advanced Search
Dubawa
3212
Ranar Isar da Sako: 2008/11/09
Takaitacciyar Tambaya
me ya sa Kur’ani bai ba da izini ga mutanen da ba su da ikon yin aure dawwamamme su yi auren mutu\'a ba?
SWALI
Kur’ani ya na kira ga wadanda ba su da halin yin aure dawwamamme cewa: duk wadanda ba su da halin yin aure na da\'imi to su kame kan su domin kar Allah ya yanke falalarsa gare su. Da a ce auren mutu\'a na da matsayi a musuluncin to da a cikin wannan ayar an yi umurni da yin sa ba maimakon kamewa, amma sai ga shi Allah masani ya na kiran wadanda ba su da damar aure to su kame kansu kuma su kiyaye domin hakan zai kai su ga falalar ubangiji. Ta wata fuska in muka lura da wannan ruwayar zamu ga cewa rashin iko shi ne rashin ciyarwa, wanda a cikin aure mutu\'a babu wannan sharadin. Saboda haka a wannan ayar aure dawwamamme zamu fahimta ba wai auren mutu\'a ba.
Amsa a Dunkule
Ayoyin Kur’ani dole ne mu hada su da juna domin mu samu fasara mai ma'ana: saboda wasu ayoyin na fasara wasu ne. a cikin wannan ayar nuni da cewa dukkan wadanda ba su da ikon aure dawwamamme ne ko mutu'a da su kame kansu, ba ya na tabbatar da aurin mutu'ne ba: saboda suratul nisa aya ta 24 ta na bayanin damar yin mutu'a ne kamar haka: idan kai mutu'a da wata mace to ka biyata hakkinta, ko da kuwa kun yanke dai dai hakin {wato kudin da zaka biya ta} da zaka biya amma sai ka kara fiye ko kuma ka rage kasa da yanda ku kayi to ba laifi a cikin hakan Allah masani ne mai yafiya. Ko da kuwa mutanen da a yau suke sukar auren mutu'a ba su da damar cewa ba shi {mutu'a} a cikin musulunci, sai dai su ce auren mutu'a ya zo cikin musulunci kuma a lokaci manzon Allah da khalifa na daya ana yin sa amma da zuwa khalifa na biyu sai ya yi hani da shi, wasu kuma na ganin cewa tun zamanin manzo Allah a ka daina. Akwai ruwayoyi masu yawa a cikin littafan shi'a da na sunna da suke nuni da halarcin auren mutu'a.
Sai dai kai ka dauka rashin ikon dukiya wanda ya zo a cikin ayar ta na nuni da auren da'imine to sai muce: ba haka ba ne domin auren mutu'a ba kowane mutune ba, ba a kuma kowane lokaci yake da damar yin mutu'a ba duk da cewa mutu'a babu {ciyarwa} amma kuma akwai kashe kudi shi ma a cikinsa, saboda a cikin wannan aure dole ne namiji ya bayyana sadaki kuma ya ba matar, saboda haka ayar ta shafi wadanda ba su da madar auren da'imi ko na mutu'a, to abin fahimta ayar shi ne a na daya wato aure dawwamamme shi ne akwai ciyarwa da sadaki amma a cikin na biyu wato mutu'a ba ciyarwa sai dai sadaki wanda ayar ta hada duk biyun.
Amsa Dalla-dalla
1. hukunce hukunce addini musuluncin bai takaita ga aya daya ba, saboda haka a kan tabbatar da wani hukunci dole ne mu yi binciken duk wata ayar da tayi bayani a kan hukuncin. Kuma mu lura da cewa wasu bangare na ayyukan ibadar mu ba a yi bayanisa ba cikin Kur’ani ba sai dai manzon Allah a cikin ruwaya ya bayaninsa: misali: yawan raka’o’in sallar asuba da sauran salloli, ayyukan hajji, da yadda za a fitar da zakka da sauran su.
Saboda haka a cikin musulunci bayan ayoyin Kur’ani akwai kuma ruwayoyi masu daraja na manzon Allah da imamai masu tsarki, a inda ba mu samu dalili aya ba ko kuma hankali bai kai gurin ba sai mu yi amfani da su wuri fidda hukunci.
Daga karshe idan hukunci ko wani bangare na shi bai zo ba cikin Kur’ani ba, ba ya na nufin cewa wannan hukunci bai cikin musulunci ba ko kuma ya takaita ga wasu ayoyi kadai ba ne, sai dai dole ne dukkan ayoyi da ruwayoyi da suka shafi wannan hukuncin mu yi dubi gare su.
2. aya ta 33 suratul nur ga wadanda ba su da ikon ciyarwa ko sadaki wato ba su da ikon dukiya[1] ta ce: wadanda ba su da ikon yin aure, dole su kame kansu domin karsu rasa falalar ubangiji[2]. In muka lura da kyau ayar tana bayanin baki daya ne kamar haka: in ba ikon aure, ku kame kai, ba wai ta ce ba in ba ikon aure da'imi to ku kame kai ta mahangar ruwaya aure ya hade mutu'a da dawwamamme, kuma auren mutu'a ba kuwa ne mutum ba ne ba kuma kuwa ne lokaci ne zai yiwu ba saboda ko da yake auren mutu'a ba ciyarwa cikinsa, amma aure ne wanda shi ma ana kasha kudi cikinsa, saboda cikin wannan auren dole ne namiji yabiya matar sadakin da suka sa. [3]
Saboda haka ayar ta na magana ne kan mutanen da ba su da ikon aure dawwamamme ko na mutu'a, saboda a cikin na farko wato aure dawwamamme akwai ciyarwa da sadaki amma a cikin na biyu wato mutu'a sadaki ne ka dai ciyarwa ba dole ba ne. In mutum ya samu kansa cikin wannan hali sai ayar ta ce ya kame kansa {ka da su shiga neman mata}.
3. ko da wadanda ke sukar auren mutu'a a duniyar yau ba su cewa babu auren a cikin musulunci, sai dai su ce auren mutu'a ya kasance a zamani manzo Allah yana cikin musulunci har ma zamanin khalifa na farko a na auren mutu'a, amma zuwan khalifa na biyu sai ya yi hani da shi.
Wasu kuma na ganin tun lokacin da manzo Allah na rayai a ka dena shi {mutu'a} [4].
Bayan mun anbaci wadannan abubuwa ukun yanzu zamu kawo dalili na Kur’ani da sunna wadanda suka halarta auren mutu'a.
Aya ta 24 suratul nisa ta na cewa: in kunyi mutu'a da wata mace to ku biyata kudin ta bayan kun yanke Konawa zaku biya to ba laifi in kun kara asaman abin da ku ka dai dai ta akai ko kuma kun rage kasan abin da ku ka yanke akai Allah masani ne kuma mai afuwa. ''
Imam baqir (a. s) a kan wannan ayar yana cewa: ta sauka ne a kan auren mutu'a.. [5]
Imam sadiq (a. s) yana cewa: wannan ayar na nuni ne da auren mutu'a[6].
Wasu tafsiran ahlusunna sun fasara wannan ayar da auren mutu'a. a cikin tafsirin tabari daga {abi nazir} ya rawaito ta mahanga biyu ya ce daga dan abbas mun tambayeshi kan mutu'a sai ya ce: shin baku karanta suratul nisa ba?, nace mun karanta: aya {famastamta'atum bi…[7]}.
Kurtabi ya ce: {jam'in maluma sun ce} wannan ayar na nuni ne da auren mutu'a wanda a farkon musulunci ana yin sa"[8].
Idan mukayi amfani da kyau zamu lura da cewa ruwayoyi da yawa suna tabbatar da samuwar auren mutu'a a farkon musulunci da kuma halarcisa.
Kuma muna da ruwayoyi masu yawan gaske wadanda suke tabbatar da auren mutu'a, a cikin littafain shi'a zamu iya ganin su amma zamu yi nuni da daya ne kawai:
Imam sadiq (a. s) yana cewa: {auren mutu'a ya zo cikin Kur’ani kuma sunna ce da manzo Allah} [9].
A cikin littafain sunna akwai ruwayoyi masu dama wadanda ke nuni da auren mutu'a sai dai zamu yi nuni da daya ne:
A cikin babin {auren mutu'a} a cikin littafin sahihul musulim da bukari, masnaf abdurrazak da masnaf ibin abi shaiba da masnad Ahmad da sunnan baihaqi daga abudullah dan masa'ud sun rawaito yana cewa: {mun kasance muna yaki tare da manzon Allah kuma ba mata mu a tare damu, sai mu kace yafi kyau muyanke gaban mu {al'aura}, sai manzo ya hane mu da aikata hakan, sannan ya bamu ikon mu biya sadaki mu yi aure da mata na dan lokaci[10].
Dukkan wannan na nuni da samuwar wannan hukuncin cikin musulunci.
Don Karin bayani:
Tambaya ta 2965 (a shafin nan 3467) game da auren mutu’a.
Tambaya ta 3352 (a shafin nan 3658), game da shafe auren mutu’a.
 

[2] tabatab'I, Muhammad husai, tarjamar tafsirin almizan, jildi na 15 shafi na 157, yadawa jami'a mudarisin hauze qom; Nisa’i: 33.
[3] Nur,33
[4] Tafsirin mizan jildi 15 shafi 460-493.
[5] Nisa: 24.
Burujardim, Muhammad Husain, jami'ulhadis shi'a jildi na 26, shafi na 35.
[6] Cikin littafin sama shafi na 36.
[7] Askari, sayyid murtaza, auren mutu'a cikin musulunci, shafi na 16; tafsirin tabari, jildi na 15,shafi na 9,.
[8] Cikin littafin sama, shafi na 19.
[9] Jami'ulhadis shi'a,jildi na 26,shafi na 40.
[10] Auren mutu'a cikin musulunci shafi na 22.
 
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • idan mas'alar jagorancin malami tana ganin cewa kafa jagora ne, to me ye gudummuwar mutane a ciki?
  4913 انتصاب یا انتخاب
  Duk da akwai nazarin cewa idan muna son mu sanya dokoki da bai kebanta da wani wuri ko zamani ba, ba mu da wata hanya sai zaben da mutane zasu yi. Kuma akwai hanyoyi biyu da suka shafi sharuddan zabar jagora kamar haka:
 • mene ne hanyar debe kewa da Kur’ani
  8430 Halayen Aiki
  idan ya zama tilawar da mutum zai yi ta Kur’ani don neman kusanci ne zuwa ga Allah, da tadabburi da bibiyar aiki da shi, to zai zama tilawar ta kusantar da shi ga manufar Kur’ani sosai, zai zama son Kur’ani zai tsananta. ...
 • Me ake nufi da hadisi rafa’i
  12130 مبانی فقهی و اصولی
  An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
 • mene ne mahanga Kur’ani a kan halayen musulmi na zaman lafiya zakanin su da sauran mabiya addine?
  13157 Tafsiri
  {Zaman lafiya tsakanin mazahabobi} na daya daga cikin fikra ta asali a musulunci ayoyi da yawa sun zo cikin Kur’ani mai girma ta fuskoki daban daban, a bayyane suna yin nuni da hakan {zaman lafiya}. A mahanga Kur’ani yaki na mazahaba saboda bambancin akida kamar yadda yake ...
 • Yaya asalin mutum yake?
  17499 خلقت انسان
  Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
 • Mene ne sharuddan da ke sa wa Rana ta tsarkake kasa da gini?
  6000 بیشتر بدانیم
  Rana na daya daga masu tsarkakewa kamar yadda ya zo a fikhu, yadda rana ke tsarkake gini da kasa kuwa; ka da a samu tazara tsarkakakkiya tsakanin zahirin (doron) kasa da bayanta (cikinta) ko kuma ginin da hasken ranar zai sauka a kansa kamar iska ko wani ...
 • Wadanne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani da kuma (kimarsu) matsayinsu na ilimi?
  4551 Ilimin Kur'ani
  Baba shakka kan cewa hakika sahabbai Allah Ta’ala ya kara yarda a gare su ya yarje musu sun bawa lamarin Kurani mai girma minimmanci sosai a lokacin rayuwar Manzo (s.a.w) da ma bayan wafatinsa (s.a.w) kuma sun dauki tutar addini da kyakkyawar koyarwa sama zuwa jama’a. kuma ...
 • DOMME AKE WA KA’ABA RIGA DA YADI MAI BAKIN LAUNI KAWAI?
  9591 حج و عمره
  Ana kiran wannan bakin kyalle da ake rufe Ka’aba da shi a wannan zamani da suna suturar Ka’aba ko rigar Ka’aba. A wannan zamani ne ake wa Ka’aba rika da bakin yadi, da aka yi masa zayyanar ayoyin Kur’ani da aka saka da launin ruwan gwal. Amma ...
 • wace hanya ce ta magance munanan saqen zuciya da tunaninnika munana da kyautata alaka ko dangantaka da ALLAH?
  12547 ارتباط انسان و خدا
  Hakika ita alaka ko daggantaka ta kasu kasu biyu, alakar ALLAH da mu da kuma alakar mu da ALLAH, to alakar mu da ALLAH na iya samun rauni, amma raunin yana faruwa ne daga bangare mu zai wuya alakar tamu da ALLAH ta yanke baki daya. Sai ...
 • Don Allah ina so ku yi min bayanin tarihin rayuwar Arkam dan Abi Arkam a takaice?
  2850 صحابه در نگاهی کلی
  Cikakken sunan Arkam dan Abi’arkam shi ne: Arkam dan Abi’arkam (Abdu Manaf) dan Asad dan Abdullah dan Umar..... dan lu’ayyu bakuraishe, bamahzume,[1] babar sa ita ce Ummayatu ‘yar Abdul Harisu daga kabilar khuza’a ta fito.[2] Yana daga cikin wadanda suka musulunta ...

Mafi Dubawa