advanced Search
Dubawa
18359
Ranar Isar da Sako: 2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
Yaya tsarin mazhabobin sunna hudu yake a wajan ma’abotansu ahlus sunna, kuma a yaushe aka rufe kofar ijtihadi?
SWALI
Yaya tsarin mazhabobin sunna hudu yake a wajan ma’abotansu ahlus sunna, kuma a yaushe aka rufe kofar ijtihadi? Shin akwai wanda ya bude kofar ijtihadin ko kawai sunayensa ba tare da an bude ba?
Amsa a Dunkule

Musulmai tun bayan tafiyar manzon allah (s.a.w) sun rabu zuwa bangarori biyu;

a- bangaren farko sun tafi kan cewa za a dogara da ahalin gidan manzo (s.a.w) da komawa zuwa gare su wajan ilimin fikihu da sauran iliman addini da na ryuwa

b- daya bangaren kuma wannan matsayin na sahabbai ne da tabi’ai,

magana tsakanin wadanna bangarori ta ci gaba da habaka har ma ta samar da abubuwan tattaunawa muhimmai saboda zuwan sababbin abubuwa musamman bayan bude garuruwan musulunci da bayyanar sababbin mas’alolin musulunci, har zuwa tsororuwar tsarin fikihun da zamansa a kujerar mazhabobin sunna hudu kamar yadda suke a yau kofofin ijtihadi a bude suke wajan ahlus sunna a wannan lokaci har suka zama tarihi saboda wasu dalilai masu yawa, da malaman mazhabobin suka samu da tsanantawar masu mulkin wannan lokaci ta rashin barinsu su kare matsayin mazhabobinsu ko da kuwa a gwamnatance, daga nan ne aka rufe musu kofar ijtihadi aka sa su yin ijtihadi karkashin mazhaba daya.

A lokacin ne wasu daga masu mafarkin su yi tunanin cewa ya kamata a ce an dawo da fikihu ransa don bunkasa shi da ci gabansa ko da kuwa bude shin ya zama karakshin mazhaba daya daga mazhabobi hudun.

Amsa Dalla-dalla

Hukunce hukuncen shari’a sun fara ne tun daga aiko manzo (s.a.w) zai kuma yi ta ci gaba har tsawon zamanin sa, Shi’a sun tafi kan cewa bayanan sunna da fayyace abin da shari’a ke nufi da tarihin manzo (s.a.w) tare da hadisansa da bayanin hukuncin shari’a na fikihu da wanda ba shi ba duk ya doru kan wuyan ahalin gidan manzo (s.a.w), sunna kuma sun tafi kan cewa duk wadannan abubuwa na kan sahabbai gami da shiryar da al’ummar musulmi bayan rayuwar manzo (s.a.w), sahabbai sun sha wahalar bayanin hukunci da ayyuukan fikihu tare da fitar hukuncin shari’a daga sunna mai girma har zuwa shekara ta 40 H, wannan ba ya nufin karewar zamanin sahabbai wasu daga sahabbai sun wanzu har zuwa bayan wannan lokacin sai dai kuma mafi yawan masu fatawar fikihu a wannan lokacin ba sahabbai ba ne, bayan lokacin sahabbai sai aikin ya kama kan tabi’ai wanda shi ne ya ci gaba har zuwa karshen karnin farko na hijira zuwa karshen karni na biyu.

 

ZAMANIN BAYYANAR MAZHABIN SUNNA HUDU (4)

Bayan makarantun ahalus sunna sun yi watsi da jagorancin Ahlul-baiti (a.s) imamiyya sai suka kagowa kansu wata hanya daban wacce ba ta Ahlul-baiti (a.s) ba, ta yadda suka koma wa sahabbai wajan fikihun su bayan sahabbai kuma suka koma zuwa ga tabi’ai.

Yayin da fikihu ya fadada tare da yawan sababbin mas’aloli musamman ma bayan kara samun sababbin garuruwan musulunci da bayyanar sababbin mas’alolin fikihu da bukatar zurfafawa a cikinsa, wannan ya faru ne tun daga farkon karni na biyu har zuwa karni na hudu, wanda shin daga nan aka samu daukakar rabuwar mazhabobin sunna hudu wadanda su ne har zuwa yau. Bayanin faruwar mazhabobi hudu ya faru ne saboda yawan sababbin mas’alolin fakihu da mutane ke musamman ma al’umma da suke sababbin shiga musulunci sannan kuma a gefe guda matsayin siyasa na taka tasa rawar wajan kara daukaka wadannan makarantu domin nesanta mutane daga makarantun Ahlul-baiti (a.s), domin nesanta mutanen daga makarantun Ahlul-baitiin shi ne a bawa masu mazhabobi dama tare da zamar wa mutane makwafin Ahlul-baiti da su wajan ba da mas’aloli, don cimma wannan buri shi ya sa aka daga mazhabobin, duk da cewa mazhabobin sunna ba sun takaita da hudu ne ba tun farko akwai mazhabobi da yawa da suka yadu a map din musulunci wadanda ba wadancen hudun ba, kamar mazhabar hasanul basary 23-110 H, wacce aka fi sani da mazhabar zahiry da mazhabar Muhammad bin jarir attabary 220-310 H, akwai dalilai da yawa da suka taimaka wajan kaiyade mazhabobin zuwa hudu kamar yadda suke a yanzu.

DALILAN TOGACE MAZHABOBI ZUWA HUDU (4)

Mazhabobi sun yawaita a wajan ahlus sunna sabubbansu da kuma yadda kowace mazhaba ta doru a kai hakan ya haifar da banbance banbance mai yawa tsakanin mazhabobin don haka sai mafiya yawan mutane suka yi kwadayin a ce a togace wannan da wasu daga cikin mazhabobin wannan ke nan ta wata fuskar, a wata fuskar kuma akwai taka rawar hukumomi a ciki wajan takaice wadannan mazhabobi da guda hudun domin mutane ba su da ikon iyakance su da hudu ko kuma batar da wata da maye gurbinta da wata wadanda ke da damar taka wannan rawa su ne hukumomi da sarakuna masu madafin iko mafi girma. Duk da kamar yadda ya zo mun ga wasu daga hukumomi sun takaice mazhaba daya ne kawa zaka ga malamin mazhabar shi kadai ke da damar yada mazhabarsa kamar yadda yake so a gefe guda kuma zaka ga hukumomi na kuntata wata mazhabar ba sa ba su damar motsi ko gudanar da ayyukansu ko fadar ra’ayinsu na fikihu, misali; abu yusuf da aka fi sani da kadhil kudhat ya samu dama sosai wajan sarakunan abbasiyawa domin yada manufarsa da yada mazhabar hanafiyya yadawa mai fadin gaske ya cika garuruwan musulmi da mazhabar hanafiyya. Haka abu yusuf ya cika dama ga masu hanafiyya da malamansa wajan yin hukunci da hanafiyya hatta wajan alkalanci.

MALAMAN MAZHABOBI HUDU

1-ABU HANIFA (NU’UMAN DAN SABIT) 150ah

2-MALIK DAN ANAS 179ah

3-MUHAMMAD DAN IDRIS 204ah

4-AHMAD DAN HAMBALI

DALILAN (SABUBBAN) RUFE KOFAR IJTIHADI A MAKARANTAR SUNNA

Babu wani mutum da ke kokwanton muhimmancin ijtihadi domin ya zamo tamkar wata jijiya mai sadar da jini zuwa sassan jikin musulunci domin bunkasa motsi da rayuwarsa daidai da zamani, wannan al’amari na rufe kofar ijtihadi ya sanya mutane sun zauna har zuwa karnin sha hudu suna cikin dokoki da shari’o’in da ba na musulunci ba, kofar ijtihadi ta zamo a bude har zuwa shekara ta 665ah a cikin sunna sai dai babu wasu daliali da sabubban da suka bunkasa sauran mazhabobin da ba da fatawa ga mazhabobi hudu kawai, tare da hana mabiya sauran mazhabobin dama don gudanar da nasu a gwamnatance kamar alkalanci, limanci, limancin juma’a, ba da fatawa da sauran su, ba a ba wa kowa wannan damar da sai daya daga mazhabobi hudu domin yin saddu ga sauran mazhabobin da ba a yarda da su ba, amma illoli da sabubban da suka sanya sunna dawo da ijtihadi kai tsaye muna iya fadar kadan daga ciki kamar haka;

1- BANGARANCIN MAZHABA

Babu kokwanton cewa mabiyan kowane malami na yin son kai da bangarancin ra’ayinsa bangaranci mai tsanani kuma ba sa la’akari ko kula da wanda ya saba da nasa ko kadan. Wani daga manyan Shi’a ya yi nuni da wanna yana cewa: Daga dalilan da suka sanya rufe kofar ijtihadi a sunna su ne tsayar da bunkasar da mazhabin shi’anci yake domin kuwa bunkasa kishiyarsa ta hanyar habaka ta da nuna girman masu ita da kara daga mutumtakarsu har ma da iliminsu a wajan mabiyansu wannan aiki ya ci gaba da taka rawa har zuwa bayan rayuwar malaman mazhabobin hudu (kamar yadda muka kawo a sama) wannan kambamawa da aka yi musu wacce ta wuce gona da iri shi ne ya sanya mabiynsu ke fargabar kusantar yin gyara ko a cikin hukuncinsu balle su saba, wannan ya hana su yin istinbadi a cikin mazhabobin su

2-ZUWAN SABABBIN ABUBUWA CIKIN ALKALANCI

Yayin da ya zamo malamai ne ke da damar alkalanci da fitar da hukunci (tsari) a cikin mutane, sai ijtihadin kowanne a cikinsu yake sabawa da na juna, sai kowane daya yake hukunci tsakanin mutane daidai da ijtihadinsa ba tare da yana lura da na sauran malamai ba, har ma yakan wuce gona da iri da suka mai tsanani ga duk wanda ya saba wa nasa ra’ayin wannan sai ya haifar da rashin daidaito a hukunce hukunce tare da samun sabani daban daban a kan abu daya, daga nan sai hukuma ta hana malamai hukunci kai tsaye ta hanyar ra’ayoyinsu ta sanya musu cewa hukuncin kowane malami a alkalanci da sauran abubuwa dole ya yi daidai da fatawar daya daga malaman mazhabobi hudu

3-FAGEN SIYASA

Sananne ne cewa tushen kowace hukuma a wannan lokaci na tsoron ci gaban tunani da daukakar ilimin malamai da masana fikihu, domin zurfafawar na iya taimaka musu wajan gano dalilan da zai iya takawa hukumar birki da hana ta taka rawar gaban hantsi wajan danniya da zalunci wanda kan iya hana hukumar jin dadi don haka sai suka dakusar da malaman zuwa wannan tunani, abin nufi da rufe kofar ijtihadin ba wai gaba daya ba a’a an iyakance ijtihadin ne kawai gwargwadon abin da yake a mazhabobi hudu ta yadda mai ijtihadi zai yi amma karkashin mazhabarsa kadai ya dora a kan abin da ya yi daidai da hakan ba tare da ya saba mata ba. Amma ijtihadi kai tsaye shi ne aka kulle tun bayan kayyade mazhabobin zuwa hudu kawai

KOMOWAR MAZHABOBIN SUNNA ZUWA IJTIHAD KAI TSAYE

Wasu daga masu hasashe (9) da marubutan zamanin da yawa sun bayyana komowa yin ijthadi kai tsaye don dawowa fkihu ransa na ainihi kuma domin ya zamto kayatacce mai tafiya daidai da zamani da cigabansa dukkan wadannan marubuta da masu hasashe sun nemi a dawo da ijtihadi kai tsaye ba kawai a mazhaba daya ba, a’a ya zamanto ya zamo malami na da damar yin fatawa kai tsaye kuma a cikin kowace mazhaba tsakanin mazhabobi hudun, wannan bukata tasu ba ta cimma samun nasara ba duk da kulawar manya a ciki saboda wasu uzururruka fararru da suka haifar da bukatar yin ijtihdi kai tsaye,      daga nan ne masu bukatar komowa zuwa ijtihadi kai tsaye ke tambayar shin mene ne dalilin da zai sa mutane sai sun yi koyi da komawa zuwa wadanda sun rayu tun karnonin da suka gabata wajan aiki da hukunci kan abubuwan da sababbi ne su kansu ba su san su ba, suke kara tambayar cewa; idan takalidi wajibi ne ga kowa mai ya sa za a takaita wadanda za a yi takalidin da su zuwa malaman mazhabobi hudu kacal ko kuma a dora wa mutane ra’ayin waninsu, kuma su malaman mazhabobin da wadanne malamai suke koyi har da su ma za su zama ababan a yi koyi da su. A takaice dai abin da ya faru shi ne, adadin masu kira da cewa a bude kofkr ijtihadi ya zamo yana karuwa a kullum har ta kai su ga samun damar rushe ka’idar rashin ijtihadi kai tsaye zuwa bude ijtihadi kai tsaye.

Tambaya ta 796 ijtihadi a wajan Shi’a (maukiiy: 855)

Tambaya ta 795 ijtihadi cikin kur’ani da ruwayoyi (mauki’iy: 854)

Tambaya ta 493 sakon bayanan mazhabobi (mauki’iy: 5182)

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa