan alamomin zasu faru, in kuwa wadannan sharuddan ba su faruwa ba, to ba dole ba ne su wakana, kuma suna da yawa, da an yi nuni da su a littattafai masu yawa[1].
Sannan wadannan alamomin ana iya kasa su ta wata fuskar zuwa gidan hudu, da zamu yi nuni da su kamar haka:
a- Alamomin zaman rayuwar al'umma: wadannan a takaice muna iya nuni da su kamar haka –wadanda sun shafin rushewar rayuwar wayewar al'umma- kamar yadda zai zo:
- Yaduwar zalunci da danniya, wato duniyar zalunci da danniya.
- Lalacewar masu mulki: abin daake nufi da lalacewar masu mulki da zaluncinsu shi ne faruwar kungiyar siyasa da hukuma da zata doru kan zaluncin al'umma na zaman rayuwar al'umma, da siyasa, da al'adu, da tattalin arziki, kamar yadda masu hukunci za su doru kan tafarkin danniya da mulkin mamaya, da wuce gona da iri cikin tafiyar da al'amuran mutane, kuma yana da kyau mu kawo cewa wannan ba yana nufin duniya zata rasa mutane na gari ba ko hukuma mai adalci ba, sai dai yana nufi galibi mai yawa daga hukumomi zasu doru bisa fasadi da karkata da zalunci ne.
- Tsadar kaya da tashin farashin kayan masrufi da zai kai da rushewar tattalin arziki, wannan kuwa yana daga cikin sakamakon zaluncin wadannan kungiyoyin danniya masu ketare iyaka ne.
- Bayyanar makaryta da dujalai da suna kawo gyara cikin al'ummu.
Hakika bayyanar dujal tana daga alamomin da suke na tabbas, wadanda addinai da suka gabata ma sun yi nuni da su, dujal a ma'anar luga yana nufin mai boye gaskiay, da boye barna ta hanyar makirci da yaudara da surkulle, kuma dujal shi ne wanda yake yin wannan aiki, kuma abin da yake bayyhana daga ruwayoyin da suka yi magana kan sa suna nuna cewa bai kebanta da wnai mutum na musmaman ba, sai dai yana nuni ne zuwa ga wasu jama'a ko kungiya mai makirci, da yaudara, wacce take yaudarar al'umma suke gaba da kuma yin fada da gaskiya, suka shan gabanta, a yau masu masana sun fassara ma'anar dujal da yammacin duniya ta wannan zamanin[2].
- Mamayar kaskantattun mutane da makaryata da shashashai ga al'amuran al'umma da dukiyoyinta, da yin komai da sunanta, (sai sufyaniyawa su zama su ne masu tafiyar da kasa kuma jagorori).
- Karyata bayin Allah na gari da masu gaskiya, da ma'abota alheri daga mazaje, da nesantar da su daga fagen matsayi da mukamai a al'umma, da sanya makaryata da mayaudara a sama da gaskata su.
- Kuma daga cikin alamomn da suke na tabbas akwai bayyanar sufyani, kuma ba zai iya yiwuwa mu samu dalili yankakke ba na cewa shin sufyan mutum ne ayyananne ko kuwa yana nufin jama'a ce makira ja'aira azzaluma, sai dai lamarin da yake a bayyane shi ne cewa ko da sufyani ya kasance mutum daya ne ko wata kungiya 'yan jari hujja mai zalunci, ko mai danniya mai wawashe dukiyar talaka, ko kuma mai yada fasadi da bata da barna da camfe-camfe, da karerayi, dukkan wannan suna da wata sifa ta musamman wacce ita ce rusawa da lalatawa ga rayuwar al'umma da zamantakarsu[3], kuma wasu ruwayoyi sun yi nuni da kisfe sufyani da rundunarsa a Baida (wani wuri ne tsakanin makka da madina), kuma babu wani mutum daga cikinsu da zai tsira domin ya bayar da labarin faruwar wannan kisfewar ne ko ya bayar da labarinsa[4].
- Yaduwar yakoki da fitinu a duniya da zubar da jini: kuma ruwayoyi sun yi nuni da aukuwar yakokin Turkawa (wannan yaan nufin su wasu muatne ne daga zuriyar Turk dan Yafus dan Nuh, suna rayuwa a mangoliya, panjab, turkiyya, sibiriya, afganistan, hindu, kuam zai iya yiwuwa ma'anarsa ta yi fadi ta hada har da kasashen yammancin duniya[5].
Kamar dai yadda ruwaya ta nuna haka nan kuma kashi biyu cikin uku na mutanen duniya zasu halaka kafin bayyanar Imam Mahadi (a.s), kuma wannan yana daga cikin alamomin wadanda ba tabbas dole ne su faru ba[6].
- Faruwar juyi kan zalunci da fasadin duniya ta yanda wasu zasu samu nasarar kafa hukuma: daga cikin akwai juyin yamani wanda yake alami ne na tsayawa kyam gaba duk wani bata da barna, da kuma neman kawar da zalunci da tsayar da gaskiya da adalci a karshen zamani[7].
Wani misalin kuma shi ne gwagwarmayar Sayyid Khurasani da tsayuwarsa da adalci.
Wadannan gwagwarmayoyi guda biyu daya a yaman, daya kuwa a Iran, suna nuan mana daya daga cikin juyin da zai share wa Imam Mahadi (a.s) fagen bayyanarsa[8].
Kamar dai yadda aka yi nuni a cikin ruwayoyin da suka yi magana game da hukuma da za a kafa a Iran cewa zata kafu kan abu biyu ne; na farko: Kiran mutane zuwa ga musulunci da bin tafarkin Ahlul Baiti (a.s). na biyu: zata tsarkake wani yanki na duniya mai fadi daga zalunci da daudar fasadi har sai ta kai ga kufa, idan Imam Mahadi (a.s) ya bayyana, sai ya mika tuta zuwa gare shi, sai ta bi shi ta kasance cikin jama'arsa[9].
b- Sabuban Addini da na Akida: wadannan dalilai ne masu nuni zuwa ga rushewar addinin Allah da dawowarsa sama tana kasa.
An karbo daga Imam Ali (a.s) –yana mai nuni da alamar karshen zamani cewa- ya ce: Idan mutane suka kashe salla, suka tozarta amana, suka halatta karya, suak ci riba, suka karbi rashawa, suka tsawaita gini, suka sayar da addini da duniya, suka sanya wawaye a sama, suka yi shawara da mata, suka yanke zumunci, suka bi son rai, suka dauki lamarin zubar da jini saku-saku, hakuri ya zama ana ganinsa gajiyawa ne, zalunci kuwa abin alfahari ne, sarakuna suka zama fajirai, wazirai suka zama azzalumai, masana suka zama maha'inta, masu karatu suka zama fasikai, aka yi wa littattafai ado, aka kawata masallatai, aka tsawaita manarori (sai dai ba ta da wani abin a zo a gani), aka warware alkawura, son rai ya kawo sassabawa, da kuma…[10].
Da wani bayanin ana iya cewa mahukunta zasu yi watsi da addini kafin bayyanar Imam Mahadi (a.s) sai dai ba dukansu ba, wato sai dai mafi yawan su zasu kasance da wannan halin, kuma don haka ne ruwaya ta zo da cewa Imam Mahadi (a.s) zai zo da wani addini sabo. Wato abin nufi a nan shi ne musulunci zai samu hujumi da canji da karkatarwar mai yawa da yaduwar camfi da karerayi a cikin, da canja ma'anar fassarar kur'ani ta yadda za a yi masa karkatacciyar fassara, sai sanin sa ya zama ya yi wahala matuka, kuma a mance da hakikanin addini da gaskiyarsa[11].
c- Sabuban halitta: daga cikin alamomn bayyanar Imam Mahadi (a.s) akwai wadanda suak shafi sabuban halittar duniya na musibu da bala'o'in da zasu cika duniya. Kuma ruwayoyi masu yawa sun yi nuni da wasu daga cikin wadannan abubuwan wadanda daga cikinsu akwai:
Tsawa a karshen zamani, da kisfewar da kasfewa ba a lokutan da suak da suka dace ba, da samun canji a duniya, da canjin yanayin iska, da ruwa, da bullowar rana daga yamma, da… sauransu.
Kuma ya kamata mu kawo cewa wadannan ruwayoyin za a iya dabbaka wasu daga cikin su bisa tawilin abubuwan da suke faruwa a wannan zamani, alal akalla wasu daga cikinsu, kamar yadda malam shahid mutahhari ya yi yayin da yake kawo ma'anar bayyanar bullowar rana ta yamma da bayyanar musulunci a hannun Imam khomain da tasowarsa daga Faris[12].
d- Sabuban daidaiku da na mu'ujiza:
- Tsawa daga sama ka kira daga sama:
Daga cikin alamar da aka yi nuni da ce a ruwayoyi daga abubuwan da zasu faru kafin bayyanar Imam Mahadi ko kuma tare da bayyanarsa akwai alamar kira daga sama. Wato wani kira ne da mala'ika zai yi a sama yana mai yin albishir da bayyanar Imam Mahadi (a.s), yana kuma kiran mutane zuwa ga biyayya gare shi, kuma wasu ruwayoyi sun yi nuni da wannan mala'ikan da zai yi kira da bayyanar Imam Mahadi (a.s) da cewa shi jibril ne (a.s), kuma duk wanda yake duniya zai ji kiran sa, kuma kowa zai san shi da harshensa da yarensa, sai dai ba tare da sun san wurinsa ba…[13].
- Kashe Nafsuz zakiyya da shahadarsa:
Nafsuz zakiyya lakabi ne na wani yaro ko saurayi daga banu hashim mai matsayi mai daukaka, wanda zai fuskanci rundunar sufyani bayan nan sai ya samu mafaka a madina, yayin da rundunar sufyani zata kai madina sai shi kuma ya fuskanta zuwa makka yana kira zuwa alayen Muhammad (s.a.w), sai dai za a yanka shi tsakanin rukuni da makam ibrahimi ba tare da wani laifi ko zunubi ba da ya yi, sai shahadarsa ta tayar da hankulan mutane su koma hayyacinsu, sai su kai ga taruwa da zata kai da shiryawa don karbar bai'ar Imam Mahadi (a.s), tsakanin kashe shi zuwa yi wa Imam Mahadi (a.s) bai'a kwanaki goma sha biyar ne kawai, kuam shi nafsuz zakiyya shi ne wanda Imam Mahadi (a.s) ya aika wa mutanen da ma[14].
Bayan wadannan alamomin, akwai wasu alamomin masu yawa da wasu ruwayoyin suka kawo su[15].
[1] Bakir sharif alkarashi, hayatul Imam al'Mahadi (a.s), shafi: 304.
[2] Nasir makarim shirazi, mahadik ba inkilabe buzurg, shafi: 192. Mehnaz Shafayi, Dujal Afsaneye yo baki'iyyat, shafi: 28 – 62. Husain karmishhayi, farhange mau'ud, shafi: 92 – 94. Ibrahim amini, Dadgustari jahan, shafi: 223. Almukaddar ardabili, hadikatus shi'a, s: 758.
[3] Mahadiye inkilabe buzurg, shafi: 202. Almasa'ilul ashra fil gaiba, sheikh mufid, shafi: 90.
[4] Muhammad taki Rashid muhassil, najat bakhsh dar adyan, shafi: 159.
[5] Hadi kamil sulaiman, ruzgare rahayi, tarjamat Ali akbar Mahadi fur, j 2, shafi: 938 – 939.
[6] Habibul lahi dahir, simaye oftab, s: 511.
[7] Ali kurani, almumahhidun lilmahdi, shafi: 138 – 139.
[8] Sayyid asadullah shahidi, zamine sazimane inkilab jahane mahdi, shafi: 439 – 445.
[9] Faride kole Muhammad arman, khurshide muntaziran, shafi: 26 – 27.
[10] Biharul anwar: 52 : 193.
[11] Abdullahi jawadi amuli, wilayatul fakih, shafi: 372. Nasir makarim shirazi, mahdiye inkilabe buzurg, s: 320 – 321.
[12] Ruzgare rahayi, shafi: 853. Tarikhe maba'adaz zuhur, sayyid Muhammad Muhammad Sadik assadr, s: 164 – 217.
[13] Zandageye Imam Mahadi (a.s) s: 315. Ruzegare rahayi, s: 869 – 871.
[14] Faride gule muhammadi arman, dawus beheshtiyan, j 4, 167. Almasdar, albai'atul lillah, s: 268. Sayyid Ali asgar sadat madani, nishanihoye zuhur, s: 113.
[15] Almajalisi, biharul anwar, j 52.