advanced Search
Dubawa
5343
Ranar Isar da Sako: 2014/11/01
Takaitacciyar Tambaya
Bisa wane dalili ne zamu yarda ingancin Mu’ujizar Annabawa, ta yadda za’a banbantasu da kwararrun matsafa, da masu rufa-ido?
SWALI
Matsafa da masu rufa-ido, su kan yi abubuwa na ban mamaki, da suka saba al\'ada, misali, kamar shiga wuta da tafiya kan ruwa da makantansu. Tun da haka ne, to ta yaya zamu samu tabbacin cewa Annabawan sun bambanta da shahararrun matsafa da masu rufa-ido, ta yadda suma suke da\'awar gaskata abin da suke akai?
Amsa a Dunkule
Dalilin gaskata Annabawa a kowa ne zamani shi ne abin da karantarwarsu ta kunsa wadda don ita suke bayyana mu’ujizozi da kan gagari a kwaikwaya. Su wadannan mu’ujizozi suna daga cikin hujjoji bayyanannu da ke kiran mutane zuwa ga imani. Bayan haka akwai bambance-bambance na zahiri tsakanin abubuwa da suka saba da al'ada da kuma mu’ujiza, ta yadda za’a iya rarrabe su. Bambanci kuwa shi ne; shi tsafi tasirinsa na takaitacce lokacini ne, ita kuwa mu’ujiza tasirinta tabbatacce ne har abada.
 
Amsa Dalla-dalla
Domin amsa wannan tambayar za mu dubi batun ta bangare daban-daban da kuma samun sauye-sauye.
Tabbatuwar Mu’ujizar Annabawa
Da farko zamu fuskantar da wannan tambayar Shin mu’ujiza ita ce hanya daya tilo da zata tabbatar da gasgatuwar Annabawa wadda take kamaceceniya da ayyuka masu sabawa al'ada da ya yi kama da na matsafa a fuska ta zahiri?
Manyan dalilai da suke lazimtawa masu neman gaskiya bin tafarkin Annabawa (a.s) sun samo tushe ne daga koyarwar Annabawa ta ainihi., kuma ta dace da bukatun bil-Adama, domin ya kai ga samun kamala. Mu mun san cewa hakika koyarwar Annabawa (a.s) tun farkon kafuwar tarihi da isa matuka ta koli a bangaren Ma'arifa ita ta dora dan-Adam bisa turba. Sannan su masu adawa da Annabawa zaka samu dukkaninsu jahilai ne, azzalumai ne, da ba su da wata bukata ko manufa ta kaiwa ga kamala ta dan-adamtaka, babu inda suka nufa sai wuce gona da iri da zama saniyar-ware da yin dimuwa da zaluntar kai. A irin wannan yanayi ne wasu zababbun mutane suka bulla domin shiryar da jama'a, suka tunkari zalunci  da hakan ya zama dalilin tsirar jama'a a ko wane zamani. Mutanen kirki masu kama da su ke karbar jagoranci na Addini da dora jama'a bisa turba gadan gadan kai tsaye.  Sai dai ayyukan shiryar da mutane na hanun Annabawa Masu Girma (a.s), na haifar da manyan sauye-sauye  ta fuskar wayar da kai da fadakarwa.
Mafi yawa daga cikin siffofi da kamala da tarin ilimi da wadannan zababbun suke da su dan shiryar da mutane a gurin mutane gama gari, abu ne na ban mamaki da ya sabawa al'ada. Gani suke hakan ya samu ne sakamakon ikonsu wajen iya bayyana abu, da yawan iliminsu. Kuma babu banbanci hakan ya gudana a ilmuka na zahiri ko na badini haka ma dangane da ismarsu da rashin aikata zunubi da kashafi da suka samu na ganin boyayyun ababe na gaibi, da dimbi tasirinsu cikin lamura..... Amma duk da hakan fa a wasu lokuta na musamman bisa izinin Allah Annabawa (a.s) kan bayyana wata babbar mu’ujiza mai ban mamaki domin cika hujja ga mutane baki daya, domin kada a samu wata kafa ga masu yinkari ko jayayya. Ko kuma ya zamana suna taimakon mabiyansu ne ta wajen kare su daga sharrin azzalumai da yan cima-zaune, masu tsotsar jinin talaka, ta hanyar bayyana da dama daga cikin mu’ujizozi. Misali, irin wadanda Annabi musa (a.s) ya zo da su, kamar sakin maciji da ratsa Teku.... Ko kuma a ayyukan Annabi Isa (a.s) masu yawa irinsu warkar da marasa lafiya, da kuma tausayin mutane. Bisa zahiri idan ka dube su sai kaga su Annabawa (a.s) wata mabubbuga ce ta rahamar Allah da samar da baye-bayen da kyaututtukan  Allah (swt) ga bayinsa mabukata.   A she kenan dalilan da ke sawa muminai suke gaskata Annabawa (a.s), a tsawon zamani, shi ne koyawa jama'a abin da sakonsu ya kunsa kafin bayyana mu’ujiza ta Annabawa (a.s). Ita wannan mu’ujiza tana daga cikin bayyananun hujjoji da ke kiran mutane zuwa ga imani. A gefe guda kuma a duk sanda azzalumai da kafurai suka ga wannan mu’ujizar tilas gajiyawarsu ta bayyana. Maimakon Imani sai su kara tsunduma a cikin kafirci da inkari, kamar yadda irinsu Fir'auna da Lamarudu da Shaddadu da ire-irensu wadanda suka ga manyan mu’ujizozi su kai.
A she kenan kuskure ne mu dauki cewa dalililn yaduwar addini da bin sa shi ne ganin wasu abubuwa na ban mamaki da suka abku ta hannun wadannan bayin Allah managarta ba wadanda ba ko wane mutum ne zai iya yinsu ba, ta yadda ya zama mutane sun kasa fuskantar wadannan abubuwan, sun kasa kalubalantar su, ballantana su yi fito na fito da su!! Domin babu wani mutum da kan iya yin imani da wani addini bisa tilas ko ta hanyar barazana, sai ta hanyar gamsuwa da bincike mai zurfi na fahimtar wannan addinin. In banda wasu daga mutane (munafikai) da suka sami kansu a tsaka mai wuya suka ga ba su da wata mafita face su bayyana a zahiri cewa sun musulunta sun yi imani azahiri ba a zuciya ba.
2- Bambanci Tsakani Mu''ujiza Da Ayyukan Matsafa.
Bayan samun bambance-bambace na zahiri tsakanin ayyukan matsafa da bokaye da na Annabawa (a.s) da aka gani a matsayin mu’ujizozi suke kamar haka.
Na daya daga ciki shi ne: bayyana mu’ujizai inda ya dace a bayyanata[1]. Duk wanda ya rayu tare da Annabawan ya gan su yana samun wannan hadafin tare da su a yayin bayyana mu’ujizarsu. Ya yinda su matsafa suna yin nasu ne da nufin tallata kai da nuna gwaninta, ba tare da wata manufa ta addini ba, wanda tun asali ma shibci ne na shedana ko rufa-ido. Ga abin da Kura'ani ya bayyana dangane da matsafa. "A yayin da suka jefa sai Musa ya ce  abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle da sannu Allah zai lalata shi. Kuma Allah baya gyara Aiyukan mabaranata." [2]. Abin nufi shi ne, tasirinsa maiwanzuwa ne kawai na wani kakaitaccen lokaci kuma gwargwadon yawa ko wanzuwan tsafin ko bokancin.  A duk sanda aka kawo shi don karfafa wata da'awa to nan take sai ya lalace, Allah Ya ruguza shi, Ya kunyata masu yinsa. Sabanin mu’ujizar Annabawa da ba zata taba gamuwa da wani cikas ba har abada.
3. Wurin Amfani Da Mu’ujiza A Sakonnin Annabawa.``
Ya zama tilas mu tattauna wannan bahasin, wato menene ya sa Annabawa (a.s) suke amfani da mu’ujiza? Shin sukan kira dukkannin jama'a ne su bisu ta hanyar mu’ujiza? Ko kuma wani yanayi ko bukata kansa Annabawan (a.s) su bayyana mu’ujizar?
Muna sane da cewa mu’ujizozin Annabawa sun bambanta, ta fuskar dabbakasu da kuma baiyanasu. A musulunci mafi yawan hanyoyi da aka fi bi, su ne hanyoyin amfani da hujjoji na ilimi. Kawai a wasu gurene da ba su taka kara sun karya ba Annabi (s.a.w) ya yi amfani da mu’ujiza ta zahiri, a duk wurare da Alkura'ani Mai girma ya yi magana game da masu neman Annabi (s.a.w) ya bayyana mu’ujiza, zaka samu ba sun nemi mu’ujizar ba ne domin neman shiriya ba. Shi ya sa a lokacin ba su karbi abin da suka nema na mu’ujizan, rashin yarda da mu’ujizar shi ne kan haifar da tabbacin saukar azaba a kansu, a irin wadannan guraren da batutuwa, kamar yadda ya zo a Al’kur'ani:
"Mai tambaya ya yi tambaya game da azaba mai aukuwa*  Daga Allah take mai hauhawa ce* Mala'iku suna hawa da Ruhu zuwa gare shi a wani yini da kwatankwacinsa ya kai shekaru dubu hamsin* To ka yi hakuri hakuri mai kyau * Domin suna ganin can nesa * Mu kuma muna ganinsa nan kusa * Ranar da zata zama kamar narkakkiyar azurfa * Duwatsu su kasance kamar audugar rimi.[3]
To a nan zamu fahimci cewa Alkur'ani a ko da yaushe ya fi bawa bangaren hujja ta ilmi mahimmanci, a maimakon tilasta kafurai su yi imani ta hanyar mu’ujiza. Akwai wasu gurare na musamman da suke bukatar a lura da su. Wannan fagen wato na bayyana sakon Annabawa (a.s) ya gudana a dukkan addinai da aka saukar. Sai babbar mu’ujiza da ta zarce saura ita ce mu’ujizar musulunci. Mu’ujizar cikamakin Annabawa, (s.a.w) ita ce Alkur'ani, domin shi zance ne na Allah (s.a.w), sannan Littafi ne na sanin Allah.
 

[1] Dancikakken bayani a dubi lamba (989: da lamba 901, a littafin Isbaatul Ijaaz).
[2] Suratu Yunus; 81.
[3] Sutul Ma’arij; 1-9.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa