advanced Search
Dubawa
9449
Ranar Isar da Sako: 2012/07/25
Takaitacciyar Tambaya
mu mun yi imanin cewa dole ne ma’asumi ya zamanto ya baranta daga duk wani nakasu na zahiri da na boye. Bisa la’akari da haka shin hadisan da ke magana a kan gajertar Imam Ali (a.s) sun kuwa inganta?
SWALI
shin hadisan da ke magana kan gajertar Imam Ali (a.s) sun ko inganta? Ko ita gajerta ba nakasa ba ce? Domin ko da yaushe mukan ji an ce ma’asumi ya baranta daga kowane irin aibi har na zahiri.
Amsa a Dunkule

Domin mu yi  bayyanin  madu’in, zamu yi zance kan mas’alar ta bangare uku:

  1. Shin abin da aka ruwaito dangane da gajertar Imam Ali (a.s) haka ne ko ba haka ba?
  2. Idan har ya ingata shin gajerta aibi ne ga mutum?
  3. Shin mene ne fassarar wasu siffofi na ma’asumai na zahiri da aka ambata a riwayoyi da a ke ginin aibu ne?

Yanzu zamu shiga bayanin wadannan mas’aloli bi-da-bi:

Da farko dai yana wajaba -kafin amsa wannan tambayar- sanin cewa wasu sifofi da wasu ke ganinsu a matsayin aibi to ba aibi ba ne. Alal misali an san cewa daga cikin sifofin Imam  Ali  (a.s) a kan ce “mai sanko mai tumbi” Shi sanko na nufin wanda ba shi da gashi a gaban kai. Shi kuwa tumbi na nufin girman ciki. To zamu ba da fassara da ta dace da matsayin Amirul muminina (a.s).

A bisa zahiri “mai sanko shi ne wanda babu gashi sosai a magabacin kansa, mai tumbi kuwa shi ne wanda cikinsa ya dan daga sama amma ba don yawan cin abinci ba,  domin  Amirul muminina ba mai yawan  cin abinci   ba ne, mai tattausar rayuwa ne”[1]

A wani zance da ya yi a Nahjul balaga yana cewa:  “To ku saurara shi Imaminku (Ali) a duniyarsa ya wadatu da riga guda da abincinsa gusa daya”.[2]

Bayan wannan gabatarwar wajibi ne a san cewa a ruwayoyi da ke magana kan sifofin Imam  Ali  (a.s) da baye-bayensa akwai lafazin “rubu’in tsawo”  kalmar “rubu’i a maza”[3] wanda wasu suka fassara ma’anarta da gajertarsa.

To wannan fassarar ba daidai ba ce kamar yadda littattafan luga suka nuna. Abin da ake nufi shi ne mai yalwan kafadu. Ku duba wannan zancen a Lisanul’arab:[4]

“Kibiya murabba’a na nufin tsakatsaki ba doguwa ko gajera ba”[5]

Littatafai da dama na luga sun tafi a kan wannan fassara”.[6]

Na biyu: Idan muka dauka gajertarsa ake nufi, ya dace mufahimci cewa ita gajerta ba aibi ba ce matukar ba ta wuce daidai kima ko dabi’a ba, ko kuma ya dadu da wata tawaya ta zahiri to a nan ne illar zata bayyana. Amma idan ba haka ba gajerta ba wani aibi ba ne. Domin Allah (s.w.t) Ya halicci mutane da siffofi mabambanta. Bisa dabi’a wadannan sifofin mutane su kan bambanta, sai dai bai kamata a aibata mutum bisa launin fatarsa ko gajertarsa ko muryarsa ba.

Na uku: Abin da aka ruwaito game da sifofin zahiri na ma’asumai (a.s) tilas su zamana ba masu sa jama’a su kyamace su ko su guje su ba. Domin su jagorori ne na jama’a, dole da’awarsu ta zama ta game komai, watau kiyaye haibarsu.

Wannan mas’alar da aka ambata a riwayoyin ba ta kebanta ga Imamai ma’asumai kadai ba  (a.s), ta game kowane mutum mai hidima ga addini da ke da dangantaka ta kaitsaye da jama’a. Tilas su zamana sun kubuta daga kowace siffa da zata kai ga jama’a su guje su. A sifofin lmamu  kamar yadda ya zo a hadisai  ya wajaba ya zamanto ba mai kuturta ko kyazbi ko ire-irensu ba.”[7]

A karshe zamu yi nuni zuwa ga wani mahimmin bayani:  Amirul muminina  (a.s) kwamanda ne na sojan musulmi kana shi ne babban kwamanda a yakoki uku a zamaninsa. To bisa al’ada a dabi’a ta soja ya zamana sadauki; masamman idan muka yi la’akari a yaki a kan yi fito-na-fito. Kur’ani Mai girma ya yi nuni da tsokaci a kan sifofin soja. Wannan matsayin yana nuna dabi’a ta soja na bukatar mutum sadauki kakkarfa kamar yadda ya zo a kissar Daluta:

“Annabinsu ya ce da su “hakika Allah Ya nada muku Daluta sarki a gare ku” sai suka ce “Kaka mulki zai kasance a gare shi a kammu alhali mu ne mafiya cancantar mulki daga gare shi, ga shi ba shi da yelwar dukiya! Sai ya ce: “Hakika Allah ne Ya zabe shi da mulki a kanku Ya kuma kara masa yelwar dukiya da ta jiki, Allah kuma Yana ba da mulki ga wanda ya so Allah ma yelwacin baiwa ne masani.”[8]

Yana daga cikin sifofin kwamanda na soja yelwar jiki. To hakika Amirul muminina (a.s) yana da wannan siffa kamila.

 


[1] Atabrizi, Jawad, a Siradudun naja’at, j10, sh429 a baiti na 1197.

[2] Assayid Radi Abuhassan Muhammamad, Nahjul balaga, sh417, wasika ta 45, dabaa’in Darulhijra, 1414H,  Kum.

[3] Almajlisi Muhammad Bakir , a Biharul’anwar, j35, sh86, dabaa’in Mu’assasatul wafa’a Berut 1404 H.

[4] A littafin da ya gabata J35, sh4.

[5] Ibin Manzur Muhammad bin Karam, Lisanul Arab j8, sh101, tailfin Adabulhauza Kum,1405 H.

[6] Ibin Asir Muhammad Aljazari, a Annihayaj2, sh190, Mu’assasar Isma’iliya,Kum, 1364 H.

[7] Biharul Anwar j16, sh408.

[8] Albakara 247.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa