advanced Search
Dubawa
16219
Ranar Isar da Sako: 2006/07/03
Takaitacciyar Tambaya
mene ne hadafin halittar dan Adam
SWALI
Mene ne hadafin samar da halittu? Ka kawo dalilai na hankali? Kuma idan hadafin shi ne neman kamala to don me Allah bai halicci dan Adam kammalalle ba.
Amsa a Dunkule

Allah madaukaki shi kansa samuwa ce da ba ta da iya ka ta ko wane bangare kuma y atattara dukkanin wani nau’I na kamala kuma samar da halittu tana nufin koraro da baiwa da ni’ima kuma hakika allah madaukakakin sarki mai yawan kwararo da baiwa ne, kuma kamalar wannan kyata ta sa ta wajabta ya halicci a bin da ya key a kamata a samar da shi, kuma samuwar ta zama ta dace shi, ita kuwa halitta da ma’anar samarwa baiwa ce ta Allah, shi kuma Allah Madaukaki mai kwararo da baiwar ne, cikar baiwarsa ne ya hukunta ya yi halitta ga duk abin da ya cancanci a halice shi din saboda halitta ta cancanta da shi.

Idan haka ne Allah madaukaki mahalicci ne saboda shi ne mai baiwa, wato abin da ake nufi da halitta da kuma ba da amsa idan an yi tambaya a kanta, ya buya ne cikin kasantuwar Allah mai kwararo da baiwarsa ne, tun da ya tabbata cewa siffofinsa ba sun fita daga zatinsa ba ne, to zai iya yiwuwa   a ce manufar yin halitta shi ne zatin Allah mai girma.

Hakika Allah ya halicci mutum a matsayin wani samamme da a badininsa ya kunshi wasu nau’o’I guda biyu, daya daga cikinsu ya fuskanci alheri da kyawawan aiki, dayan kuwa ya doshi sharri ne da kuma yin mummunan aiki, kuma a lokaci guda yana karbar kiraye-kiraye biyu da gyara da kiran annabawa ya zuwa ga alheri da gyara da kuma kiran shaidan ya zuwa ga sharri da aikata barna. Kamar yadda tattare da shi akwai dama ta iya cimma mafiya daukakar matakai na daraja da kamalar wanda ya yi halittar, sannan kuma yana da dama rikitowa kasa ya zuwa ga mafi kaskancin mataki na kasan tsanin nan na kamala.

Idan har mutum ya bi hanyar nan ta gaskiya duk da cewa yana da karkata ta dabbobi da kuma abin da yake kunshe da shi na kai kawo (wasiwasi) na shaidan da tarkunansa, to ta haka nan zai fifici mala’ika, saboda shi mala’ika ba a jarabce shi da wannan karkatar ta dabba din ba ballantana shaidan, amma zai fadi warwas ya zuwa ga darajar da take kasa da ta dabba, saboda ita dabba ba ta da wannan karkata ta ma’ana da take da ikon daukaka da iya irinta mutum.

Da a ce za mu kaddara cewa Allah tsarki ya halicci mutum tare da dukkanin kamaloli wadda zai iya yiwuwa   ya same ta, to wannan ba a ganinsa a matsayin samun kamala bisa zabi dangane da mutum din, sannan kuma tabbas Allah mai tsarki ya halicci ababen samuwa net un kafin ya halicci mutum kuma a irin yadda muka ambata, kuma duka suna a gare su.

Idan haka ne manufar halittar mutum tana tabbata ne yayin da ya zama yana da dama ta iya kaiwa ga kamala kuma ya zama yana kaiwa ga wadannan matsayan ne ta hanyar aikace-aikacensa bisa zabinsa.

Amma su kafitai da wadanda suke aikata sabo da zunubai da suke ci bayantar da su na kaiwa ga wannan kamala, to su din duk da rashin cimma manufar ta asali na halittar mutum wadda ita take misalta nufin Allah na shari’a, to su din take da hakanba sa zama masu saba wa manufar halittar a can tun asalin samuwar, saboda Allah mai tsarki ya so a bisa manufarsa ta samarwa ya sanya su masu ikon iya zabar fatarkin gaskiya ko kuma na barna.

Da a ce Allah ya sanya tafarkin barna da karkata ya zama ba zai yiwu ga mutum ba to imani da yin biyayya bisa nufi da zabi ga mutum zai zama ba shi da wata ma’ana.

Amsa Dalla-dalla

Domin tambayar ta fita sosai da sosai, tilas mu lura da wasu sashen abin nema:

Abin nema na farko shi ne: Manufar Allah mai tsarki ta yin halitta.

  1. Bisa hukuncin cewa Allah wajibul wujudi ne (wato samuwarsa tilas ce a hankalce), sannan bisa cewa samuwar tasa ba ta damfara da wata samuwa ba, to bisa wannan dalili ba ma zai yiwu kwakwalwa ta kawo cewa samuwarsa tana da iyaka ba a doron hakkinsa ko kuwa wata tawaya, kuma lallai ya tattaro dukkanin kamaloli.
  2. Daga cikin gungun kamalarsa ne cewa ya zama mai kwararo da baiwa da samuwa. Allah mai tsarkin a Kur’ani yana cewa: “Babu wani abin gudu a cikin kyautar Ubangijinka”.[1] Babu iyaka ga kyautar Ubangiji ta fuskancin Allah mai tsarki a kan haka duk wurin da ba a sami kyautar Allah ba to dalilin haka ya saura ne cikin iyakantuwar mai karbar da hukuncinsa ba, wait a fuskacin mai bayarwar da kwatarowar ba ne, domin duk abin da zai yiwu a ba shi to za a ba shi din.
  3. Tabbas duk wani alheri da kamala yana bubbugowa ne daga samuwa, haka duk wani sharri da tawaya ya mabubbugarsa rasi ne, saboda sharrori al’amura ne da babu su, musalin ilimi alheri ne kuma kamala ne, amma jahilci sharri ne kuma tawaya ne, haka nan iko a gefen Gajiyarwa da rashin dama su ma kamala ce kuma alheri ne, idan haka ne sanannen abu ne cewa samuwa alheri ce abin da yake daura da ita kuma na sharri da tawaya su kuma rashi ne.
  4. Bisa kallon mu ya zuwa ga matashiyar nan ta uku za mu san cewa kasantuwar Allah mai kwarariwa ne ga samuwa, haka nan yana tabbata ne ta hanyar halittar da samarwar. Idan haka ne tilas ne Allah mai tsarki ya zama mai kwararo da samuwa sabida shi ne mai yin halitta, da wata ma’anar daban. Idan har wani abu ya dace ya kuma cacanci a ba shi samuwa sai kuma ya zama Allah din bai samara da shi ba, to wannan ashin halitta shi din za a lissafa shi a matsayin rowa da hana alheri bis alura da cewa samuwa alheri ce, ita kuwa rowa ta koru a wajen ammai mai tsarki.
  5. Tabbas siffofin Allah su ne ainahin zatinsa, su din ba wai wani abi ne da ya karu a kan zatinsa ba, a yayin da su kuwa siffofin dan Adam da sausan da ma sauran jukkina daban sun karu ne a kan zatinsu. Misalin tuffa tana da zati kamar ja da zaki yana daga cikin siffofin wannan zati, amma wannan jan da zakin sun fita wajen zatin tuffa. Zai iya yiwuwa   tuffa ta siffantu da wasu siffofi daban kamar kore da tsami tare da tsayuwar zatin a kan halinsa na hakika.

Yin bincike game da zama abu daya tsakanin zatin Allah mai tsarki da siffofinsa bincike ne da ya shafi masu ilimin zance (ilmul kalam) mai zurfi da zai iya yiwuwa   mu koma da shi ya zuwa ga ilmul kalam din ko binciken tauhidi na sifa ga wanda yake son karin bayani.

Abin da yake babba a gare mu a wannan bigire shi ne kasantuwar Allah mai kwararo da samuwa ne, wanda shi ne manufa ta karshe na yin halitta da samarwa, ita ce sifar Allah ta zati sannan ita ce ainahin zatin ba wai karuwa ta yi a kan zatin ba. Idan haka ne da za a ce saboda me ya zama halutta ta zo daga Allah?

Za mu iya cewa: Saboda shi ne Allah. To idan haka ne manufa ta karshe a hakika shi ne ma’anar zancen masana falsafar mu na cewa: “Tabas dalili na karshe da kuka dalilu na aiki sun zama abu daya ne a cikin aikace-aikacen Allah”[2]. Kuma akwai tsammanin da zai yiwu mu iya amfanuwa da shi na wannan ma’ana daga sashen wasu ayoyi na Kur’ani,[3] kamar zancensa madaukaki da yake:

“Gare shi dukkanin al’amura suke komawa”.[4]

Abin nema na biyu a kebance hadafin Allah na halittar mutum, a duk zancen da ya gabata shi ne manufar nan dangane da asalin halitta da yanayi gamamamme, amma manufar mai aiwatarwa wajen halittar wani abu samamme na nau’in mutum, to yana da bukatuwa ya zuwa wata kebantaka kari a kan waccan manufar ta farko. Ita ma wannan kebantaka dangane da mutum tana aiwatauwa ne cikin kamala ta musamman wadda Allah yake nufi na halittarsa ta hanyar halittar mutum.

Karin bayani a kan wannan:- daga cikin abin da ya lazimta kasantuwar Allah mai kwararo samuwa ne ga kamala shi ne ya halicci kamala a duk inda zai yiwu, kuma kafin Allah ya halicci mutum din ya halicci wasu samammu da suna mala’iku da yanayin da Allah ya sanya su suke jin dadi da dukkanin kamalolinsu. Da zai yiwu su ji tun farkon halittarsu abin nufi dukkanin kamalolin su (mala’ikun) da suke da dama da ita a yanzu haka tun farkon halittarsu,

saboda haka irin wadannan halittu ba zai yiwu su iya samun kowane irin launi daga cikin launonin kamala ba, irin martabar da kamalarsu ba ta karbar karin kamalar ba, Allah madaukaki yana fada ta harshen mala’ikunsa ya na cewa:

“Kowane daya daga cikinmu yana da matsayi sananne, a cikinmu akwai wadanda suke cikin sahu, sannan a cikinmu akwai wadanda suke cikin tasbihi”.[5]

Ali amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce:

“Sannan ya rarrabu tsakanin abin da yake sammai madaukaka, sai ya cika su da mala’ikunsa hawa-hawa, akwai wadanda suke cikin sujjada ba sa ruku’u, wasu kuma cikin ruku’un ba sa mikwwa tsaye. Wasu cikin sahu ba sa zamewa, wasu kuwa cikin yin tasbihi ba sa gajiyawa”.[6]

su wadannan suna bauta wa Allah mai tsarki, wannan ita ce kamalar da Allah ya yi a gare su, sannan ba su da ikon su saba bin umarnin Allah.

Allah madaukaki ya ce:

Ba sa rigayar Allah da magana, su da umarninsa suke aiki”.[7] Mala’iku ba sa rigayar Allah da yin magana ba kuma sa saba masa yin aiki.

Haka nan Allah Madaukaki ya ce:

Yak u wadanda kuka yi imani ku tsairatar da kanku da iyalanku daga wutar da abin konawarta su ne mutane da duwatsu, a gefukanta akwai mala’iku masu tsanani da kaushi, ba sa saba wa Allah a kana bin da ya umarce su, kuma suna aikata duk abin da ya umarce su”.[8]

Saboda kasantuwar Allah mai kwararo da samuwa ne, sai yayinufin ya halicci wata kamalar daban kari a kan kamalar da take ga mala’iku, ita wannan kamalar ita ce zabin da mutum yake da shi. Abin da ake nufi shi ne cewa zai halicci wani abin halitta samamme da zai iya samun wadannan kamalolin bisa zabinsa da ‘yancinsa, saboda haka sai ya halicci mutum, wanda bai mallaki wata kamala da ta cancance shi ba a farkon halittarsa, amma an halicce shi da wani yanayin da saboda shi yana da ikon iya kaiwa ga wadancan kamaloli ya isa ya zuwa wadancan martabobin.

A bayyane yake karara cewa duk kamalar da mutum zai iya kaiwa gare ta ya iya cimmata ta hanyar zabinsa bisa cikar ‘yancinsa ita ce mafificiyar kamala da aka ba wa mala’iku tun farkon halittarsu a lokaci guda.

Amirul muminina Ali amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce:

Tabbas Allah ya sanya wa mala’iku ba tare da sha’awa ba ya sanya wa dabbobi sha’awa ba tare da hankali ba, amma sai ya hada wad an adam duka biyun. Duk wanda hankalinsa ya rinjayi sha’awarsa sai ya zama ya fi mala’ika alheri, wanda kuwa sha’awarsa ta rinjayi hankalinsa to ya fi dabba sharri”.[9]

Malam Maulawi ya dau wannan ma’ana sai ya tsara waka a cikinta yake cewa:

*Lallai Allah ya halicci duniya a bisa nau’i uku

*A tattare su ne hankali da ilimi da samuwa. Wadannan su ne mala’ikun da ba abin da suka sani face yin sujjada.

*Son raid a karkacewa da samuwa a halitta kadai haske ne marar kaidi da yake rayuwa ta hanyar shakkun Allah.

*Wani mugun daban kuma ba su da wani rabo na ilimi.

*Su ne dabbobi wadanda suka shagaltu da abincinsu kawai.

*Ba sa ganin komai in ba karmami da ciya yi ba.

*Ita babba ta rafkana daga samun tsiyatuwa ko arziki.

*Na ukun shi ne mutum dan Adamu rabinsa mala’ika ne rabinsa dabba.

*Babangarensa na dabba yana kai shi zuwa faduwa.

*Yayin da daya bangaren yake kai shi ya zuwa ga daukaka da yin sama.

A duk sanda daya daga cikin wadannan mafuskanta biyu suke neman rinjayar daya, sa sannu dai yakar juna za ta tabata a tsakaninsu.

Idan haka ne manufa da ita ta karshe na halittar mutum ita ce kasantuwar Allah mai tsarki mai kwararo da samuwa ne daga cikin abin da ya lazimci kasantuwar Allah mai kwararo da samuwa ne, shi ne da ya halicci wannan nau’I wanda zai yiwu na daga nau’o’in kamaloli, wannan kamalar nau’o’in kamaloli.

Abin nema na uku: Saboda me Allah bai halicci mutum bisa kamalarsa ba?

Bisa waiwaye ya zuwa abin da ya gabata na bincike zai iya yiwuwa   mu ce manufar halittar mutum zai iya tabbata ne a cikin da mutum ya mallaki iya karbar kaiwa ya zuwa ga kamala, kuma cewa zai iya samun wannan kamalar ne ta hanyar aikin da ya yi bisa zabinsa, da za mu kaddara cewa ya sami wannan kamala tun farkon halittarsa, to kai tsaye ba za a lissafa wannan cikin kamalar da ya samu bisa zabinsa ba. To hadafin halittarsa ta asali da bai tabbata ba.

Tilas ne mu lura da cewa daukakar da mutum yake iya kaiwa na wata daraja kwaya daya ta tsanin neman kamala, shi ake lissafawa a neman kamala ta zabi dangane da mutum, shi ne tabbatar da kuma kaiwa ga hadafi na asalin halittarsa, ko da kuwa ya kasance ya kai ga wani gwargwado na daukakar ne na wani bangare.

Abin nema na hudu: Mutum da yake kafiri da mai sabo, idan mutum bai kai ga wata daraja ko da kwaya daya ba a tsanin neman kamala, ya zama ya kashe dukkanin lokacinsa a cikin kafirci da sabo da tsururutar zunubi, to irin wannan mutum duk da haka ba ya fita daga manufar nan ta halitta. Saboda shi ma ya isar da rayuwar tasa ya zuwa ga aiki sabida shi mutum yana da damar ya yi kasa ya zuwa ga darajar nan ta faduwa, domin hakika Allah ya halicce shi da yanayin da ta hanyarsa zai yiwu ya zabi tafarkin alheri da kamala, ko kuma ya zabi tafarkin tsiya da yin kasa. Idan haka ne har ma mutumin da yake kafiri da mai aikata zunubi da ya iya yin wani motsi sabanin abin da Allah yayinufi tun a can asalin samuwarsa.

Na’am, tabbas Allah mai tsarki yana son mutum ya daukaka ya sami kamala ya kuma gode masa, ba ya sonsa da ya sami faduwa ko ya yi abin da bai yarda da shi ba.

Da wata fassarar daban: Tabbas Allah a cikin halittar mutum yana da wasu nau’o’in manufofi guda biyu:

Manufa ta samarwa da kuma mamanufa ta shar’antawa. Manufa ta samarwa tana aiwatauwa ne wajen ba da dama da yiwuwa   ga dukkanin mutum na sadar da damarsa da tanade-tanadensa ya zuwa martabar nan mai kyau ko mummuna.

Amma dangane da manufa ta shar’antawa kuwa ita ta takaita ne wajen nufinsa na lallai mutum ya bi tafarkin nan na samun kamala ya isar da damar nan tasa ta gini a kan abin da ya gabata, zai yiwu mu ce lallai mutum mumini na iya tabbatar da manufar nan ta Allah ta shari’a kari a kan mashigar nan tasa na tafarkin hadafin nasa na samuwa. Amma shi kafiri da mai sabo, to shi idan har bai tabbatar da manufar nan ta shari’a ba to ya fita daga tafarkin nan na hadafin samar da shi.

Fadakarwa:

Akwai wani zance da bai gushe ba a cikin binciken tun da akwai ruwayoyi da yawa a wannan fage, amma mu za mu tsaya a wannan iyakar don kafuwa ga kwadayin mai tambaya ta karkatarsa, da kuma nisantarmu da yin bayanai filla-filla sama da abin da muka kawo.

 


[1] Suratul israi aya ta 20.

[2] Tafsirul mizan na daba-daba’I juzui na 8 shafi na 44.da kma maariful kur an na ayatollah I misbahu yazdi. Juzu’I na 1 shafi na 154.

[3] Surar bakara aya ta 210. Sutrar ali imrana a ya ta44. Da anfal aya ta 67 da fadiri a yaa ta 4 da hadidi a ya ta 5.

[4] Surar hudu aya ta 123.

[5] Surar ssaffati aya ta 164, 166.

[6] Hanjul balaga bugu na daya.

[7] Surar anbiya ‘I a ya ta 27.

[8] Surar tahrimi a ya ta 6.

[9] Wasa’ilush shi’a judui na 11 shafi na 164.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa