advanced Search
Dubawa
7371
Ranar Isar da Sako: 2006/05/17
Takaitacciyar Tambaya
Yaya aka samu tunanin akidar Rashin addini mai cewa siyasa daban take da addini?
SWALI
Yaya aka samu tunanin akidar Rashin addini mai cewa siyasa daban take da addini?
Amsa a Dunkule

A lokacin samun canjin turan kiristoci sun samu matsala da ta kai su ga cewa addini yana da tawaya, kuma ba zai iya biyan bukatun mutane sababbi ba a fagen siyasa da zaman tare, don haka sai suka kai ga tunanin raba addini da siyasa.

Sai aka samu baruwan addini da siyasa a matsayin tunani mai ci a yammancin duniya, domin an samu karkacewa a tafarkin addini da suka samu, wanda yake cike da son rai da tsakude, da wannan ne ya kasa amsa bukatun al’umma.

Amsa Dalla-dalla

A zamanin sabuwa haihuwa (sabon zamani)[1] na tsakiyar karni na sha biyar miladiyya ne aka fara samun tunanin Rum da Yunan na da a cikin yammancin duniya, sannan kuma a zamanin samun gyara da canji[2] a karnin na sha shida aka samu kafa shi ta hannun ma’abota addini kamar Luta, don haka a lokacin wayewa[3] a karni na 17, da 18 miladiyya sai ya samu gudanawa da kama wuri ta hanyar tunanin amfani da hankali da binciken ilimi. Kiristoci sun fuskanci cewa kiristanci yana da tawaya ba zai iya biyan amsoshin wannan zamanin ba da suka hada rayuwar al’umma, ala’adu, siyasa. Don haka ne suka shelanta cewa addini ya zo ne kawai don nuna alakar mutum da Allah da lahirarsa, ba shi wani abin cewa a fagen siyasa da rayuwa, kuma da wannan ne aka samu yaduwar tunanin raba addini da siyasa, da musanta komawar mutne zuwa fagen addini yayin da suke da tambayoyi kan al’adu da siyasa da rayuwa, sai aka samu bayyanar malaman falsafa na cire addini[4] suka rika zuwa daya bayan daya.

Bisa la’akari da aibn da aka samu game da tunanin kiristanci ana iya cewa akidar cire addini ta samo ne daga ci gaban yamma , domin muna gani a fili sakamakon karkacewar koyarwar addini da bin son rai da ya samu kiristanci ne da aka cakuda su da koyarwar addini sai ya zama ba zasu iya biyan bukatun dan adam ba a kowane zamani, don haka sai addinin isa (a.s) da ba shi ne addinin karshe ba kuma isa (a.s) bai taba da’awar cewa babu wani Annabi (a.s) bayansa ba, ya ma karfafa cewa akwai “ahmad” da zai zo bayansa (a.s).

Amma musulunci addinin karshe ne kuma ya samu kariya daga karkacewa, don haka ba shi da matsalar da ta samu kiristanci taraba addinin da siyasa, sam wannan bisa hakan ba shi da wani wurin zaman a addinin musulunci, sai aka samu wasu masu neman kwaikwayon yammacin duniya suna maimaita irin wadannan maganganun suna masu zaton cewa idan suka kawo wannan tunanin zasu iya sanya duniyar musulmi ta samu ci gaba ne. misali akwai Dr. Jabir Usfur a abin da ya rubuta a mukaddimar  littafin “al’islam wa usulul hikam” -da Ali Abdurrazaka ya rubuta- yana cewa: mu muna alfahari da mutane kamar Dahdawi, Muhammad Abduh, da Ali Abdurrazak, kuma da su ne muke koyi, domin sun kasance masu goyon bayan ci gaban wayewar wannan zamanin.

Karin bayani:

1. Mahdi Hadawi tehrani, wilayat wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

2. Mahdi Hadawi tehrani, bawarho wa fursish’ho, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na daya, 1378.

 

 

 


[1]Renaissance.

[2]  Reformation.

[3]  Enlightenment.

[4] Secular.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
  8281 Tsare-tsare 2012/07/24
  Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
 • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
  14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
  Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
 • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
  12493 2019/06/16
  dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
 • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
  17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
  Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
 • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
  7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
  Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
 • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
  6470 Tsare-tsare 2012/07/24
  Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
 • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
  6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
  Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
 • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
  14494 Tafsiri 2012/11/21
  Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
 • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
  15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
  Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
 • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
  8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
  Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa