advanced Search
Dubawa
6658
Ranar Isar da Sako: 2014/10/06
Takaitacciyar Tambaya
Shin ya inganta a karanta kur\'ani ga matattu?
SWALI
Shin yana inganta a karanta kur\'ani ga wadanda suka mutu shin akwai hadisi da yake bayani kan hakan?
Amsa a Dunkule
Dangane da tabbatar da mustahabbancin karanta kur'ani ga mamata akwai nau'in dalili kan hakan guda biyu: nau'in farko shi ne  riwayoyi da suke gamammen bayani kan tunawa da mamata domin su mamata suna amfana da kyawawan ayyukanku sannan bayyanannen al'amari ne cewa karatun kur'ani yana daga cikin kyawawan ayyuka karbabbu.
An karbo daga manzon Allah (s.a.w) cikin fadinsa: kada ku manta da yan'uwanku da ke kwance cikin kaburbura, lalle su suna fatan kyawawan ayyukanku, lalle su suna raye suna kwadayin ayyukan alherinku domin su ba su da damar da ikon yin aiki, saboda ku yi sadaka da addu'a gare su.
Sannan kashi na biyu shi ne: riwayar da ta ke bayanin amfanin karatun kur'ani ga mamata misalin riwayar da aka karbo daga imam rida (a.s) ya ce: duk wanda ya ziyarci kabarin mumini to karanta suratu inna anzalnahu kafa bakwai kusa da kabarin lalle Allah zai gafarta masa tare da wanda ke kwance cikin kabarin.
 
Amsa Dalla-dalla
Gabanin tsunduma cikin bada amsa ya kamata mu tunatar da wani abu:
1- ma'anar mutuwa a mahangar muslunci:
Musulunci bai ganin mutuwa karewa da halaka ga mutum, ma'ana shi ne shi ruhin dan adam wanda bai taba karewa kadai dai yana rabuwa da fita daga gangar jiki wanda daga karshe ita gangar jiki ita ke rubewa shi ko ruhi yana nan yana ci gaba da rayuwar har zuwa wani iyakantaccen wa'adi  sannan daga baya aka hada shi ruhin da gangar jiki su ci gaba da rayuwa[1]
Allah madaukaki na cewa: sai suka ce shin idan muka bace cikin kasa zamu kara samu wata sabuwar rayuwar? Bari dai su sun kafirta da saduwa da ubangijinsu* ka ce musu mala'ilkan mutuwa da aka wakilta shi kanku  zai karbi rayukanku sannan zuwa ga ubangijinku zaku dawo.[2]
Annabin Allah yana cewa: fitar mutane daga duniya daidai yake da fitar jinjiri daga cikin mahaifiyarsa da ya rabu daga rayuwar duhun ciki da kuntata ya tsallako zuwa sarari mayalwaci mai haske.[3]
Imam ali (a.s) ya ce:  ya ku mutane mu daku an halicce mu ne domin wanzuwa da dawwama ba a halicce mu ba domin mu mutu, lalle ku ta hanyar mutuwa baku barin wannan duniya kadai dai kun tashi daga wani gida zuwa wani gida sabo. Saboda haka ya zama wajibi ku tanadi guzurin da zaka tsallaka wancan gida.[4]
An karbo daga imam husaini(a.s) ya ce: ita mutuwa wata gada ce da take daukeka daga matsalolin duniya, kamar yadda ta kasance ga makiyin Allah daga bukka zuwa kurkuku. [5]
Ayoyi da riwayoyi  na bada shaida kan cewa mutuwa da rubewar gangar jiki ba su cutar da ruhi  shi ruhi na wanzuwa yadda yake domin yanda ciki gashin kai akankin kansa domin hakikaninmu na tare da rai da ruhinmu ba wai gangar jiki da tsoka ba, mutuwa ba ta nufin shike nan komai ya kare labari ya ya zo karshe ita mutuwa bude wani sabon shafi ne na sabuwar rayuwa a wata sabuwar duniyar daban wanda dan adam zai ci gaba da rayuwarsa cikin ta.
Bayan mutuwa mutum na da wani hakki kan makusantansa  da sauran muminai daga cikin hakkin akwai yi masa wankan gawa  sanya masa likkafani  yi masa sallah binne shi sannan sauran wajibai da ake bisa bai ba lokacin rayuwarsa to ya kamata cikin sauri a sauke masa su, amma sauke wasu ayyyuka da suke mustahabbai ga mamata daga cikinsu akwai yin sadaka don shi karanta masa kur'ani da yi masa addu'a dukkanin wadannan mustahabbai  ne dangane da mamata.
 
Karanta Kur'ani Ga Mamata:
Dangane da tabbatar da mustahabbancin karatun kur'ani ga mamata zamu iya kawo nau'in dalilai guda biyu kai da sukai bayani kan hakan, nau'in na farko shi ne riwayar da bayani a dunkule take umarni da a dinga tunawa da matattu  ta hanyar kyawawan ayyukan dominsu suna amfana da wadannan kyawawan ayyukan sannan bayyanan abu ne cewa kur'ani na daga cikin kyawawan ayyuka.
1- an karbo daga manzon Allah (s.a.w) kada ku manta da `yan'uwanku dake kwance cikin kabari lalle suna fatan kyawawan ayyuaknku suna kwadayinsu kasantuwarsu ba su da damar yin wani sabon aiki kamar yadda ku kuke da ita, saboda ku yi musu sa daka da addu'a da karatun kur'ani.[6]
2 imam Sadik (a.s) yana cewa: mamamci  na yin farin ciki idan yaga ana nema masa gafara da arahama kamar yadda rayayye ke farin ciki idan aka ba shi kyauta.[7]
Kashi na biyu shi ne riwayar da ke bayanin tasirin karatun kur'ani ga mamaci, imam rida (a.s) yace: duk wanda ya ziyarci kabarin dan'uwansa ya karanta suratu inna anzalnahu kafa bakwai kusa da kabarin  to Allah zai gafarta masa tare da wanda yake cikin kabarin[8]
 

[1] Islamic teaching wallafar sayyid muhammad husaini tabataba'I sh 133 bugun daftarul intisharatul islami wanda ke jingine da jami'ul mudarrasin hauza ilmiyya Kum bugu na hudu shekara 1385
[2] Sajada aya 10-11
[3] Tarjamar littafin nahjul fasaha na abu kasim hadisi mai lamba 2645 bugun saziman cafi intisharatil jawidani.
[4] Irshad  sh 229, tarjamar muhammad bakir sa'idi  kurasani bugun intisharatul islamiya.
[5] Muhajjatu baida wallafar mulla muhammad muhsin  faizul kashani juz 8 sh 255
[6] Anwarul hidaya wallafar shaik hassan ali sh 115 bugun mabugar nu'umanu najaf
[7] Mahajjatul baida juz 8 sh 292.
[8] Biharul anwar wallafar muhammad bakir majalisi juz 79 sh 169, bugun manshuratul islamiya tehran.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa