advanced Search
Dubawa
8179
Ranar Isar da Sako: 2012/05/19
Takaitacciyar Tambaya
Me ya sa batun isma da biyayya ga imamai (a.s) da masu da’a bai samu gurbi ba kuma ba a tattauna batun ba zamanin imam Ali (a.s) da imam Hasan (a.s) kamar yadda aka yi a zamanin imam Sadik (a.s)?
SWALI
Me ya sa batun isma da biyayya ga imamai (a.s) da masu da’a bai samu gurbi ba kuma ba a tattauna batun ba zamanin imam Ali (a.s) da imam Hasan (a.s) kamar yadda aka yi a zamanin imam Sadik (a.s)?
Amsa a Dunkule

Zancen isma da biyayya ga Imamai Ma’asumai (a.s) an tattauna a kansu tun zamanin Manzon Allah (s.a.w). Sai da zamanin Imamu Sadik (a.s) ya bambanta da sauran zamuna nan sauran Imamai (a.s). Damar da ya samu ta fuskar zamatakewa da wayewa babu wani Imami (a.s) da ya samu wannan damar. Dalili kuwa shi ne, a lokaci da gwamnatin Banu Umayya ta raunana take tangal-tangal da karfafuwar ikon Abbasiyawa. Wadannan sassa biyun sun yi ta fafatawa lokaci mai tsawo a tsakaninsu. A gefe guda a zamanin Imamu Sadik (a.s) dama ta samu saboda hali da mulkin ke ciki sai ya zamana lokaci ne na farfadowar Musulunci da bunkasar ilimi.

Amsa Dalla-dalla

Zamu yi bahasi a batun isma da biyayya ga Imami ma’asumai (a.s) ta fuska biyu:

Na fako: Batun isma a zantukan Imamai (a.s):

Idan muka bi diddigi muka binciki nassosi da ke batu game da ismar Imamai (a.s) da yi musu biyayya, zamu ga akwai shi tun a farko-farkon zamanin manzanci a lokacin Manson Allah (s.a.w).

  1. Shafi’i ya ruwaito a littafin Manakib da isnadi zuwa ga Abdullahi bin Mas’ud ya ce: “Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Ni ne addu’ar Annabi Ibrahim (a.s).” Sai muka ce: “Ta kaka ka zama addu’ar babanka Annabi Ibrahim (a.s)? Ya ce: “Allah Ya yi wasici ga Annabi Ibrahim (a.s) “(ka ambata) zamanin da Ubangijin Ibramu Ya jarrabe shi da kalmomi ya ba da su cikakku Ubangiji Ya ce: “Hakika zan sanya ka abin koyi” Annabi ya ce: “Kuma ka sanya shugabannin nan daga cikin ‘ya’yana,” Ubangiji Ya ce: “Alkawarina na Shubanci ba ya samun azzalumai”.[1] Sai Annabi Ibrahim ya yi farinciki, ya ce: “Ya Ubangiji a zuriyata ma da akwai shugabanni irina? Sai Allah (SWT) Ya masa wahayi Ya ce: “Ya Ibrahim ba zan maka alkawari da ba zan cika maka ba. Ya ce: “Ya Ubangiji wane alkawari ne ba zaka cika mum shi ba”? Ya ce: “A cikin zuriyarka ba zan ba wa azzalumi shugabanci ba. A sannan sai Annabi Ibrahim ya ce: “Wane ne azzalumi a cikin zuriyata? Sai Ya ce masa: “Duk wanda ya yi sujjada ga gunki ya bauta musu ba Ni ba.” A sannan Annabi Ibrahim ya ce: “Ka nisanta ni da ‘ya’yana daga burin bautar gumaka, hakika sun badda mafi yawan mutane’.[2] Sai Annabi (s.a.w) ya ce: “Sai addu’ar ta iso gare ni ta iso ga Ali, a cikimmu babu wanda ya taba sujjada ga gunki, sai Ya zabe ni Annabi Ya zabi Ali wasiyyi”.[3]
  2. Kasim bin Kayis daya daga cikin sahabban Amirul muminina Ali (a.s) da Imamu Sajjad (a.s) na musamman ya ce: “ Ita da’a a kan yi ta ne ga Allah Shi kadai da ManzonSa da majibinta al’amarin da Allah Ya kusanta su a gare Shi da kanSa, inda Ya ce: “Ku bi Allah ku bi Manzo da ma’abuta al’amri daga cikinku. Allah Ya yi umurin da bin ManzonSa ne saboda ma’asumi ne tsarkakke kuma ba ya yin umurni a yi sabo, kuma Allah Ya yi umurni da bin ma’abuta lamari saboda su ma ba sa yin sabo kana ba sa umurni da a yi sabon Allah”.[4]
  3. A Nahjul balaga Amirul muminina (a.s) ya yi iShara game da batun isma:

A huduba ta 147 yana cewa: “Ba sa saban wa Addini, ba sa sabani da shi”.[5] Ba zai yiwu wani ya rasa sanin wani hukunci na Addini ba, balle ya samu sabani da masanin).

b. A huduba ta 131yana cewa bayan kore wasu sifofi ga buran Imamu Ali (a.s) ya ce: (s.a.w) “Ba mai watsi da hadisai ba ne, al’umma su halaka”.[6] A bisa dabi’a wannan na tabbatar da wajabcin biyayya ga Imami (a.s).

c. A huduba ta 105 yana cewa: Yaku mutane ku nemi haske da makamashin fitilar mai wa’azi da ya wa’zantu, ku kwankwada daga tataccen marmaro da ba ya gurbata.”[7]

Hakika an yi zantuka da dama da suka Shafi batun ma’asumai (a.s) a ruwayoyi a gurare daban-daban, amma zamu takaita a nan.

Na biyu: Dangane da dalilan da suka sanya yawan tattauna zancen akida a zamanin Imamai biyu watau Bakir da Sadik (a.s) fiye da a zamunan sauran Imamai (a.s) zamu bayyana a takaice. A bangaren siyasa, lokacin Imamu Bakir (a.s) musamman ma a lokaci Imamu Sadik (a.s) lokaci ne da gwamnatin Ummayawa ta raunana tana tangal-tangal, kana Abbasiyawa suka kara samun damar fada a ji. Kasantuwa lokaci ne da Umayyawa ke cikn tsaka-mai-wuya na siyasa ba su da wata dama ta tursasawa Imaman Shi’a (a.s) da cutar da su (irin lokacin Imamu Sajjad (a.s).

Sannan su Abbasiyawa sun daga tutar su ne da sunan kare Ahlin Annabi (s.a.w), da dauko fansar jininsu, kafin su hau kan mulki. A bisa kaskiya sun hau halifanci ne da wannan taken. Wannan shi ya sa babu wani tarihi da ya nuna an tursasa musu (a.s) a bangarensu a wanna lokacin. Wannan lokaci kyakkyawar dama ce ta yada ilimi da karantarwar Imamai (a.s). Kana daga cikin abubuwa da suka yi matukar tasiri a wannan batu (na akida) Sharuda na karantarwa na musamman da tattaunawa da sauran kunkiyoyi da mazhabobi na musulunci.[8]

 


[1] Bakara: 124.

[2] Ibrahim: 35-36.

[3] Sayyid Dawus, Aliyu bin Musa, a liffafin Dawa’if j1, sg78, daba’in Alkhiya’am.,Kum, 1400,HK.

[4] Salim bin Kayis Abusadik, a littafin Salim bin Kayis.sh884,, dabaa’in IntiShara’at Alhadi, Kum, 1415 HK.

[5] Nahajulbalaga zance na j1, sh 206 dabaa’in Darulhijra, Kum,

[6] A littafin da ya gabata sh153.

[7] A littafin da ya gabata 153.

[8] don karin bayani sai a dubi R.K: Imamu Mahdi, Siratul’a’imma, sh353, Mu’assasar Imamu Sadik (a.s) Kum,1415 HK.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa